Sashe 10
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin dare Murad ya kasa runtsawa so yake kawai ya ga Nene ya gaya mata shawarar da ya yanke da zuciyarsa, sai dai baya son ya ganta a gaban Fulani don haka ya bari sai cikin daren ya mik’e daga shi sai jallabiya mai masifar kyau sai shinning take ya bi ta wata k’ofa zata sadashi da b’angaren Fulanin.
Shiru b’angaren Fulanin sai masu tsaron k’ofar da wasu daga cikin barorinta da suke kai kawo a parlourn. Ya d’an bi su da kallo suna kai masa gaisuwa ya yi saurin dakatar da su, kai tsaye ya isa sashen Nenen tura k’ofar kawai ya yi ya shiga d’akin. Nenen da take zaune akan sajjada tana lazimi ta ‘dago tana kallonsa cikin nazarin fuskarsa…. Ya zube a gabanta yana kama hannunta wanda ba ta rik’e carbin da shi ba. Suka shafa addu’ar tare sannan Nene ta zuba masa ido cikin kulawa da tausayi irin na uwa ta ce “Me ya faru Murad?” Gyara zamansa ya yi kafin ya ce “A ina d’an uwa na yake da zama?” Nene ta gaya masa da sauri ya ce “Kina da numbern layin sa na can?” Ta d’aga masa kai. Ya girgiza kansa yana furta “Lokaci ya yi Nene da zaki sanar da shi Mahaifisa ya bayyana idan yazo daga sannan ne kowa a masarautar nan zai san ke kika haife mu….” Nene ta yi saurin zuba masa ido tana fa’din “Idan na fa’di haka aka buk’aci sanin ta yaya na samu cikin ku me Zan ce?” Sai ki ce “KUDIRAR ALLAH… ni dai abinda nake buk’ata ki kira min shi ya zo garin nan ina son na ga d’an uwana na ji d’uminsa na tare da ni, ina so ya zo Nene mu yanke shawarar da ta dace da mu? Na gaji da walagigin da ake da rayuwarmu ya kamata mu fuskanci rayuwar mu ta gaba mu san mu su waye shegu ne mu? Ko kuma da gaske mu y’an halak ne don haka ki kira sa please yanzu….” Nene ta saki ajiyar zuciya tausayin Murad na kamata bata san sanda ta danna kiran Jaheed ba, bugu biyu ya d’aga cikin d’oki ganin numberr Nigeria ce, jin muryar Nene da ya yi a cikin wayar ya saka shi sakin ajiyar zuciya ya ce “My Nene ina jin ki?” Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Jaheed lafiya k’alau, ya kamata ka zo Nigeria Zan nuna maka mahaifinka da d’an uwanka….” Wani irin duuum Jaheed ya ji a kwanyarsa da k’arfin gaske ya ce “Da gaske Nene? Are you sure za ki nuna min su? In dai kin tabbatar to zan taho Nigeria a gobe da daddare…” Nene ta d’aga kai ta ce “Da gaske nake Jaheed a yanzu haka ma ina tare da Usaininka….”
JIKAR NASHE✍🏽🥳
Saboda wani uziri da yake tare ni, ga duk masu bibiyar litattafaina sun san baba typing ranar asabar don haka yanzun ma ina neman afuwarka a wannan tafiyar ma ba typing d’in asabar sai dai lahadi In sha Allah. Nagode sosai Najee na gaisheku, ta ce labarinta na gaba tata k’addarar na gaba dafatan zaku cigaba da bibiyar ta.
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ta idanunsa na gano bai yi na’am da shawarata ba, kuma a tsorace yake da abinda na fa’da d’in, don haka don son kwantar masa da hankali sai na yi murmushi na girgiza masa kai na. “Abinda kake nufi nake nufi ba Amintacce, ba nufi na zan amince su kashe ni kamar yarda suka buk’ata ba, sai dai zan ba su damar da zasu kashe ni d’in ba tare da na mutu ba…” wannan karan sosai na saka shi a cikin ru’dani fiye da baya, ba mamaki bai fahimci juyayyaen zance na ba. Na sake jifansa da murmushi “Da kai ka’dai na yarda shi yasa nake gaya maka duk sirrina, Mijina kafin ya rasu kai ne mutum na farko da ya amince da shi ya kuma yarda ya gaya masa duk sirrinsa, D’ana guda d’aya tak da nake da shi kai ne kake masa rik’on mahaifi bayan Mai martaba don haka nima na baka dukkan yardata zan kuma sanar maka da sirrina don na san ba zaka zamo mai tona min asiri ba. Na san a yanzu da suka samu labarin zan yi tafiya za su saka himma wajen son su ga sun kashe ni a hanya don haka zan shiga motar da na zab’a don na san tuni sun shirya kashe ni a cikin ta, sai dai da kai zan yi tafiyar amma ba tare da sun san da kai zan yi ba. Muna fara tafiya bayan barin mu gari zan buk’aci na kewaya a cikin daji tanan zaka samu damar jan mutanen cikin motar ka ce su je su nemo ni bayan da’dewa da tafiyata ban dawo ba kuna shiga ni kuma zan fito zan sakawa motar wuta na kuma koma cikin dajin na b’uya kuna zuwa na san zaku yi tunanin na mutu a ciki amma fa kada ka sake ku dawo sai kun d’au lokacin da ka tabbatar motar ta ci wuta sosai.” D’aga kansa ya yi cike da amincewa da shawarata. Ba waya a lokacin don haka tilas za’a buk’aci a je gida a sanar shi Kuma sai ya yi amfani da wannan damar ya saka ni a
Wata motar ta haya zuwa inda na nufi guduwa, na ba shi address da komai na Garin da kuma gidan da zan zauna kafin na b’ace na bar k’asar. Bayan cikar buri na na ganin Maimartaba ya samu Magaji. Shi Amintacce shine zai zame min mai lek’en asiri a gidan sarki. Don haka idan komai ya lafa na ce masa zan dawo gidan Sarkin da zama cikin b’atacciyar shiga can wani sashe da ba wanda yake shigarsa a gidan saboda wajen tarihi ne Amintacce kuma shine mai kula da b’angaren.
