Sashe 20
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A d’akinta ta zube jikinta na zuba wata irin kakkarwa kamar mai Jin sanyi ita da kanta ta hango kalmar nan da hausawa suke cewa ta faru ta k’are! Duk k’ok’arin ta na son rufawa kanta asiri ashe Rabbi ya shirya ranar da zai banka’dashi a bainar jama’a. Hoton hannunta yake kallo hoton da ya bayyana Nene da Sarki a wani yanayi, ta da’de da tanadin hoton don tun sanda aka d’auke shi ta zare do don hoton d’aya ta masa kyakykyawan b’oye don zuwan wannan ranar, ba tare da sanin cewa Tauraruwa ta b’oye duk wasu copies na hotunan ba. Niyyar ta ta sanar da duniya fywad’e Sarki ya yiwa Nenne har ta samar da cikin yaran, ashe da aurensu komai ya wakana ba tare da sanin ta ba. Tsanar Tauraruwa ta sake bunk’asa a zuciyarta fiye da wacce take mata a baya. Ta yaga hoton bayan ta masa wani irin kallo ta zuba a cikin toilet. Fitowar ta kenan daga toilet d’in Amra ta shigo cikin d’akin fuskarta na bayyana tashin hankalin da take ciki. Wani irin kallo ta zubawa Amrahn tana jin wani haushinta. “Yaya kin cuceni kin dasa min son mutumin da kika san baki da hope akan zan same shi Wallahi Allah ya isa ban yafe miki ba.” Wani irin kallo ta yi wa Amran tana furta “Allah ya isa? Ni kikewa Allah ya isa Amra?” Ko kafin ta yi wani yunk’uri Amran ta murgu’da mata baki tana furta “Eeh d’in, ai bani ka’dai ba ma yau mutane da dama zaki karb’i Allah ya isarsu macuciya kawai.” Daga haka ya fice da sauri dama jakarta tana kafa’darta. Saroro Raheenan ta yi tana sakin ajiyar zuciya bayan fitar Amran mamaki take sosai to Amra ma kenan ta mata haka da ba abinda za’a danganta su da ita da ya wuce a ce k’anwarta ce ina ga Y’ay’an cikinta da ta janyo musu abin gori har muddin rayuwarsu. Ta runtse idonta kawai tana jin yarda zuciyarta take wani irin turiri da tarnak’in b’acin rai. Bata da abinda zata kare kanta tunda Tauraruwa ta san komai. Ba Kuma ta da bakin da zata yiwa kowa bayani a gamsu laifinta dumu dumu ya fito bata da abinda zata togace kanta daga tarin laifukanta.
____
D’aya bayan d’aya yake kallonsu yana jinjina girma da izzar mulki na sarki Allah, tabbas wannan shine abinda ake kira KUDIRAR ALLAH bai san mafari ba balle ya san ranar da ya kusanci uwarsu har cikin su ya shiga, amma da yake Allah yaso zuwansu duniya sai ya kintsawa mak’iyansa su aikata hakan, da kuma ya so su zama halastattun y’ay’a sai ya kintsawa tauraruwa zuwa wajen Baffa Liman don an d’aura aurensu. Tabbas ba abinda zai cewa Jalla da ya wuce godiya da kuma jinjina k’arfin mulki da mai yiwa Bawa a sanda ya d’ebe haso daga dukkan buk’atarsa, sai ya ba shi a lokacin da bai zata ba bai kuma tsammani ba. Shirun da ya yi yana kallonsu, ba tare da ya furta komai ba shi yasa su a damuwa da mayar da nasu hankalin kansa, musamman Nene da bata san a wani matsayi take ba matarsa ko kuma kuyangarsa ko kuma sa’daka, duk da ta san a doka irin ta sarautar gabas babu wa’dannan abubuwan. Lumshe idanunsa ya yi hawayen da ya da’de yana b’oyo suka samu damar ziraro wa ta kwarmin idanunsa, ba hawayen komai ba sai na jin da’di dana farin ciki mara misaltuwa. Ji yake duk abinda ya mallaka zai iya mallaka wa Tauraruwa shi wacce ta zama itace tsanin cikar burinsa. Ya dubi Jaheed yana sakin ajiyar zuciya kafin Ya ce “Mujaheedu ina son ganin Uban goyonka a gobe In sha Allah Zan tafi takanas har gida don jaddada godiyata gare shi.” Jaheed ya d’aga kai yana furta “Allah ya nuna mana In sha Allah.” Ya fa’da yana kallon Faruk da shima yake musu kallon farin ciki da samun cikar burinsa. A lokutan baya ba k’aramin tausayi Jaheed yake ba shi ba musamman idan aka je neman aure aka hana shi, sai ya ji duk duniya ya rasa sukuni ya