← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 43

Sashe 14

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bai d’au lokaci ba ya sake dawo min wannan karan razanar da yake ciki har tafi ta baya, ya zube a gabana yana zufa ya furta “Shikkenan Tauraruwa sun fasa dashen wai, amma a gobe za su bawa Maimartaba wani magani da zai bugu sosai har ya sadu da ita bai sani ba, itama kuma ba zasu Bari ta sani ba don za su bugar da ita, duka na ji zantukansu ne ta inda suke sirri ba tare da sun san ina wajen ba, sai dai cikin rashin sa’a ina juyowa suka gan ni, da sauri suka biyo ni da k’yar na b’ace a cikin duhun bishiyu amma na san sun ganni kuma wallahi kasheni za su yi. Don ina ji D’aya daga cikjnsu yana furta “Mu kashe shi in dai mun same shi don bayyanuwar wannan sirrin kamar katsewar numfashin mu ne a duniya kun san sarai Maimartaba ba zai bar mu ba. A yanzu na lura Tauraruwa ba burinsu Samun Magajin Sarki ba burinsu tarwatsa duk wani farin cikin Sarki burinsu b’ata masa suna da saka wa mutane tsanarsa a zuciya kin kwana da sanin yarda Al’ummar Gabas suka tsani Zina suke kuma gaba da duk mai aikatata ina ga ace Sarkine da kansa ya aikata, na san tawa ta k’are tauraruwa da ni da dukka Ahalina sai dai ina ina rok’on alfarma a gareki ki kula min da Yarinyata ki tsare min mutuncinta don Allah.” Ya fa’da yana sakin wani irin kuka mai bayyana da gaske bankwana yake, abinda ya sake dugunzuma min kwanya. Na saka shi ya shiga wani d’aki na rufe d’akin na datse da d’an mukullin da ke hannuna, kafin na shiga wani d’aki na yi shigar da zata b’atar da dukka kamannina na koma kamar wata Bafadiya don irin shigarsu na yi. Ban ji tsoro ba na fito daga sashen da ba kowa a cikinsa daga ni sai halina don sashena mai tsohon tarihi tun kakaninmu anan suka yi zamanin su don haka duk wani abin tarihi na masarautar gabas yana cikin wannan b’angaren ba wanda ya damu da shigarsa don sai a yi shekara ma baa bu’de shi ba, daga shekara sai shekara ake shigarsa a lokacin hawan Sarki na bikin k’aramar Sallah daga nan shikkenan don ko bikin hawan Babban Sallah baa bu’de shi.

Tsakiyar dare ne don haka ba kowa a wajen sai kukan tsintsaye, a nutse nake tafiya zuciyata cike da tsoro sai dai k’arfin hali irin nawa yasa na dake na isa har sashen Baffa Liman, wanda k’ani ne ga mahaifinmu da suka ha’da iyaye wato y’an maza zar suke, a gidansu kowa ya san sarautar Limancin Babban Masallacin Gabas yake.

A k’ofar shiga sashen nasa na tsaya, na yi kuma k’ok’ari sosai wajen kaurara muryata har ta dawo kamar namiji na ce wa mai tsoron sashen ya min iso a wajen Baffa Liman Ina son ganinsa ne a uzurce nake. Shiru mai gadin ya yi kamar ba zai je ba sai kuma ya juya zuwa zauren gidan wanda na tabbatar addu’ar da nake ce tasa ya tafi ba musu. Tsawon mintoci kafin Ya fito ya iso inda nake da hannu ya ce min “Bismilla ya ce ka shiga.” Na kuwa dogara y’ar sanda ta da ta mayar da ni kamar tsoho na isa zauren inda anan ne d’akin da Baffan yake ganawa da mutane.

