Sashe 34
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sun taimaka mata ta yi wanka kafin a bari mutane su fara shiga ganinta. Nasma ce ta kira Najee ta gaya mata wani irin tsalle Najeen ta yi cikin murna ta ce “Ina Adda Najman take?” Nasma ta ce “Tana lafiya ban ga kin zo ke da mijinki ba kuma kowa ya zo daga Garin Gabas d’in.” Najee ta saki ajiyar zuciya rashin sanin amsar da zata bata a hankali ta furta “Kina kusa da Nene don Allah bata.” “Nene tana gida ki kira wayarta mana..” Ta d’aga kai “Okay nagode ki gaishe min da Addan zan zo In sha Allah..” Tana kashe wayar ta fara kiran Nene. Nene ta d’aga wayar tana furta “Ya aka yi Najee…” “Ina son zuwa naga twins pls Nene..” Nene ta yi d’an tsam da ranta kafin ta furta “Ki yi hak’uri Najwa idan kin zo kinga asirinmu zai tonu…” shirun da Najee ya tabbatarwa da Nene bata so hakan ba sai kuma ta fara jin shashshek’ar kukanta. “Shikkenan ki yi shiru zan turo a d’aukeki jibi tunda Baffa ya ce gobe zan tare..” Najwa ta saki ajiyar zuciya hankalinta ya d’an Kwanta duk da tana ganin kamar jibin ya mata nisa. Suna sallamar Nene ta cigaba da d’an tattara kayan da zata buk’ata duk da Uban sitturun da Tauraruwa ta ce An saka mata a d’akinta a gidan Mai martaba hakan bai hanata tsintar abubuwanta masu amfani ba. Jikinta ya yi sanyi duk sai ta ji bata son rabuwa da gidna Baffan duk da shi ya nemi haka ya ce a goben ta bi ayarin da suka zo ganin jarirai idan anzo tafiya da su Najma. Umma ce ta shiga d’akin da sallama tana duban yarda yanayin jikin Nenen yake a sanyaye. “Mai gyaran jiki tazo zata fara aikinta Nene.” Nene ta waro ido tana furta gyaran jiki kuma? Na menene Umman yara god’ai go’dai da ni.”
Umma ta watsa mata wani kallo kafin ta girgiza kai “Wallahi Nene sai kin dage gidna sarauta baa zama haka gwara ma ki tashi tsaye duk wannan dattijantakar ta k’arfi da yaji da kika d’orawa kan ki ki direshi idan kina son kin malllaki Mijin ki, ki tuna ya yi gwagwarmaya da mata iri iri dole sai kin dage kafin ya ji banbanci tsakaninki da su. Gata nan zata shigo zata miki yau ta miki gobe sai kuma ki tafi da ita masarauta ta cigaba da miki…” Nene ta sunkuyar da kai haka kawai sai ta ji kunyar Umman mai girma ta mamaye ganinta. Shigowar Jaheed da sallmarsa ya ce yasa Umman shiru da zancen da ta b’aro mata na ta je wajen Anty Surayya Dee ta gyareta da kayan mata na bojuwa herbals sannan ta ganganra gurin mai kayan matan zuru itama ta bata had’addun kayan Gyara y’an garari. Jaheed ya gaida Nene kafin ya sake wa Umma sannu ya furta “Doctor ya ce ba za’a iya tafiya da ita yanzu ba a bari ta yi ko sati biyu ne, don haka mai martaba ya ce a kyaleta idan sati biyun ta yi zai turo da private jet a d’auketa.” Umma ta d’aga kai ta furta “Hakan ma ya yi.” Jaheed ya gyara zama ya ce “Yanzu Umma ba za’a yiwa Murad afuwa ba a mayar masa da matarsa tunda a kuskure da rashin sani ya saki Najeen……” Wani irin d’agowa Umma ta yi tana kallonsa ta ce “Saki kuma?
Murad ne ya saki Najwan?” Ta fa’da idanunta suna bayyana wani irin taratsatsin b’acin rai….. Nene ta waro ido tana runtse su lokaci guda Shikkenan Jaheed ya b’ata mata aiki me yake son ta ce da Dattawan arzikin nan? Hasbunallah! Umma kuwa fuskarta a ha’de take kallon Nene ta furta “Tunda ya saketa yanzu tana ina? Ai sai ta dawo gidan Ubanta….” A cikin kalamin Umma Murad ya hango tsagwaron b’acin rai mai bayyana rashin sassauci ga wanda ya aikata laifin ya san za’a kai ga haka da ya san Umman ba ta sani ba bata yarda za’a yi ya furta hakan….
