Sashe 19
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Najma na zaune da cikinta a gaba ta hangosu tana ganin Tauraruwa gabanta ya fa’di ganin yarda kamanceceniyarsu da Jaheed ta bayyana matuk’a da gaske. Ko baa fa’da mata ta san tabbas sun ha’da jini da Jaheed don haka da sauri ta durk’usa tana gaishesu. Tauraruwa ta juyo tana kallonta suna amsawa tana fa’din “Wannan dai Umma daga gani itace surikar tamu da ta k’i mu ko?” Najma ta sunkuyar da kanta kunyar duniya na lullub’eta ta dinga ji kamar k’asa ta tsage ta shiga saboda kwarjini da k’imarsu. Umma ta d’an saki murmushi ta ce “Bata guje shi ba Yarinta ce. Tun ba yau ba kuma ta yi nadamar abinda ta aikata.” Tauraruwa ta d’an tab’e baki ta ce “Allah ya kyauta, zan so mu gaida Uwarta Ai ta gan mu taga dangin Jaheed ba shegen da take tunani ba ne.” Umma dai hak’uri take bata tana furta “Duk dai abin bai kai haka ba, a yi hak’uri a rashin sani ne..” “Ai dama a rashin sanin zata aikata haka, idan banda haka son duniya ka’dai ba zai barta ta wulak’anta Jaheed ba da ta san asalinsa da toshensa to irinsu ne masu wulak’anta d’an adam ba tare da sun san kima da darajar da Allah ya ba shi ba, duk kasawar d’an adam wala ta tawayar halitta ko talauci yana da nasa girman a wajen Ubangiji ba mamaki ma ranar lahira ko kwatankwacinsa ba zaka kai ba, amma a duniya ka dinga d’aga masa kai saboda wata baiwa da Allah ya maka wacce ta kere ta sa. Allah dai ya kyauta ya shirya duk masu hali irin na Uwarta, ga shi nan Allah ya nuna musu ishara ta hanyar sanya jinin Jaheed a cikinsu, Jikan mahaukaciya yanzu kuma ko da wani suna za’a kira shi. Jikan Sarkin Gabas ko? Sai kuma a fara dana sani ko?” Ta fa’da tana sakin murmushi wanda da alama na takaicin abin ne da yake huda zuciya da ruhinta. Su Fulani Saddik’a dai sai hak’uri suke bata ganin yarda Tauraruwar take ta kumfar baki. Da alama duk wani abu da Mahmeey ta yi shi Tauraruwa ta ji labarinsa. Najma dai durk’ushe take tana zubar da hawaye kawai ita kanta a yau ta na jin Mahmeeyn bata kyauta mata ba, don tun suna yara ita ta cusa musu tsanar Jaheed a zuciyarsu ta hanyar nuna musu Ubansu ya fi son Jaheed d’in da yake tsintattan d’a shikkenan Suka samu kafar tsanar Jaheed d’in ta wanzu a zuciyarsuqba tare da sun san dalili ba. Da sun samu Uwa ta gari kamar Umma da suma sun zama y’ay’a na gari da kowa zai yi alfahari da su. Suka wuce suka barta tana sake zubar da hawayen. Mahmeey da take tsaye a window ta ji kaf abinda ya faru hankalinta ya tashi matuk’a ainun da jin Jaheed d’in Jinin sarauta ne ta yi saurin gyara fuskarta da ta bayyana rashin nutsuwa jin sallamar su Umman a k’ofar sashenta. Cikin natsuwar fuska da fara’ar dole da ta k’ak’alo ta amsa musu sallamar tana murza key d’in parlourn ta bu’de musu k’ofar suka shigo. Tun daga ganin farko da ta yiwa Tauraruwa hankalinta ya yi bala’in tashi don bata hango sassauci a fuskar Tauraruwar ba gwara ma Nene ta saki tata fuskar ta kuma gaisheta a mutunce kamar yarda ta saba a lokutan baya. Murya na rawa ta amsa tana furta “Barka da sauka Nene ashe yau za ki dawo?” Mamaki ya kama Nene ta dai daure ta amsa mata suka samu waje suka zauna. Tauraruwa ta dinga kallon Mahmeeyn shek’ek’e kafin ta furta “Masu gida ran gida, Iyayen Jaheed ne suka zo gaida ku, d’an mahaukaciya da ya riki’de ya koma d’an Sarkin gabas!” Sunkuyar da kanta ta yi da sauri don ta san bata da cewa bata isa da Tauraruwa ba da sunansu ya gama karad’e yankin arewa. Arzikin su ya shahara irin shaharar da kowa ya san su ko a radio zaka yawaita jin sunan Sarkin gabas akan gaba wajen taimako da bada tallafi ga al’umma musamman marayu da yake jin kamar duk wata dawainiyarsu ta rayata a wuyansa ne. Jin shiru bata amsa ba suka mik’e Tauraruwa ta gama yar mata da maganganu sannan suka fice daga sashen suka barta da tarin dana sani da takaici a zuciya wannan fa shine asalin YIWA KAI (Littafin Zee kumurya na Bright pens Mikiya). Najma kuwa kuka ta saka a tsakar parlourn kukan da ya sake dugunzuma zuciyar Mahmeey ta rasa ma me zata ce mata da ya wuce zuba mata ido tana tsaki.
