Sashe 29
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Nene na fita sashen Tauraruwa ta nufa kanta tsaye basa cikin parlourn fadawa suka sanar mata suna cikin d’akin barcin Tauraruwar. Zama ta yi a parlourn tace su sanar da Tauraruwa zuwanta. Tauraruwa ta mik’e da sauri ta nufi parlourn Ido ta zubawa Nenen cikin mamakin ganinta da safiya haka. Su da suke shirin zuwa su d’aukota idan ta je wajen su Babi ta dawo. “Shigo Nene, daga ina haka?” Nene ta cire hannayenta daga tagumin da ta zuba kafin ta mik’e ta bi bayan Tauraruwa tana furta “Ina Najee take?” Gaban Tauraruwa ya fa’di jin ashe Nene ta sani ita da bata so zancen ya fita ba a samu a mayar masa da matarsa tunda saki guda ne! Maimartaba ma ta rok’eshi kada ya fitar da zancen zuwa a ga abinda Allah zai yi haka su Hajja da Yakumbo. Ta ciji leb’enta tana jin koma wa ya gayawa Nene bai kyauta mata ba, don bata son iyayen Najee su ji don ta san ba zasu ji da’di ba ace an sakar musu y’a a daren aure! “Ki shigo ciki mu yi magana.” Ta furta cikin mutuwar jiki. Nene ta bi bayanta suka shiga d’akin. Anan ta hango Najee ta yi wankanta tana sanye da doguwar Riga mai bala’in kyau y’ar morocco. Gashinta mai tsayin gaske da cika ta d’aureshi a tsakiyar kanta. Ta yi kyau ba d’an ka’dan ba. Tana ganin Nene ta mik’e da gudu ta fa’da jikinta tana dariya. Nene ta saki ajiyar zuciya ta rungumeta sosai tana jin soyayyar Najeen na sake bunk’asa a zuciyarta. Sai kawai ta ji hawaye na zuba mata sanin cewar har abada ba zasu zamo abu guda da Najeen ba, ba zata haifa mata jikoki kamar yarda ta dinga fata ba.. Ta ja hannun Najeen suka zauna a gefen gadon. Tauraruwa kallonsu take kawai tana murmushi soyayyar da suke wa junansu tana burge ta matuk’a da gaske. “Zan tafi da Najee bana buk’atar sake sauraran komai daga bakin ki ko na Murad ba abinda zan ce muku sai godiya, zan tafi da ita idan ta gama idda zan aurar da ita ga mutumin da ya san mutuncinta wanda zai rik’e min ita da yardar Allah mai ku’di Kuma da mulki tunda kuma da shi kuke tunk’aho..”Tauraruwa ta ware ido cikin mamakin furucinta ta ce “Ki tafi da ita ina kuma? Auren naki da nata fa? Ko kuwa daga saki d’aya sai ki haramtawa mutum matarsa?” “Ko Rabin saki ya mata na haramta masa Najee har abada wallahi! Ki gaya masa ko Najwa ta rasa Mijin aure ba zata koma gidansa ba har abada!!”
D’if ji da ganin Murad da yake bakin k’ofa ya d’auke ya runtse idanunsa a hankali yana furta YA ILAHAL ALAMEENA!
JIKAR NASHE CE🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Da sanyin jiki ta isa parlourn Umman tana zaune tana gyaran farcen k’afarta. Ta amsa da fara’a tana kallon Najman da ta shigo jikinta a sanyaye, ta zauna a kujerar kusa da Umman kanta a k’asa tana wasa da hannunta, Umman da ta fahimci abinda ya kawota sai ta saki ajiyar Zuciya ta ce “Allah ya sanya albarka a aurenki Najma, Ubangiji ya baku zaman lafiya ya ka’de dukkan fitina, shi aure dai hak’uri ne yake kai shi ga wani mataki mai girma idan kin jure, ki yi biyayya ga mijinki iya iyawarki sai soyayyarki ta dinga hauhawa a zuciyarsa rashin yi masa biyayyar yana rage k’ima da martabar soyayyarki. Kishiyarki kuwa ki zauna da ita lafiya da zuciya d’aya, Allah ya baku zaman lafiya da mijinki ya ka’de dukkan fitina ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya. Tashi ki je Allah yasa gidan zaman ki ne. Najma ta amsa a zuciyarta tana mik’ewa a hankali girma da mutuncin Umman yana sake k’arfi a zuciyarta da gaske Umma mace ce managarciya wacce duk wanda ya sameta a matsayin Uwa ya ji dad’insa duniya da lahira bata damu da duniya balle abinda yake cikinta shi yasa take zaune zuciyatta fresh ba abinda ke damunta. Umman ta kama hannunta ta rakata har wajen motar Baffan ta sakata a ciki tana sake jaddada mata mahimmancin addu’a kafin ta kai ga ta shiga cikin gidanta. Baffa da’di ya ji har a ransa yana sake k’aunar Umman a zuciyarsa data zamo mace mai matuk’ar sanyin hali da sauk’in zuciya. Irin matar da maza suke kambamata a ko ina wajen abokansu. Ya ja motar suka nufi gidan Jaheed shima yana sake jaddada mata ta yi hak’uri ta kuma jajirce da bautar ubangiji shine tsani da mutum yake bi ya taka matakin nasara a aurensa.