kuma shiga damuwar da tafi Jaheed sai ga shi rana guda Allah ya ware ya sakantawa Mujaheed da nagartaccen Uba mai nasaba ta gaske alfaharin dukka y’ay’aye. “Faruk ka kira Baffa ka gaya masa gobe yana da bak’i, ko kuma mu bari kawai mu masa surprise.” Faruk ya d’aga kansa yana furta “Hakan ma zai fi mu basu mamaki ta hanyar ganin mu kwatsam.” Tauraruwa ce ta hararesu tana furta saboda haka ake yi, sai kawai su ganmu sama taka gwara dai a gaya musu.” Girgiza kai Jaheed ya yi yana furta “Aa Ammeey gwara dai ki bari mu musu surprise d’in.” Shiru ta yi tana jin da’din sunanta da ya kira. Maimartaba ya yarda da abinda suka ce don haka ya ce Tauraruwa ta shirya da mutanen da za’a yi tafiyar, ciki kuma ta ha’da har da yaranta Khaleefa da macen Haneefa.” Tauraruwa ta jinjina kai tana d’an jin shakkar kiran yaran nata don tun bayan bayyanarta a matsayin rayayyiya suke fushi da ita ba don komai ba sai don mayar da su marayun k’arfi da yaji da ta yi. Maimartaba ya san abinda ya tsaya mata a rai don haka ya saki murmushi yana dafata ka’dan ya ce “Dole za su yi fushi da ke Tauraruwa amma na lokaci ka’dan ne da zarar sun ga y’an uwansu sun kuma ji silar faruwar abin za su miki uziri don ina tabbatar miki a yanzu ba wanda ya fi su farin ciki da bayyanuwarki.” Nutsuwa ta samu sosai a ranta har hakan yasa ta samu k’arfin gwiwar kiransu. Haleefa ya amsa don yana zaune ne cikin iyalinsa ya ce mata Allah ya kai mu” da wata irin murya da ta bayyana tarin fushinsa. Haneefa kuwa bata amsa ba tana kallon wayar tana ruri har Tauraruwa ta gaji ta tura mata text. Ganin text d’in sai kawai ta tura mata amsa da Ok. Ta kashe wayar hawaye suna suntirin zubo mata. Haka kawai tana raye ta barsu Suna maraici duk da Maimartaba ya zame musu bango abin jingina fulani Saddik’a ma ta taka rawar gani a wajen inganta rayuwarsu don idan ta Fulani Raheena ce sai dai su dawwama cikin bak’in cikin rayuwa.
A daren ranar dai barci bai samu ga ahalin Sarkin gabas ba. Hira ce sosai ake yin ta a sashen Fulani Saddik’a, cikin nisha’di da walwala duka yaran har da Tauraruwa da take ta sake basu labarin wasu abubuwan da ta manta. Jaheed ne ya kalli Murad cikin tsokana ya ce “Wai tsaya Ammeey kada dai yaron nan gauro ne?” Tauraruwa ta saki murmushi ta ce “Gwauro mana, amma ya kusa angoncewa da amaryarsa y’ar mutanen Yola da na masa kamu tuntuni, a kwanaki bai fi kwana biyar bikin ba.” Murad ya zaro ido waje yana furta “wai wace wannan matar ne?” Tauraruwa ta girgiza kai “Idan mun dawo daga kano zan wuce da kai har Yola don ku fara zantawa da matar taka na san dai ta ko ina bata da makusa za kuma ka sota zaka yi alfahari da ita In sha Allah.” Bai sake magana ba ya dai sake k’udirce wa a ransa matuk’ar matar bata masa ba, a take wajen zai saketa ba abinda ya masa zafi.
Kashegari Kuwa Kano ta yi manyan bak’i. K’arar Parking d’in motocin yasa Baffa ya kalli matansa ya ce “Kamar fa motoci nake ji a harabar gidan nan.” Umma ta zaro ido tana mik’ewa ta ce “Bari na lek’a na gani.” Ta juyo tana fa’din “Ai kuwa bak’i ne Baffa daga gani kuma manya ne.” Da murmushi fal kan fuskarsa ya mik’e a hankali ya furta “Allah ya kawo mu ranar kenan.” Umma ta kalleshi saroro don son k’arin bayani sai dai bata samu amsa daga bakinsa ba ya yi saurin saka hular sa yana ficewa waje.
Tarba mai kyau ya musu duk da matan gidan basu san da zuwansu ba, amma Umma ta yi k’ok’ari sosai wajen ganin bata ba shi kunya ba. Ruwa da lemo kawai suka sha sannan Sarki ya dinga jaddada kalmar godiya garesu. Amsawa kawai Baffa yake yana fa’din “Yi wa kai ne.” Tauraruwa ce ta yi gyaran murya tana furta “Baffan yara ina ajiyata?”
JIKAR NASHE✍🏽🥳
A yi hak’uri jiya network ne ya hana ni posting.