Isarsu sashen Umman suka zube a parlour Umma ta k’walawa Najee kira akan ta zo ta kawo musu dadduma su yi Sallah. Ta fito da d’an tsallenta tunaninta Umman ita ka’dai ce turus ta yi ganin su Nene har da Fulani Saddik’a da take ta jifanta da murmushi ta juya ta kallin Tauraruwa da itama take kallonta tana murmushin ta furta “Matso nan My Inlaw matso mu gaisa mana kika ja kika tsaya haba amaryar Murad…” wani irin waro ido Najee ta yi sai kuma ta k’ifta idon tana kallon Nene ta ce Murad kuma ko dai Ya Jaheed ina ni ina wannan masifaffen mutumin Allah ya kiyaye wallahi….
JIKAR NASHE✍🏽🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: “Matsayin matarka uwar yaranka.” Tauraruwa ta furta kanta tsaye tana sakarwa Maimartaba murmushi. Da sauri su Murad suka k’araso wajen Sarkin da su Nene da suke tsaye. Maimartaba ya saka hannu ya janyo Jaheed ya sanya shi a jikinsa yana jin soyayyar yaron tana fusga a zuciyarsa tausayin rashin taso wa da shi a rayuwarsa yana sake mamaye zuciyarsa. Tabbas zai gode wa mutanen da suka kula masa da Jaheed har zuwa yau da yake tsaye sun cancanci a sakanta musu da mafi darajar Sakantawa. Ba shi da muryar da zai bu’de ya yi godiya a garesu sai yaga kamar matsayin su ya zarce hakan. Ina da burin ganinsu yana da burin ganin Uban da ya zamewa Jaheed Uba a lokacin da ya rasa nasa Uban. Baya jin wajen nan da dandazon mutanen da suke wajen zai bari ya nuna tarin farin cikinsa yarda ya kamata don haka kawai sai ya ja hannun Jaheed d’in da na Murad suka wuce da don isa b’angarensa. Baya buk’atar sanin komai a yanzu duk da hakan mutane zasu so ya faru lokaci zai ba su lokacin da za su zo su amsa laifukan su da kan su shi kuma ya yi musu hukunci irin wanda ya dace da su.
Tauraruwa ta bi shi bayan ta kalli Fulani Saddik’a tana sakar mata murmushi ta ce “Ki biyo ni da k’awarki” ba sai ta mata fashin bak’i ba kai tsaye ta san wacce take nufi, don haka ta damk’i hannun Nene da take tsaye dukkan jikinta a sanyaye gani take abin kamar almara ko irin mafarkin da ta saba yin sa kullum.
Fulani Raheena kuwa wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske, zuciyarta ta mata nauyi kamar yarda dukka gabban jikinta suka mata nauyin, jikinta yana bata matsayin ta a zama matar Sarki yana neman ya zama tarihi. A sanyaye ta mik’e jikinta sanyi k’alau ta d’an bi mutanen da suke bin ta da kallon Allah wa dai da ido kafin ta zare jikinta zuwa b’angarenta, hatta da barorinta haushinta suke ji a idanunsu ta gano yarda suke Allah wadarai da bak’in halinta. Ta ha’diye yawu mai d’acin gaske sanda ta yi arba da kallon da su Abdul y’ay’anta na cikinta suke mata kallo ne da kai tsaye ta kasa fassara shi duk da zuciyarta na nuna mata su ma Allah wadaran suke da zamanta mahaifiyarsu. Dad’i d’aya da take ji a ranta da su suka zama halastattun y’ay’an Sarki, ashe gaggawa ta yi ta aikata waccan katab’orar nata rabon yana tafe, me yasa ta yiwa Allah katsalandan a cikin aikinsa? Hawaye ne suke don zubo mata don haka kamar wulgawar iska ta yi saurin b’acewa daga wajen, tana jin muddin bata tafi ba gaf mutanen wajen suke da fara jifanta don zuciyar wasu a dama a fusace suke musamman jin sarki bai ce komai ba game da hukuncin da zai zartar musu.