Sashe 21
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: . Sun isa Masarautar Gabas hankali kwance cikin tafiyar da ba su gaji sosai ba. Musamman kasancewar tafiyar an yi tane cikin kwanciyar hankali da tarin nutsuwa zuk’ata kuma suna cikin annashuwa. Suna parking dandazon jama’ar suka zo musu barka da sauka. Wannan karan ga duk wanda ya kalli fuskar mai martaba ya san yana cikin tarin farin ciki da nutsuwar zuciya. Dole ya kasance mai godiya ga Allah ba don komai ba sai don samun abubuwan da ya fi so a rayuwarsa Tauraruwa da kuma yaransa biyu da yake jin kamar ba shi da wasu y’ay’an da suka wuce su. Gefe guda kuma soyayyar magaifiyarsu ta yi wa zuciyarsa mugun kamun da bai tab’a ha’duwa da shi ba ko a zamanin samartakar. Komai na matar ya yi masa siffa da kamannin fuskarta da kuma rantsatstsiyar kunyar da ba kowace mace ba ce take samu sai wacce Allah yaso da rahma. Kunya wani yankice daga Imani haka Manzon Allah s.a.w ya ce. Don haka kunya take zama adon da yake k’arawa mata kyau da nagarta ana son mace mai kunya tana da kwarjini a idanun maza da wuya wani namijin banzan kuma ya kawo mata maganar banza matuk’ar ya sameta da kunya. Don haka ya dinga jin soyayyar Nene tana sake fusgarsa ba don komai ba sai don kunyar da ta wa fuskarta ado da ita. Ta kasa ha’da ido da shi duk da k’ok’arin sa na son ganin hakan ta faru. Shi ka’dai ya saki ajiyar zuciya kafin ya lumshe ido yana ayyana ya zama dole ya yi wani abu a satin nan a kawo masa matarsa, idan ba haka ba tunaninta da kewarta ba zasu tab’a barinsa ba. Tauraruwa da take ankare da shi da duk yanayinsa ta saki murmushi kawai ba tare da ta furta komai ba don ba a mahallin cewar take ba. Sai sun k’arasa sashensa za su yi magana ta fahimtar juna da shi.
Sanda Fulani Raheena ta samu labarin dawowarsu gabanta ne ya tsananta bugu, hankalinta ya fi na baya tashi zufa ta ko ina zubo mata take, har dare zuciyarta bata natsu ba musamman da ta ji muryar Jakadiya tana rangwa’da sallama. Wata irin hautsinawa cikinta ya yi ta tabbata abinda take gudu ne ya zo. Jakadiya ta shiga fuskarta a ha’de don ba d’an ka’dan ba take jin haushin matar nan bama ita ka’dai duk wanda ya kwana ya tashi a masarautar gabas ya san kuma abinda ya faru zuciyarsa cike take taf da tsanar Fulani Raheena. Dukkan mutuncinta ta zube k’asa wanwar haushinta da tsanarta sun samu mahalli a zuciyar ahalin masarautar. Ta d’ago idanunta da k’yar tana kallon Jakadiyar da take tsaye ba wani alamun russunawa a tattare da ita ta ce “Sak’on kira ne daga Maimartaba, ya kuma ce k’afata k’afarki.” Hantar cikinta ta kad’a kamar yarda zuciyarta ta bada sautin bugu mai k’arfin gaske. Jikinta ba k’wari sam ta mik’e very slow tana jan alkyabba ta suturce jikinta. Layar da yake hannunta ta sake rik’ewa k’am da niyyar idan aka je fada ta matseta kamar yarda Malaminta ya umarceta ya kuma d’orata a turbar cewa matuk’ar ta aikata hakan Maimartaba ba zai iya aikata komai ba sai abinda ta ce. Zuciyarta bata amince ba don tana ganin kamar girman lefinta ya shige yafiya amma sanda Malamin ya mata rantsuwa sai ta samu nutsuwar zuciya ka’dan tana fatan Layar ta yi mata aikin rufe bakin Maimartaba ya kasa furta mata kalmar saki. Ta saka takalma a sawunta kafin ta fita Jakadiya kuma ta sakata a gaba suka bi ta ainihin k’ofar da zata sadata da sashen Maimartaba daga b’angaren nata.
Shiru parlourn baka jin komai sai sanyin a.c da wani sassanyan k’amshi da ya gama mamaye parlourn. Sai sautin karatun Alkur’ani da yake tashi ka’dan ka’dan a cikin parlourn cikin suraturrahman.
Tauraruwa ce a hakimce a parlourn hannunta d’auke da fruits tana sha cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Ta sauke idanunta a cikin na Raheena da ta yi saurin d’auke nata idon tana hangar inda zata ga Maimartaba don ta matsa layar da ke hannunta. Tauraruwa ta yi murmushin da kai tsaye za’a kira na isa kafin ta mik’e cikin takun isa ta isa gaban Jakadiya. Murya a murd’e cikin dakiya ta ce “Mai martaba baya buk’atar ganinta ya bada sak’o a bata da fa’din ba zai iya ganin mahainciya ba, wacce ta dinga gararanba da igiyar aurensa a duniya, Ya saketa saki uku sannan yana buk’atar d’akinta zai sanya Uwar su Jaheed a ciki, ga mukullin gida nan ya ce ki bata ta ci albarkacin yara biyu na halak da ta haifa masa wanda likita ya tabbar da zamowarsu zuri’arsa, bayan haka baya buk’atar sake ganin Raheena a idanunsa, kwana biyu ya bata ta tattara komatsanta mai guri tana zuwa.” Daga haka ta shige sashenta ba tare da ta sake yiwa Raheenan kallo na biyu, saboda tsanarta mai girma da ta mamaye duka sassan zuciyarta, take Jin kamar at fisgita ta matseta ta kasheta.
