Sashe 6
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nene ma da k’arfin gaske take yafito yawun bakinta take ha’diya don yawun bakin gaba d’aya ya k’afe k’af, jin mak’ogoronta take a bushe kamar baa tab’a halittar yawu a wajen ba. Suna yara sanda abubuwan suka faru har ta rasa ranta amma sam hakan ba zai saka ta manta da fuskar matar ba. Ta girmesu a shekaru amma alherinta ga al’umma kamar ba jinin sarauta ba yasa ta samu soyayyar jama’a kowa yake rububinta da gasken gaske. Abubuwan suka dinga dawo mata kamar majigi a kwanyarta ta dinga kallonsu kamar wancan lokacin da abubuwan suke faruwa a zahiri. Hannun Najee ta kama ta damk’e da k’arfin gaske tana sake runtse idonta zuciyarta na bugu saboda razanar da take ciki. Idan har ya tabbata ba mutuwa ta yi ba tabbas akwai gagarumar k’ura a masarautar gabas! Najee ta juyo tana kallon yarda hannayenta suke kakkarwa a tsorace ta ce “Nene lafiya menene?” Yatsanta ta saka a baki alamar ta yi shiru tana girgiza mata kai idanunta cikin na Najwan itama Najwan ita take kallo tana mamakin yarda idanun Nene suka jirkita zuwa jajaye sosai da alama tashin hankalin da take ciki ba shi da ma’auni balle a taskance mizanin sa. Sai itama ta ji tata zuciyar ta firgita bata san sanda ta koma jikin Nenen ta lafe ba tana danne k’irjinta da yake bugawa da k’arfin gaske.
Sarki Mukhtar ya cigaba da kallonta ita d’in ma shi take kallo kafin ta saki murmushi tana fisgar leb’enta. Sannan ta sauke idanunta akan Hadiman da cikinsu har da me rawar d’ari. “Kuna mamakin dawowata ne bayan kun binne ni a kushewa.” Sai ta lumshe ido hawaye suna bin k’uncinta. “Allah ya nufi dawowata cikin Amincinsa bayan dawowartawa kuma sai yasa na dawo har da y’ay’ana na halak malak. Bayan Murad da kuke gani akwai k’aninsa Jaheed, wanda ya yi aure yana da matansa biyu, a yanzu ne zaku fuskanci duk abinda Allah ya so ko ana muzuru ana shawo sai Allah ya k’addara nufarsa.” Ta fa’da tana sakin murmushi ta cigaba da takun isarta zuwa inda sarki yake a zaune ta zauna a gefensa kujerar da ba wanda ya isa ya hau sai shi ba wanda ya tab’a kwatanta hawanta har ta da Fulani Raheena da ake ganin ta cika ta tumbatsa. Wannan karan Nene kanta a cikin firgici take jin ashe matar wai ta san Jaheed to ta ina? Ta ina kuma suka zama y’ay’anta da har take bibiyar rayuwarsu har ta san sun yi aure? Kada dai da gaske su Jaheed y’ay’anta ne, to ta yaya ta ina kuma? Ji ta yi kanta yana wani irin sarawa ta kama hannun Najee ta sake damk’e wa da kyau kamar dai Najeen ce zata tsareta daga dukkan abin cutarwa.
“Ina raye mai martaba ban mutu ba, ka daina min kallon fatalwa am still alive and am still your’s favorite person…..” ta fa’da tana saka idanunta cikin na Sarkin da ya gama ru’dewa sai dai izza da isa ta mulki ta hana shi bayyana hakan ya daure ya jure ya d’aga mata kai alamar ya gamsu, duk da har a zuciyarsa bai gama gamsuwar ba. “A tashi taron nan mai martaba bana buk’atarsa don ni na yiwa yaro na mata zarka’ded’iya ba wacce kuke so ku Aura masa ba, tuni an d’aura masa aure… don haka yanzu nake son a sallamesu.” Ba wani Ja Sarki ya kalli Bafadensa d’aya ya masa alamar da ya sallami jama’ar wajen. Take kuwa aka sanar da mutane an fasa wannan aure don haka kowa ya tafi. Aka rufe sarki don ya mik’e ya shiga cikin zabgegiyar motarsa matar tana gefensa kamar ta shige jikinsa ta bi bayansa suka shiga motar mutane sam ba su yi mamaki ba, don sun san duk wanda sarki zai so a rayuwa to bayan Tauraruwa ne sunan da yake gaya mata kenan a zamanin da take raye. Murad ta yafito da hannu ta masa alamar da ya shiga da sauri ya girgiza kai yana kallon Mamma da ta kafa masa ido don haka kai tsaye ya bi bayan Mamma. Tauraruwa ta saki murmushi kawai tana girgiza kai. Aka ja motar Sarki zuwa fadarsa ta cikin gida.
