Sashe 42
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ta gama shirya tsaf cikin kayan da bata san wanda ya kawo su ya ajiye a kan gadon ba sai jin kunya da nauyi ya hanata fita parlourn ta yi zamanta a katafaren gadon da yake d’akin Mai martaban tana sake hakaito abinda ya wakana tsakanin su a tsakiyar daren yawan albarka da Mai martaba ya dinga shi mata har yanzu muryar na nan ra’dam a cikin kunnuwanta ta girgiza kai tana sakin murmushi ha’de da lumshe ido a hankali Ta furta Hamdan Katheran Ya rabb…” Dai dai lokacin da ya tura k’ofar d’akin ya shigo. Idanunsa a kanta yana kallon yarda yanayinta ya nuna mabayyaniyar kunya. Murmushi ya saki ya zauna a gefen gadon yana d’auke mayafi da ta rufe fuskarta da shi ya furta “Ai na siyi bakin Fulanin Gabas mai mulkin zuciyar Mai Gabas! Allah ya yi miki albarka ki taso mu je mu karya.” Gani ya yi ta zame ta tsuguna a gabansa cikin nutsuwa ta furta “Ina kwana ranka ya da’de an tashi lafiya?” Ya zuba mata idanu walwalar fuskarsa ta kasa b’uya ya furta “Idan ma na tashi lafiyar Ai kin fi kowa sani Ranki ya da’de..” Ganin yarda yake tsokanarta sai ta mik’e kawai tana murmushi hakan yasa ya bi bayanta yana sake jifan ta da wasu kalamai da tasirin su ya girmama a kwanyarta….
Suna gama breakfast Tauraruwa da Fulani Saddik’a suka shigo. Fulani Saddik’an bakomai a ranta suka gaisa da Maimartaba da Fulani Nene. Tauraruwa na cigaba da tsokanarta da ya kwanan bak’unta. Bayan mintuna da zamansu Tauraruwa ta d’ago tana kallon Maimartaba ta furta “A yau nake son karb’o yaran Raheena daga inda na ajiye su don ta damk’a kowanne ga mahaifinsa…” Maimartaba ya guntse fuska b’acin ransa ya bayyana don a zahirin gaskiya ko sunan Raheena ba ya son ji balle a masa zancenta.. “Hakan Ya yi ya furta cikin bayyana b’acin ransa. “Ki kawo yaran nan ki kuma saka tazo ita da abokan lefinta da suke d’aure a gidan Yari.” Tauraruwa ta d’aga kai tana ficewa daga b’angaren nasa. “A yau itama take son sauke nauyin da yake kanta, don biyu daga cikin yaran tuni suka matsa mata suna son sanin asalinsu don sun manyanta suna son su yi aure amma ga duk inda aka je neman aure sai a ce sai an san asalinsu.
A yammacin ranar Tauraruwa ta shigar da zaratan Samarin su hu’du cikin Fadar Maimartaba. Daga bayanta kuma Fulani Raheena ce da tsoronta da fargaba ya sake bayyana musamman ganin da ta yiwa yaran kamaninsu da k’annen mai martaba da suka zama iyayensu ta sake bayyana muraran kana gani ba tare da ka tambaya ba zaka gasgata hakan.
Fuskar Sarki ta bayyana tsananin b’acin ransa, ya zubawa K’annensa ido yana sake bin yaran da kallo. Tauraruwa zata fara magana ya d’aga mata hannu “Ba sai kin yi magana ba kowa anan ya san d’ansa ina son su d’au y’ay’ansu su kuma fice daga cikin masarautar Gabas har abada na yanke alak’ata da su.” Ya juya ya kalli Saddik’a ya furta “Ba ke ba yarana da kika haifa wa’danda na tabbatar jinina ne halak har abada bana son ki sake kusantarsu na baku awa biyar kacal ku fice daga masarautar nan da ku da duk wata tsiya taku!” Shiru Fadar ta yi tabbas hukuncin da Maimartaba ya zartar shine abinda ya dace… Haka kowa yake furtawa Maimartaba ya nemi kowa ya fita yana buk’atar hutawa. Nene ma ta mik’e zata bi bayan su Tauraruwa ya sa hannunsa ya danne nata hannun yana furta “Wa zai kula da ni idan kika bi su?”
……Murad kuwa wata irin soyayya suke mai tsayawa a zuciya a yanzu ya tabbatar ya yi dace da kalar matar da yake so. Wacce bata k’auro a soyayya take bayyanata take nuna masa iya iyawarta tamkar ba yarinya k’arama ba. Ko da yake shi ya ginata a kan wannan tsarin ya kawar da duk kunyar da take tsakaninsu don ya ce Ba wata kunya da Allah ya halatta ta tsakanin Mace da Mijinta. Ita sirrinsa ce da ya halatta taga komai na jikinsa don haka komai tare suke yi cikin kwanakin da basu wuce bakwai ya yi wani irin gogar da ita. Ta kuma ta ji ta bi take shayar da shi wata irin soyayya mai zafin gaske..