Jakadiya ma kallonta ta yi tana furta “Raheena kin ga illar son zuciya ko? Yanzu wa gari ya waya? Bayan tsinuwar Allah da malaikunsa sai kuma ki sabbabawa kanki tsinuwar mutane da Allah wadarai, ba kowa kika yiwa ba wallahi sai yaranki. Ga takardar sakinki nan Allah ya kiyaye na gaba ya yafe miki kurakuranki, ita da kuka so sakawa a wahala ga shi nan itace ta haifo Masu mulkin gabas magadan gabas ko ba komai ta tsinci dami akala Allah ya kiyashemu aikata aikin DA NA SANI….. “ daga haka ta fice ta bar Raheenan a durk’ushe tana sakin wani irin kuka mai bayyana b’acin ran da zuciya take ciki, irin kukan da kana ganin mai yinsa ka san yana cikin tafasa da k’unar zuciya.
Ba wanda ya fito daga Sarki har Tauraruwa duk da suna jin saurin kukan nata da yake da k’arfin gaske take yin sa. Har ta gaji don kanta ta mik’e zuwa b’angarenta don ta fara tattara kayanta kamar yarda Maimartaba ya bada sak’o a gaya mata. Tana ha’da kayan tana jin b’acin ranta na sake ninkuwa ita ce yau zata bar sashennan sashen da duk k’uriuciyarta a ciki ta yi shi ta hayayyafa kuma. Me yasa ta bi son rai ne ta bi zugar she’dan ga shi nan ya kai ta ya baro ya wurgata a motar Dana sani…. Y’ay’anta ma sun gujeta ba sa zuwa ko inda suke. Ta dinga jin zuciyarta na turiri.
………….
Kwana uku tsakani Su Baffa suka shirya tafiya Yola saboda yarda Nene ta kasa Alkunya ta nuna musu iyayenta take son gani da y’an uwanta gaba d’aya. Hakan yasa kan dole aka shirya tafiyar. Sai dai kafin su tarin sai ga wayar Tauraruwa tana sanar musu su yi zamansu ba sai sun je ba, su Inno d’in za su je Kanon kashegari Idan Allah ya kai mu. Nene bata so ba amma don dole haka ta hak’ura kada a ga ta fiya rashin hak’uri ta jure hak’urin shekaru ma don haka na rana guda d’aya ba zai gagara ba In sha Allah. Suka mayar da kayan aka kuma shiga shirin tarar su dama gidan a hargitse yake dalilin gyaran biki da aka fara. Umma duk ta kwashe kayan furnitures d’inta Jaheed da Faruk za su saka mata y’an waje masu tsadar gaske. Kamar yarda suka ha’da ku’di suka Yi wa Najee kayan d’akin suka bawa Baffan da cewa sai ya k’ara da nasa. Tuni Mahmeey ta samu labarin Auren da za’a yiwa Najeen da Y’ay’an Jaheed hankalinta ya tashi zuciyarta ta afka kogin nadama da dana sani ta tabbata ita ta cuci y’arta da yanzu take cikin tsananin damuwa na rashin aurenta ga Jaheed d’in ko kallo bata ishe shi ba. Ita kuwa Khaireey tun bayan da ta ji wanda Najee zata aura sai ta yar da makaman yak’in ta kuma bawa Umma hak’uri bayan Jaheed ya tursasata bisa dole don Najee ta gaya masa duk abinda ya faru. Umma tana murmushi ta dafata ta ce “Bakomai Khaireey sai dai ina son ki cire wannan zafin kishin a ranki, Namiji Mijin mace hu’du ne don haka baki da hurumin da zaki hana Mijinki aure saboda son zuciya ki tsarkake zuciyarki dafatan samun abokiyar zama ta gari ya kuma kareki daga dukkan sharrinta ke da ahalinki ya kuma kintsawa Mijinki soyayyarki fiye da kima. Idan kika rik’e wannan tabbas kin rik’e babban makami.” Ta d’aga kai tana fa’din “Shikkenan In sha Allah Umma nagode.” Jaheed kuma murmushi ya saki yana furta “Madallah da Uwa ta gari. Sanyin idaniyar y’ay’a a duniya.” Tun daga lokacin Khaireey da Najee suka d’inke take kuma bata shawarwari da wayar mata da kai a b’angaren aure. Wani abin idan ta gayawa Najee zunb’ura baki take ta ce “Mhmn sai kace wata y’ar iska? Allah ya kiyaye.”
Khaireey murmushi take ta ce “Allah ya kaimu lokacin da zaki amsa sunan y’ar iskar da kan ki, na ganki kina tan’dar lab’ban Murad ko kina shigewa jikinsa…” wani yawu ya tofar tana yamutsa baki tace “Bakinsa kuma mhmhn? Allah ya min tsari, yawun zan sha sai kace wata k’azama.” Khaireey ganin sam Najee ba zata fahimceta sai ta ja baki ta tsuke a ranta tana dariya dafatan Allah ya kai mu lokacin zata bata amsa daidai da kalamanta.
Kashegari tun wuri aka kammala komai a gidan Baffa dalilin manyan bak’in da za su zo. Jaheed ma da matarsa tun safe suna gidan haka Faruk da nasa Iyalan.