Fulani Raheena kasa jiran motar ta yi sabida yarda zuciyarta take a hautsine da sauri ta bi ta wata siririyar hanya don isa sashenta tana jin duk duniya ba wanda ya kai ya tashin hankali, duk da ba ita ta aikata komai ba amma ta san komai ta san kuma wa’danda suka aikata. Sauri take kamar zata tashi sama bata bari kowa ya ganta ba balle a bita ta shige sashenta, ta mayar da k’ofar ta rufe da k’arfin gaske, rufewarta ta ya yi daidai da bugun zuciyarta kamar zata b’alle k’irjin ta fito. Ta fige mayafin kanta da alkyabbar da ta jik’e da gumi kamar ta shiga ruwan sama. Har ta suman kanta d’igar gumin take, zaman dirshan ta yi a k’asa tana tura yatsun hannunta cikin sumar kanta da ta tashi kamar ta mahaukata a firgicen ta ce “Na shiga uku ni Raheena? Komai ya lalace min dama wannan matar ba ta mutu ba, suka min k’arya ta mutu suka saka na sakankance da cikar dukka burikana, wayyo Allah na ni Raheena tabbas b’aragurbin k’wan gab yake da fashewa warinsa kuma zai iya kashe al’umma da dama a cikin Garin Gabas. Bata san hawaye take ba sai da ta ji d’igar su a saman harshenta ta lumshe ido tana sake datse leb’enta. A fili ta furta “Kun cuceni! Kun jefa ni a Ramin da ba mai iya fitar da ni sai Allah, sai dai ina tabbatar muku wannan abin har ku zai shafa Ba Raheenatu ita ka’dai ba.”
Ta fa’da tana sake hargutse sumar kanta. Bugun k’ofar da ake ne a sassanta ya saka cikinta sake hautsinawa da sauri ta fa’da toilet gudawa ta yi sosai kafin ta fito ta nufi parlourn ba tare da ta rufe kan nata ba ta ce “Waye ne?” “Wanda kika san zai zo.” Aka furta daga can. Raheena ta ware ido tana mamakin jin Muryar yau a zahiri duk da da sai dai ta ji ta a cikin waya ko a cikin duhu. Da sauri ta saka hannu ta zare mukullin tana murnar ganin ko wane shege ne mai bata umarnin da sam bata iya ja da shi a zahiri. Idanunsu ne suka sark’afe cikin na Juna hanjin cikin ta ya sake hautsinawa ta bu’de idonta a razane ta ce “What? Dama kai ne?” Murmushi ya sakar mata yana tureta gefe ya shiga cikin parlourn bayan ya mayar da k’ofar ya rufe ta ruf. Ya k’are wa d’akin kallo kafin ya mayar da kallonsa kan Raheenan da idanunta still suke a waje gashin kanta da yanayinta ya nuna ta a matsayin mahaukaciya sabon kamu. Murmushi ya saki ya ce “Tun yanzu Raheena? Tun komai ma bai faru ba na gan ki a haka? Ina ga idan wad’ancan sirrikan suka bankad’a. Kin ga zauna magana nazo mu yi ta nutsuwa. Idan kika sake kika bayyana sirrin da ya da’de lullub’e a cikin k’asa wallahil azeem sai na sanar da sarki wacece ke? Bana son jin sunana a maganar kisan Tauraruwa don na san kin san komai duk da ba hannun ki a ciki, wallahi kika sake kika tona mana asiri sunan naki sirrin banka’dadde.” Ya fa’da yana sakin dariya sannan ya juya ya fice da sauri duk da a firgicin yake shima hakan bai hana shi nuna jarumta ba da nuna bai san komai ba. Raheena ta bi bayansa da kallo tana jin tashin hankalinta na sake hauhawa me yake nufi? Ta b’oye laifinsa da kai tsaye za’a jingina mata laifin ko me? Shikkenan ita Raheena ta zama mai laifi kashi kashi kenan? Idan kuma bata b’oye laifin ba haka na nufin fashewar b’aragurbin k’wan kenan? Cabd’ijam! Tabbas Ni Raheena ina cikin matsala. Ta furta a fili.
Fulani Saddik’a kuwa jikinta a salub’e yake sosai, duk wani karsashinta ya gudu sai tsoro da jin kamar shikkanan za’a rabata da Murad da take jin sa kamar gudan jininta. Ta shiga sashenta hannunta cikin na Murad da sam ya kasa sukuni da walwala shima zuciyarsa a cikin ru’danin take, neman wanda zai sanar da shi wacece waccan matar yake? Yana jin nauyi da kunyar tambayar Mamma duk da itace Tambayar da son amsarta ya fi kowace tambaya a wajensa. Maganar matar da take ikirarin aura masa ba matsalar sa ba ce muddin matar bata masa ba sakin ta zai yi, ba ruwansa da wai itace mahaifiyarsa me yasa tana son sa ta wullar da shi kuma wanene Jaheed da har take kiransa d’an uwansa?