Sashe 13
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wata irin hayaniya ce ta sark’e a wajen kowa kallonsa ya koma kan Raheena da hankalin ta ya tashi matuk’a ainun, bata zata a sirrinkanta har da wannan Tauraruwa ta sani ba. Ma’ana kenan duk wad’ancan yaran da take haifa suna raye ba tare da ita kanta ta san suna rayen ba. Zufa ce take karyo mata sosai, musamman da ta yi arangama da kallon da sarki yake mata, da alama shima bai san da wannan badak’alar ba sai yanzu. Cab’di jam! Idan kuwa haka ne tabbas ba zata kwana ita ka’dai a ciki ba tilas sunan duk mai hannu a ciki ya fito tunda ita dai a yanzu ta san b’aragurbin kwan da take b’oyewa ya fashe don haka dole na kowa ma ya fashe!
Shiru ya kasa samuwa a wajen wasu da dama tsananin mamaki da al’ajabin abin suke suna ganin kamar alamara. Ashe shi yasa lokacin in dai ta haihu sai a ce yaro ya mutu. Gyaran muryar da Tauraruwa ta yi ne yasa suka ja baki suka yi shiru ba don komai ba sai don suna son su san me kuma ya faru a gaba.
Bata hak’ura da bibiyar wa’danda suke mata ciki ba, kamar yarda nima ban hak’ura da bin duk wani taku nata ba da sace d’an da duk zata haifa har zuwa sanda suka ankare da abinda nake aikatawa. Suka shirya kasheni. Na ji su a lokacin da suke shirya dukkan manak’isarsu kamar yarda mai kawo min rahoto yazo ya gaya min da recording d’in da komai yana cikinsu amma basu san ba ta tare da muguntarsu ba, shi mutum ne salihi kuma masoyin Sarki na gaske ya yi Basaja a cikinsu a zuwan shi mutum ne mugu mai son lalata rayuwar sarki kamar yarda suma suke so.
Hankalinsa a tashe ya iso sashena amintacciyar baiwa ta tana gaya min shine ban yi a k’asa a gwiwaba na fito sirrintaccen parlorna da nake ganawa da bak’in sirri. Idanunsa kawai na kalla na tabbatar da ba lafiya ba kuma yana cikin matsananciyar damuwa da fargaba. “Bawa na gari!” Na kira shi da sunan da nake kiransa da shi. “Me ya faru?” Muryarsa cike da tsoro da firgici ya ce “Tauraruwar Sarki sun shirya kasheki a gobe cikin dare…” Dariya na yi sosai kafin na gyara zama na na ce “Ba wanda yake mutuwa sai kwanansa ya k’are ba su isa su kasheni ba sai Allah ya so. Me ka ji suna k’ullawa? Da wata siga za su kasheni?” Shiru ya yi kafin ya girgiza kai ya furta ban tabbatar ba tauraruwa tsoro da firgici ba su bar ni na ji k’arashen maganar ba, abu guda na sani sun ce dole su kawar da ke idan ba haka ba ke ce zaki musu Katanga daga cikar dukkan burikansu…” shiru na yi ina mamakin bak’ar zuciya irin ta jama’ar da suke Ke waye da mai Gabas. “Tashi ka je adalin bawa Allah ba zai ba su nasara ba, dukkan hukunci a wajensa yake da shi kuma na dogara.” Na fa’da zuciyata cike taf da tauhidi na kuma gasgata babu wanda zai min abinda Allah bai min ba.
Ban yi barci ba ina ta sak’a abinda zai fishsheni har zuwa sanda zuwa ta ta amince na barsu su kashe ni d’in….