Duk wa’dannan abinda na shirya d’in haka suka tafi successfully ba tare da kuskure ko ka’dan ba. Hankula sun tashi sosai da jin labarin rasuwata an Kuma gaya min duk halin da Maimartaba ya kasance a ciki akan rashi na. Burin wa’danda suke so kashe ni ya cika aka dinga murna bayan an je an tabbatar da ko b’urb’ushin gawata babu a wajen. Na yi irin mutuwar da suke so mutuwar da Sarki ko gawata ba zai gani ba balle ya tuna. Tun ranar da aka yi jana’iza ta Sarki ya saka aka kwashe duk wani abu da zai dinga tuna masa da ni ciki kuwa har da hotuna na da ma sunan Tauraruwa gaba d’aya, wanda shi ya saka min da kansa tun muna yara saboda ni ka’dai ce y’ar Uwarsa da muke ciki d’aya. Bayan afkuwar lamarin da wata guda na dawo cikin masarautar gabas cikin wata sirrintacciyar hanya a kuma wani sirrintaccen dare na kuma zauna a sirrintaccen waje da ba wanda ya san da shi sai amintacce na abokin sirrina.
Tun daga lokacin muka dinga saka ido akan duk abubuwan da suke faruwa a cikin masarauta, suna can suna shirin su na don cutar da sarki da kawo masa b’aragurbin d’a ko na waye ba don komai ba sai don su samu cikar burinsu na hanb’are Maimartaba daga kan kujerarsa, kujerar da suke bak’in ciki da kasancewrsa a kai. A wannan lokacin da idonsu ya rufe suke son lallai sai Raheena ta samu d’a da za’a kira jinin Maimartaba har suka tara da d’aya daga cikinsu wanda shi ya san kansa aka kuma samar da cikin sai dai a haka na dinga bin dare da taimakon amintacce muka dinga canja yaran da gawar jarirai muna d’auke wa’danda suka haifa da taimakon Matar Amintaccen da ta zama itace Unguwar Zoma a cikin masarautar. Duka wannan abinda ake ba wanda ya sani, a haka ganin tabbas Raheena ba zata samu rayayyen d’a ba sai Suka canfata da cewa haihuwar wabi take don haka suka komawa biyu daga cikin matan Sarki wa’danda suka san kai tsaye zasu amince banda Saddik’a da Suka san koda wasa ba zasu tab’a zuwa mata da maganar ta yarda kai tsaye ba. Tsautsayi yasa Raheena ta fara kishi da matan Sarkin da suka amince a haka har ta musu shune a wajen Sarkin a zuwan cewa k’annensa suna tarayya da su. Ya tsananta bincike ya gano da kansa hakan yasa ya musu sirrintaccen saki ba tare da kowa ya sani ba ba don komai ba sai don gudun b’ata sunan zuri’ar sa a masarauta ko b’ata sunan k’annensa. Wannan ya wuce ba su san kuma Raheena ba ce ta aikata duk wata kitimurmura.
Ganin hak’ansu ta kasa cimma ruwa sai suka koma bin y’an mata suna musu fyad’e da niyyar idan sun samu ciki su d’auke su su b’oye har sai sun haihu. Nan ma burinsu bai cika ba don labari da ya ishi kunnen Maimartaba sai ya sanya tsatstsauran mataki da ba ta yarda za’a yi shirinsu ya yi tasiri. A wannan lokacin burinsu b’ata sunan Sarki da yi masa shirin aikata zina shima ta yarda Al’al’ummar Gabas za su yi tur da shi har a tsige shi daga sarauta.