Suna zaune da yammacin ranar kansa a kan cinyarta Tana wasa da sumar gashinsa yana lumshe ido ya ce “Naj kina son na koma ruwa ne?” Turo baki ta yi ta furta “Bismillah mana..” Ya d’an bu’de lumsassun idanunsa a kanta ya furta “Ba fa na gajiya da ke Naj…. kin san alk’awarin da zan miki?” Ta girgiza kai. “Har abada ba zan miki Kishiya ba, Saboda Allah ya mallaka miki duk wani abu da nake son naga matata da shi, komai kina da shi…..” Ta saki murmushin da ya bayyana murnar da zuciyarta take ciki ta ce “Allah ya amsa bakinka K’alb yasa har abada ba zaka sake d’arsa soyayyar wata mace a ranka ba…” Ya shafa cikinta da girman sa ya kusa isa haihuwa ya furta “Allah ya kawo mana Babies lafiya mu isa Nigeria mu ba su mamaki….” Lumshe idonta ta yi tana furta “Ameen saura kuma idan suka zo ka fifita soyayyarsu akan tawa wallahi bar maka su zan yi…” Dariya ya yi sosai ya furta Kishi har da Angels d’ina? Ba zan so su fiye da ke ba amma na san zan yi musu so mara kwatance…”. Murmushi ta saki tana burin ranar da za su isa Nigeria tana zakwa’din zuwa sabida rabonta da can shekara guda kenan… Ta tuno sanda Nene ta kira waya ta balbale Murad da fa’da Murad d’in ya saka wayar a fuskar Najwa, ya kalli Najwa ya ce “Tell her you love me ba zaki iya rabuwa da ni ba?” Najee tana dariya ta furta “Yes Nene I love my Husband please!” Nene ta waro ido tana kallonta da yarda ta yi wani masifar kyau ta furta “Najee da kan ki?” Ta d’aga kai tana shagwab’a fuska irin na yara. Nene murmushi ta saki ta furta “Ai shikkenan Alhamdulillah Rabbi ya sake ha’da kan ku.. Yaushe zaku zo Nigeria?” “Sai ta haihu Nene zamu zo because she is pregnant…” Nene kashe wayar ta yi tana dariya wani farin ciki na ratsa zuciyarta Najwa ce da cikin jikokinta Najwa dai mafi soyuwa a gareta fiye da komai da kowa a duniya… “Alhamdulillah ta furta a hankali….” Har Maimartaba da yake zaune a gefenta ya juyo yana kallonta “Saura ke Fulani ina son ganin precious daughter d’ita.” Fulani Ta d’an lumshe ido tana kallon cikin da ke gabanta na wata shidda kunya tana sake kamata wai itace da ciki tana yi y’ay’anta na yi banda Maimartaba ya cije da tuni ta cire cikin amma ba yarda zata yi da k’addarar Ubangiji. Mai martaba ya shafa cikin yana furta “Ina son cikin nan Fulani kamar yarda nake son mai cikin…” Fulani ta b’oye kanta a cikin k’irjinsa tana sakin murmushi… dafatan Allah ya rabata da cikin lafiya ita da Najwa don Khaireen Jaheed tuni ta haifi santaleliyar y’ar ta mai kama da Nene kwabo da kwabo.
A daren wata rana da Najwa ba zata tab’a Mancewa da ita ba nak’udar ta sark’e mata. Daga ita har Murad sun tsorata sosai da yarda ciwon nak’udar yazo mata a gaggauce don kafin su fita harabar gidan da suke su nufi asibiti kai ya fito Najwa ta durk’ushe cikin azabar Ciwo ta furta “K’alb wani abu zai fito….” kafin ta k’arasa ta saki wani irin nishi mai nauyin gaske. Sai ga kukan Jaririya Murad ya ware ido yana kallonta cikin mamaki ya ce “Naj kin haihu…” Kafin ta amsa wani kan ya sake dannowa sai ga Baby ta sake fitowa daga ita har Murad d’in sai suka ki’dime dariya kawai suke. Da sauri ya yi waya asibitin da yake zuwa antenatal aka turo da ambulance aka kwashe su a gaggauce bayan nurses d’in sun yanke cibiyar yaran a wajen. Murad dai fuskarsa dariya kawai yake saki yana furta Alhamdulilah kafin ya kira Kowa Baffa ya fara kira yana d’agawa ya furta “Baffa Najwa ta haifa maka mata biyu…” Baffa da ya ji zancen daga sama ya waro ido yana furta “Murad Allah yasa ba wasan da ka saba min ba ne…” “Am serious Baffa Wallahi ta haihu yara biyu Mata.” Baffa ya furta “Alhamdulillah!” Ya shiga k’walawa Umma kira da Mahmeey suma cikin tsananin Farin ciki suka dinga furta kalmar Alhamdulillah!
Tsaf aka fito da su daga d’akin da aka gyara su sai k’amshi suke su da Uwarsu, zuwa d’akin da zasu huta Najwa lumshe ido kawai take tana kallon Murad da ya nufo gadon cikin sauri ya kai mata kiss a kumatu yana furta “I love you Naj…” Ta saki murmushi tana furta “Love you Too K’alb.” Ya d’aga yaran yana murmushi ya furta “Guess their names….” Ta lumshe ido ta ware akan yaran da suke tsananin kama da ita sai dai sun d’auko hasken fatar Mahaifinsu ta furta “Am not good in guessing…” Ya lakaci gefen k’uncinta ya furta “Umma and Fulani Saddik’a…” Ta lumshe ido tana turo baki ta furta ta ce “Nene fa?” Ya girgiza kai “Ki haifota next year ita da Tauraruwa kin san fa na fi son yara mata…” Ta girgiza kai tana furta “Allah kawo masu albarka.. Yaushe zamu tafi Nigeria?” “Nextweek In sha Allah ya furta yana d’ora Babyn a jikinta “Oya gyara ki bata nono na samo ganye kuma na miki wankan jego…” Ta waro ido ta ce “Mhmn sai na koma Nigeria na san Nene zata min….