Sashe 26
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
JIKAR NASHE✍🏽🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Tsananin tashin hankalin da yake ciki ya zarce duk wani tunanin mai karatu, k’ok’ari yake ya fisge takardar daga hannunta sai dai ta k’i yarda ta bashi damar hakan ta hanyar mik’ewa da mugun gudu ta shammace shi ta fice daga d’akin tana furta naga abinda yake ciki don haka maganar ka janye sakin ma bai taso ba… daga haka ta saka kai ta fice daga sashen nasa ta fa’da wani d’aki da aka ajiye dattawa biyu da zasu zauna da ita a sashen kafin ta saba wanda suka zamo na kusa ne da sarki a b’angaren dangantaka su yakewa kallon iyaye mutane ne masu daraja a idonsa da yakewa kallon mahaifa sune kuma a gurbin mahaifan nasa d’aya K’anwar Uba ce a wajensa da suke iyaye guda da ita, ita kuma Yakumbo Danejo k’anwar Mahaifiiyarsa ce da suka sha Nono guda don haka ko baa fa’da ba ka san sune iyayen Sarkin gabas. A gabansu ta zube tana mayar da numfashi da sauri suka d’ago kai suna kallonta ganin yarda ta mayar da k’ofa ya rufe garam da sauri har da murza key bayan haka ga shi tazo ta zube a gabansu tana haki hakan zai tabbatar maka da rashin wanzuwar lafiya a tattare da ita. A sukwane suma suka mik’e suna furta “Lafiya kike kuwa?” Duk da dukan da zuciyarta yake yi gefe guda kuma tana murnar cikar muradinta bai hanata yin rawar baki wajen sanar da su mutuwar auren da aka k’ulla a yau a kuma cikin dare guda komai ya faru ya k’are… idanu suka ware a razane suke kallonta zuciyarsu na bugawa da mugun gudu kafin su furta “Wani irin zance ne mara da’din ji haka? Shi Murad d’in ne ya sake ki?” Ta d’aga kanta kafin ta saka hannu ta mik’a musu takardar sakin da ke hannunta. Basu iya karatu ba don haka basu damu da su duba abinda ke ciki ba, illa mik’ewa da Hajja Bintu ta yi tana lalubar wayarta mai torchlight ta fara danna numberr Maimartaba. A bugu guda ya d’aga ta saki ajiyar zuciya ha’de da sanar da shi mak’asudin kiran, ya yi shiru kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce “Ya yiwa kansa, a taho mana da ita yanzun nan zuwa b’angaren Tauraruwa.” Daga haka ya zare wayar daga kunnensa cikin matuk’ar k’una da zafi da zuciyarsa take yi. Shi Murad zai to nawa asiri aure a rana guda a kuma yi saki cikin dare guda tabbas zai nuna masa asalin sunansa na Muhammad Mukhtar mai gabas!
Tana ajiye wayar ta mik’e don cika umarnin mai martaba “Mik’e mu je can sashen umarnin Mai martaba.” Hajja ta fa’da tana jan hijabinta ta zura a jikinta. Ta kama Najee da ta mik’e da k’yar ta bi bayan ta suka fice ta wata k’ofa daban da ta tabbata ba zasu ha’du da Murad ba.
Dubawar duniya bai ganta a cikin gidan ba ya kuma manta da d’akin da su Hajja suke. Cikin tashin hankali ya gama zagayen sashen kafin zuciyarsa ta sare ya tabbatar bata nan. Zaman dirshan ya yi k’asa ya kuma rik’e k’uncinsa hannu bibbiyu cikin mabayyanin tashin hankali ya ce “Ni Murad me na aikata?” Zufa ce ta fara fitar masa daga jikinsa ba ta komai ta sai ta matsanancin tashin hankalin da yake ciki bai san da wane ido zai kalli maimartaba da Tauraruwa ba su amince su bashi matarsa tabbas ya aikata babban kuskuren da gyaransa sai Allah. Wace amsa zai basu a lokacin da suka bijiro da tambayoyinsa garesu? Babu! Shine amsar da ya ji zuciyarsa na amsa kuwwar gaya masa. Gwuiwoyinsa suka sare don shi da kansa ya san tabbas amsar da aka ba shin itace amsar da ta dace da tambayarsa. Ya runtse idonsa da k’arfin gaske a lokacin da idanun nasa suka cigaba da hasko masa kyakykyawar fuskarta a yayinda da ya bu’deta.