JIKAR NASHE🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Tsit suka d’auke wuta a d’akin, Ko kwakwkwaran numfashin baya fita da k’arfi a d’akin, Tsoro da tashin hankali sun bayyana k’arara a idanunsu da fuskokinsu. Umma ta mik’e zuciyarta na sake tunzira da
Wani mashahurin b’acin rai da
Ya kasa b’oyuwa a dukka sassan jikinta musamman fuskarta da ya bayyana muraran don idanunta har jajir ya yi saboda tsananin b’acin rai. Jikinta har rawa yake ta fice daga d’akin Nene kuma ta kasa saka baki ta kirata saboda wata irin kunya da ta lullub’eta. Jin rufe k’ofarta da k’arfin gaske yasa Nene sakin wata k’akkarfar ajiyar zuciya ta d’ago tana kallon Jaheed cikin wata irin murya data bayyana rashin kuzarinta a fili ta ce “Hankalinka ya kwanta Mujaheedu, duk abinda nake hak’ilon b’oyo ka bayyana shi ka b’ata min shiri na cikin d’an k’ank’anin lokaci, Yanzu wace amsa ka tanadar min da zan amsa tarin tambayoyinsu da wani suna kake son su kira ni? BUTULU KO?”
Ta fa’da tana sirantar da ganinta a cikin nasa idanun. Zazzafar k’wallar da ta taru a k’asan idaninta ta samu damar sub’otowa ta fara kwaranya da saurin gaske kamar an kunna famfo. Jaheed ji ya yi duniayr na wani irin katantanwa da shi kamar wanda ya sha abin maye. Ya runtse nasa idon da k’arfin gaske don tabbas kukan Nenen na nufin abubuwa da dama kuma yana neman saka nasa hawayen zuba wanda ya manta yaushe rabonsa da hakan. Shirun dai suka yi don basu da wata mafita sai wacce su Umman da Baffan za su yanke a halin yanzu.
—-
Bata shiga sashen Baffan ba don a yanayin da take ciki ta san tabbas idan ta shiga abubuwan da zata furta ba masu da’di ba ne, zafinsu zai iya tasirin da zai tafarfasa zuciyar Baffan, ba kuma ta san hakan don hakan ta shanye ta shige nata sashen ta kai gwauro ta kai mari tana neman abinda zai d’auke mata nata b’acin ran. Sai dai ba wani sauk’i da ta ji a zuciyarta kuma ranta ya sake tabbatar mata da nanata mata sunan da ta sakawa Nene na Butulu a tunaninta laifin kacokam yana kan Nenen zuciya bata da k’ashi. Ta lumshe idonta sai ga k’wallar itama ta fara kwaranyo mata. Ta ja gefen Hijab d’inta ta share k’wallar kafin ta fara jan addu’oin da take jin zata iya samun sauk’i da su cikin zuciyarta.
Sai da ta kawar da b’acin ran sannan ta nufi b’angaren Baffan. A zaune yake yana kallon T.V Africa Tv3 channel yake kallo. Da muryarta da ta k’ara sanyaya saboda yanayin da take ciki ta yi sallama ta shiga. Ya d’ago yana kallonta da alamun ya fuskanci yanayin b’acin ran da take ciki duk da k’ok’arin b’oye hakan da take yi. Tana zama yana jefo mata tambayar da ta sa ka ta d’ago kai da sauri “Me ya faru? Da alama ko menene girmansa ya kai tunda har ya canja min kamannin fuskarki.” Ta zauna tana sakin ajiyar zuciya a hankali kafin ta dubi abincin da ke gabansa ta tabbatar ya ci abincin ya sha kuma fruits da furarsa kamar yarda ya saba duk dare a al’adance sannan ta saki jikinta a hankali ta bijioro masa da maganar. “Ka san k’addara ta raba auren Murad da Najwa….” Da wani irin hanzari ya d’ago kai yana kallonta “Wani irin magana nake ji haka? Yaushe aka yi hakan duk ban sani ba? Yau fa kwana biyar da tariyar…” Umma ta ciji leb’enta na k’asa kawai a hankali ta furta “Ban sani ba wallahi Baffa, na dai ji zancen
A sama daga bakin Jaheed kamar yarda ka ji shi….” Shiru ya yi yana jin wani irin abu yana suka a zuciyarsa kafin ya yi k’arfin halin furta Lahaula wala k’uwwata illa billah….. ya saki ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya d’an girgiza kansa yana jin sauyin da zuciyarsa ta yi wajen nauyi da hayak’in b’acin rai suna tafiya a hankali “Kira min Nenen na ji yarda aka yi…” Umma ta mik’e don cika umarninsa itama dai sosai take yak’i da zuciyarta wajen ganin k’iyayyar Nenen bata wanzu a zuciyarta ba.
A k’ofa ta tsaya bayan ta yi sallama can k’asan mak’oshi Nenen ta amsa mata tana d’ago kanta cikin mutuwar jiki. Ta sauke idanunta a hankali a cikin na Umman kafin ta amsa sallamar. “Baffa na buk’atar ganinki…” Hakan Umman kawai ta ce mata ta juya ta fice. Wata irin razana da firgita ta ji zuciyarta ta mata ta buga sosai cikin k’arfin hali ta ja addu’a akan harshenta kafin ta mik’e jikinta na rawa ta zura dogon hijabinta ta fita jikinta sam ba laka idanunta suna kunyar Arangama da na Baffa.