Sashe 5
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun bayan isar su turakar mai martaba ta mayar da k’ofa ta rufe tana nazarin d’akin da k’amshinsa yasa ta fara tuna duk wata rayuwarta ta baya komai a d’akin bak’o ne a wajenta idan banda Maimartaba da bai sake mata daga mutumin da ta sani ba, barin ma yanzu da take zaune daf da shi yana sanye cikin jamfa da wando kansa ko hula babu. Ya zuba mata ido yana mamakin yarda aka yi ta rayu tsawon shekaru talatin ba tare da ya ji a jikinsa cewa tana raye ba, me yasa ta b’oye masa sai yanzu taga damar bayyana kanta bagatatan, shin bata san irin yanayin da ya shiga ba tun bayan rasuwarta bata san da k’yar walwalar sa ta dawo ba. Haushi take ba shi ta yarda ta bagarar da lamarinsa tsawon wad’annan shekarun don haka ya kasa ce mata komai illa zuba mata manyan maganansa da ya yi, yana mata kallo da ta tabbatar na tuhuma ne da neman ba’asi. Sai dai ta k’i furta komai kamar yarda yake so illa juya cup d’in futar hannunta da take cikin nisha’di tana sakin walwala ta kai cup d’in furar bakinsa kamar yarda ta saba a Zamanin baya in dai tana kusa ita take ciyar da shi ta shayar da shi bata amince wani ya ba shi komai ba sai ita da kanta. Kamar zai bu’de bakin ya sha sai kuma ya doke hannunta furar ta zube musu a jiki gaba d’aya. Murmushi ta saki tana furta “Haba mai martaba Tauraruwarka ce fa, Sadauki baya fushi da tauraruwarsa ina neman afuwa ka sha furar nan zan sanar da kai yarda duk abubuwan Suka faru a haka da kuma dalilina na aikata hakan.” Haka kawai ya ji zuciyarsa na rawa ya ji kuma yana son k’aryatata sai ta ga ya mik’a da sauri ya fisge d’ankwalin da yake kanta da mayafin da yake kanta. Gashinta ya ja sosai ya duba tsakiyar kanta sai ga abinda yake nema a bayan wuyanta wata babbar tawadar Allah ce a gefen wuyanta, ya mayar da gashin nata da ya kwanta har gadon bayanta yana sakin ajiyar zuciya. Kallonsa take tana sakin murmushi ta ce “So that yanzu ka yarda nice dai Tauraruwarka ba fuska na saka ba ko?” Ya d’aga kai a hankali kawai ba tare da ya ce komai ba ya koma ya zauna yana kallon zoben hannunta da nasa ne ya bata shi tun kafin ta mutu nan ya sake tabbatar da dai tauraruwa ce a gabansa ba wata ba sai ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa murya a cunkushe ya ce mata “Ina saurararki gaya min dalilin da yasa kika yi k’aryar mutuwa alhali kina raye?” “Saboda ka samu magaji, na san idan ba haka na yi ba har abada ba za su barka ka samu magaji ba. Yanzu kuwa da na aikata haka ba gashi komai ya zama sai labari ba, bayan Murad kana da d’a Jaheed yana nan kuma cikin k’oshin lafiya har da matansa biyu……” wani irin kallo ya mata ya ce “Ta yaya aka yi aka aurar min da d’a ba tare da sani na ba? Tauraruwa wani irin abu ki aikata haka? Kuma da gaske kin tabbata yaran nan y’ay’a nane na halak, za kuma ki bada shaida a duk inda aka buk’aci hakan?” “Nima ban san an aurar da shi ba, don ban bayyana kaina ba a wajen iyayen rik’on sa sai dai yanzu nake son sanar da su komai…. Jaheed da Murad kamarsu d’aya don ba zaka iya banbance kamaninsu ba sai dai ta banbancin halayya. Kuma ko Kur’ani za’a bani na dafa zan tabbatarwa da duniya d’iyoyinka ne halak.”Maimartaba shiru ya yi ransa yana sake dugunzuma yana b’aci ace d’ansa na cikinsa bai san da shi ba har ya yi aure? Sabida kawai tsoron sharrin magauta ashe kuwa lokaci yazo da ya kamata ya fuskanci magautansa idan ta kama ko yak’i ne zai yi da su Wallahi don sun zalunceshi. Farin ciki guda da yake da ya zama tabbas Murad da Jaheed yaransa ne na halak, ba kamar yarda al’umma ke zargi ba, sai ya samu zuciyarsa da samun nutsuwa fiye da fargabar da yake ciki a da. “Ka yi hak’uri duk na aikata haka ne a bisa son cetoka da ni kai na daga b’aragurbin mutanen da suke cikin Fada burinsu na kashe ni bai cika ba duk da k’ok’arin su na aikata haka.” Ya d’ago yana kallonta sai kuma ya jinjina kai ya kasa furta abinda yake ransa, gani kawai ta yi ya mik’e ya shige toilet hakane ya bata damar mik’ewa itama don fita daga d’akin zuwa nata d’akin da yake gaba da parlournsa ka’dan. Tun asali anan b’angarenta yake bata tab’a yarda ta yi nisa da mai martaba. Tana tura k’ofar Murad na kai hannu