Hannunta damk’e cikin na Hajja suka ratsa har cikin sashen Tauraruwa babban sashen da ta tare a ranar. Shiru sashen sai hadimanta da suke ta kaiwa da kawowa. Ganin Hajja ce ba su yi k’ok’arin tsayar da ita ba suka bari ta shige har cikin sashen da d’akunan barcin Tauraruwa suke. A babban d’akinta suka tsaya suna nocking a hankali. Tauraruwa da ba barci take ba ta idar da nafila kenan ta basu umarnin shiga duk da bata san su waye ba amma zuciyarta ta yi mummunan bugawar da ta tabbatar koma meye ya faru ba zai zama alheri ba. Ta mik’e a hanzarce ganin Hajja rik’e da hannun Najee. Zuciyarta ta sake tsinkewa cikin kasalalliyar murya ta furta “Lafiya Hajja? Me ya faru na ganku tare a tsohon daren nan?” Hajja bata amsa ta ba har sai da ta dangana ga wata kujera a d’akin suka zauna ita da Najeen sannan ta kalli Tauraruwa ta ce “zauna y’ar nan lamarin fa babu da’din ji.” Harbawar da zuciyar Tauraruwa ta yi wannan karan har yafi wancan ta dafe k’irjinta da take jin idan bata dafe d’in ba saboda matsanancin bugun da yake komai ma zai iya faruwa. “Ya saketa ko?” Shine kalamin da ta ji kawai ya fita daga bakinta…” Hajja ta d’an ware ido cike da mamaki ta mayar mata da tata tambayar “Dama Kun yi da shi zai saketa ne?” Tauraruwa ta d’an cije leb’e da ta tabbatar da samuwar amsarta bata buk’atar wani k’arin bayani. “Ya furta da bakinsa, idan har muka sake muka sa ta tare a gidansa tabbas zai saketa a gidan aurenta! Amma me yasa zai yi sakin bayan ta bayyana masa kamanninta?” “Tun kafin yaga fuskata ya ja hannuna ya damk’a min takardar sakin…. Sai dai bayan da yaga fuskarta wa sai yaso ya janye takardar ni kuma na ruga na gudu tunda na tabbata ba don Allah yake so na ba don Allah ina rok’on alfarmarki Mahmah ki raba wannan auren….” Har abada kuwa!” Tauraruwa ta furta cikin muryar da yake bayyana b’acin ranta. Ta ja waya ta kira mai martaba sai dai bugun duniya bai d’aga wayar ba ta san tabbas yana cikin yanayi na b’acin rai, tana daina kiran wayar Murad ta dinga shigowa ba kakkautawa. Kallon wayar kawai ta ji ranta ya sake b’aci bata san sanda ta kashe wayar gaba d’aya ba tana jin ko sunan Murad bata son ji a wannan lokacin da zuciyarta take buk’atar nutsuwa da dogon nazari kafin ta san irin hukuncin da zata yanke akan maganar.
Fita ta yi daga babban d’akin nata kafin ta dawo ta ce Hajja da yakumbo su koma d’akin da ke kusa da nata. Najee zata mik’e ta kira sunanta “Dawo mu kwanta tare kin ji Najwa..” Najee ta ja k’afarta a hankali zuwa saman kujerar da ta tashi, zuciyarta take jinta wasai ko yanzu kam burinta ya cika zata wahalar da shi kamar yarda ya gallaza mata a rayuwa kuma bata jin zata sake komawa gidan sa har abada.
“Tashi ki shiga ki yi wanka, ki tabbatar kuma baki saka wannan zancen a ranki ba balle ya dameki gobe zan kira Nene zan sanar mata duk abinda muka zartar zaki ji.” Najee ta d’aga kai tana lumshe yalwatattun idanunta da suke cike da zaro zaron gashi.
Ganin Tauraruwa bata d’aga wayar ba sai hankalinsa ya sake tashi kai tsaye ya mayar da kiran kan Jaheed. Yana cikin barci ya dinga jin kiran da k’arfin gaske da sauri ya d’aga ganin me kiran yana fatan koma meye ya zama lafiya. Bai jira yace komai ba ya ce “Na cuci kai na Jaheed na saki matata a cikin rashin sanin cewa itace matar da nake muradi nake kuma burin mallaka a matsayin matar da nake so….” Jaheed runtse idonsa ya yi kawai kafin cikin raguwar murya ya furta Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna saki nawa ka mata Murad?” Runtse ido Murad ya yi hannunsa na rawa ya zubawa hannun da ya rubuta takardar sakin ido yana jin da da gatari kusa da shi ba abinda zai hana shi sare hannun da har ya rubuta sakin ba tare da ya ankarar da shi wautar da yake shirin aikatawa ba… “Na ce saki nawa ka mata Murad???” Murya na rawa ya furta “Duka………” Jaheed ya runtse idonsa kawai bai san wayar ta fa’di daga hannunsa ba……
Hope an yi sallah lafiya Ubangiji Allah yasa mun yi ibada karb’abbiya ba k’ishirwar banza muka sha ba… In sha Allah jibi zamu dawo postinga gadan gadan kamar yarda muka saba ba za kuma mu tsyaa har sai mun kammala littafin biizinillah… Allah yasa muna daga cikin y’antattun bayin da aka y’anta a cikin watan ramadan wannan somin tob’i ne na fara sakar muku don haka zaku gan shi ka’dan, alamace ta nuna ku shirya gadan gadan Kudirar Allah na nan tafe ranar lahadi Idan Allah ya kai mu.