Gyaran murya ya yi kafin ya d’an haska ni da torch light ya ce “K’araso wani bak’o muka samu cikin daren nan.” Ban yi magana ba sai dai na k’arasa zuwa saman buzun da yake nuna min. Na zauna sosai kafin na saka hannu na yaye mayafin hiramin da yake kaina kamanina na Tauraruwa da na san ba zasu tab’a gogewa a idanun Baffan ba Suka bayyana, wani irin fitgita Baffan ya yi kafin ya yi baya da sauri har torch light d’in hannunsa na fa’duwa yana fa’din Subhanallahi me nake gani haka? Ashe dai da gaske ana fatalwa? K’ok’ari yake ya zunduma ihu na yi saurin saka hannu na toshe bakinsa ina rik’e dariyar da take son sub’uce min na ce “Baffa ka nutsu ni ce, Tauraruwa ce a zahiri Ba fatalawa ba, ban mutu ba ina raye ina son wannan kuma ya zama sirri a tsakanin mu….” Jikinsa bai bar rawa ba sai dai ya d’an nutsu ka’dan ya zauna sosai yana kallona ya ce “Ki rantse da girman Ubangijjnki ba fatalwa ba ce ke..” Na saki murmushi na ce “Wallahi Baffa ni ba Fatalwa ba ce, ka ji na rantse maka ba wanda ya san ban mutu ba daga Amintacee sai kai da yau na zo neman taimakonka.” Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ce “Ke kuwa Hajiya mai ya kai ki aikata haka?” Labari na bashi, labarin da na lura ya firgita shi matuk’a da gaske don zufa yake gogewa sosai a goshinsa ya ce “Hasbunallah yanzu kina nufin su ne suka aikata haka?” Na d’aga kaina cike da gamsarwa na ce “Wallahi Baffa, shine yanzu na zo neman taimakonka, na tabbata ko maimartaba aure zai yi kai ne dai Waliyyinsa wanda zai amince ka karb’ar masa aure don haka nake son kafin goben burinsu ya cika mu je da kai wajen Amintacce wanda shine Uban yarinyar a d’aura aure a gidana ka bashi sadakin y’arsa da duk abinda shari’a ta tanadar.” Liman ya jinjina kai ya ce “Hakan da kika yi shine daidai Hajiya, amma a ina kike ga zamu samu shaidu da zasu zame mana shaida ko nan gaba.” Shiru na yi ina tunanin mutane uku da zuciyata ta amince da su, na san kuma ba zasu tab’a k’in goyon bayan abinda nake so ba, don haka kai tsaye zuciyata ta amince da na kirasu na saka su a matsayin shaidu su ma. Baffa Liman da kansa ya saka aka nemo masa mutane ukun da na ambata wanda shima kai tsaye ya ji zuciyarsa ta amince da zab’i na.

Sanda suka shigo suka ganni su ma ba k’aramar firgita suka yi ba, sai da na kwatanta musu irin ta Baffa Liman sannan Suka amince da ni, don haka ba b’ata lokaci muka isa tsohon gidan tarihi cikin tsakiyar dare sanda kowa yake kwance a mashimfi’di. A daren ranar juma’ar aka d’aura auren Maimartaba da mahaifiyar su Murad wato wannan baiwar Allahr Nene da ke tsaye….

Gaban Nene da na Maimartaba har ma da na su Fulani ba k’aramar fa’duwa ya yi a wajen ba, idanun kowa ya fito waje tun kafin Tauraruwa ta k’arasa labarin kowa ya shiga firgici musamman wa’danda Suka san Suna da ruwa da tsaki a cikin duk abubuwan. Hayaniya ta fara yawa a wajen. Murad da Jaheed kuwa wata irin runguma suka kaiwa Nene tsananin farin cikin da suke ciki ya kasa b’oyuwa. Maimartaba ma murnar yake yana ta kallon su Jaheed cikin tsananin k’auna tare da mamakin yarda aka ce wai Nene matarsa ce ta ya hakan ta kasance don dai shi ya san ko a mafarki bai tab’a ganinta ba balle har ya kusanceta irin kusanci da Namiji yake wa Mace har a samar da ciki a cikin mahaifa. Ya gyara zama yana jiran jin k’arashen labarin a bakin Tauraruwa da murmushin kan fuskarta ya kasa b’acewa.

Gyaran muryar da ta yi a loudspeaker ne yasa aka yi shiru don son cigaba da jin labarin da yarda aka haihu a ragaya.

An d’aura auren cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai me? Muna shafa addu’a muka ji an turo k’ofa… hankali tashe muka d’aga kai don ganin waye?

Kun san dai bana typing weekend wannan ma na alk’awarin da na d’auka ne na cika shi don haka ku yi hak’uri da abinda ya samu.

JIKAR NASHE✍🏽🥳

08033748387.
Chapter 14 · 0% Book details