da niyyar kwankwasawa. Turus ya tsaya yana kallonta idanunsa cikin nata zuciyarsu na bugawa lokaci guda. Tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafin ta janye nata idon ta kama hannunsa tana furta “Haba farin cikin rayuwata baka yi murna da gani na bane d’an Mamansa…” Hannunsa ya janye a hankali yana furta “Ba ke ce Mamana ba ina son sanar da ke haka don ko a yanzu ina tare da Mamana….” Ta d’ago tana masa wani kallo sai kuma ta saki murmushi ta zare hannunta cikin nasa ta yi hanyar tafiya murya a k’asa ta furta “Har abada ni Uwarka ce Murad! Duk da ban yi nak’udarka ba amma kai d’ana ne halak malak, duk duniya ba wanda ya isa ya canjawa tuwo suna, Albishir guda da zan maka ka shirya nan da sati guda zaka tare a gidanka da matar da na aura maka!” Ta shige sashenta ta bar shi a tsaye yana cizar leb’e da mamakin wacece ita da take magana murya cike da confidence. Ya yi kwafa yana cigaba da nocking d’akin Maimartaban. Fitowarsa daga wankan gumin da ya sha saboda firgici kenan ya ji bugun k’ofar kamar za’a b’alle k’ofar mamaki ya kama shi, sai kuma ya saki murmushi sanin cewa Tauraruwa Uwar rigima ta sake bayyana wato halinta na nan na rashin uziri ga kowa a duk sanda ta so wani abu. Bai damu da jallabiyar da ke jikinsa ba ya yar da towel d’in hannunsa kafin ya saka hannu ya mur’da handle d’in, sab’anin tauraruwa Murad ya gani a tsaye yana mayar da numfashi kamar wanda ya ci tseren gudu. Kamar Uwa kamar d’anta, sau tari ya sha kwatanta d’abi’u da halayyar Murad da na tauraruwa ashe dai tabbas jininta ne. Murmushi ya sakar masa yana furta “Ran Sarki ya da’de lafiya ake min wannan bugu haka?” Mamaki fal fuskar Murad ya zubawa Sarkin ido yana mamakin fara’ar da yake gani da walwala a fuskarsa alamar yau a cikin farin ciki yake, zai iya cewa tun tashinsa bai tab’a ganin Sarkin a yanayin farin ciki irin wannan ba. “Shigo Murad, don na san abinda ya kawo ka.” Maimartaba ya fa’da yana saka tarin hannunsa cikin na Murad d’in da yake tsaye kamar mutum mutumi. Bai bar shi ba sai da ya zaunar da shi a bakin tattausan gadonsa ya koma ya cigaba da shafa kansa har yana yin y’an wak’a mamaki ya dinga neman kashe Murad a zaune. Sai da y fesa turarukansa sannan y taje sumar kansa kamar wani sabon ango sai ya dawo gurin Murad ya zauna daf da shi yana furta “Da gaske itace Mama ta?” Na san shine tambayar da kake son yi min. Amsar itace “Eeh da gaske Tauraruwa itace Babarka duk duniya baka da wata Babar da ta zarce ita………
JIKAR NASHE✍🏽🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: KUDIRAR ALLAH BOOK 2.
(Don Allah ku zamo masu rik’on amana, idan kin san kin siyi littafina ne don ki watsa shi a duniya don Allah tun ban yi nisa ba ki gaya min na dawo miki da ku’dinki. Ina yin littafi kyauta Amma wannan dai ban yi niyya ba. Don haka pls ku kiyaye kada mu zo muna samun rashin fahimta da mutum kuma ya k’ulla ce ni, Allah yasa ku ji kuma ku bi, idan kun bani ha’din kai zaku ji da’din harka da ni In sha Allah.🤗)
08033748387.
.
Da yawa daga cikinsu k’wak’walwar su da tunaninsu ya daina aiki na wuncin gadi. Tsoro da fargaba ya ziyarcesu suka rasa sukuni a zuciyarsu. Harta Sarki wani irin gumi yake yarfarwa. Bai tab’a tunanin abubuwan da suke ji a tatsuniya za su iya kasancewa a gaske ba, wato Fatalwa! Shin dama wanda ya mutu yana dawowa ne? Shine tambayar da ya yiwa kansa a zatonsa a zucuayrsa ya yi tambayar sai dai kallon da fadawa suka masa ya saka shi sanin cewa lallai a zahiri ya yi maganar. Don suma da alama tambayar da suke son yi kenan sai dai zuciyar kowa da bakin kowa ya kasa bari ya yi furucin tsoro ne sosai a ransu, ji suke kamar su dare su bar wajen. Wani abu ne da kai tsaye za’a iya kira ALMARA ko irin mafarkin nan mai wuyar sha’ani.
Su kansu matan Sarki sun girgiza da ganin wannan baiwar Allahn idanunsu duk a waje suke suna cigaba da kallon Fatalwar matar a tsaye a gabansu tana sakin murmushi cikin isa da ginshira kamar dai yarda take kasancewa a lokutan da suka gabata. Fulani Saddik’a kanta a firgicen take, balle Fulani Raheena da take jin kamar ta saki fitsari a wando. Ta runtse ido ta bu’de ya fi a k’irga duk don ta tabbatar ba wancan rud’anin mafarkin da ta saba ba ne.