Kashegari bayan fitowar Sarki Fada da safiyar Alhamis ya dubeni ganin yarda na shigo fadar kamar ba nutsuwa a tattare da ni, a gefen sa na zauna ina gaisheshi cikin kulawa ya dinga dubana kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Akwai abinda yake damun Tauraruwar Gabas gaya min maza koma menene na miki maganinsa.” Murmushi na saki kafin na furta “Tafiya zan yi ran Maimartaba ya da’de tafiyar kwana biyu shine nake tsoron ka hana ni, tafiyar tana da matuk’ar mahimmanci gare ni da kai gaba d’aya har ma da al’ummar gabas da na tabbatar suna farin ciki da samuwar farin cikin ka.” Shiru ya yi shirun da yasa k’irjina ya dinga bugu, bana son na ji kalmar “A’a daga bakinsa tun kafin ya furta kalmar a’a na san bai yi na’am da wannan tafiyar tawa ba. Ido na zuba masa kallon da na san idan na masa shi yana saka shi ko baya so ya aikata abu. Ai kuwa na raunata zuciyar tasa don a wannan gab’ar kasa dakatar da ni ya yi, ya dai d’aga min kai cikin murya mara amo ya ce “Allah ya tsare ya kiyaye hanya ina zaki amma?” Na yi shiru ina kallon mutanen da suke gefensa wad’anda na san burinsu su ji inda za ni. Na ce “Yola jihad Adamawa.” Murmushi maimartaba ya saki don ya san Yola mahaifarmu ce kuma a kowane lokaci in dai na nufin sada zumunci ina zuwa saboda dangin mahaifiya a can su ke. “A gaida mutanen Yola, sai ki zab’i bayin da zaki yi wannan tafiyar da su, amma bisa shara’din ba zaki zarce kwana biyu ba kamar yarda kika alk’awarta kin san sam bana son yi nisa da ke na kan zamo Rabin mutum idan ba kya kusa da ni.” Ina murmushi na d’aga masa kai kafin na fice daga Fadar jikina a sanyaye don ina jin wannan itace ha’du wata da maimartaba ta k’arshe sai kuma wani lokaci mai dogon zango. Mutanen Fadar na dinga bi da kallo ina nazarin fuskokinsu a take hasashe na ya bani gaskiya tabbas mugayen suna cikinsu kuma sun ji da’din tafiyar daga gani wata hanyace da zasu samu ta cikar burinsu.
Na zab’i bayin da nake so aka kuma shirya min motocin da Zan tafi da su. A ru’de amintacce na yazo ya ce da ni kada na shiga Motar da na yi nufin yin tafiya da ita don sun saka wani abu mai kama da bom da zai iya tashin motar cikin lokaci guda zata k’one da duk abinda suke cikinta. Na girgiza masa kai ina furta “Ita zan hau Amintacce ba don komai ba sai don na shirya mutuwa! Tunda har burina na samawa Maimartaba Magaji bai cika ba gwara na mutu kawai!” Shiru ya yi yana kallona cikin mamaki na san yanayin da nake ciki ne ya ba shi tsoro har hakan ta kasa b’uya akan fuskarsa… ya zube a gabana “Tauraruwa don Allah kada ki fara, ina mai martaba zai saka ransa a duk sanda ya samu labarin rasuwarki, ki tuna fa ba shi da uwa ba shi da uba ke ka’dai ce Y’AR UWARSA DA KUKE UWA DAYA UBA UBA DAYA, ina kike son ki je ki bar shi cikin tarin mak’iyan da Suka masa k’awanya?
To fa! Yau kuma Tauraruwa ta koma k’anwar Sarki? Ashe dai ba y’ay’anta ba ne to ta ina aka samar da cikin Nene? Na waye? Ko dai na Fulani Raheena ne ta dasa k’wayayan a cikin Nene? Wata sabuwa in ji Y’an caca!🤣
Idan kin san kina karanta min littafi baki biya ba ki taimaka ki biyani hakkina Wallahi wannan ba kyauta ba ne….
JIKAR NASHE✍🏽🫣🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ni kaina a firgicen nake, kwanyata at gaza aikin da ya kamata sai wani irin tsuma jikina yake, ji nake dama na farka naga mafarki nake ba zahirin gaskiya ba, zan so ya kasance mafarkin ne saboda yarda tsoro ya jijjiga zuciyata. Ganin Amintacce a gaba na ya tabbatar min da ba mafarkin nake ba, hawayen da suke zubo daga idaniyarsa suka tuna min cewa ya kamata na mik’e mu je mu ceci baiwar Allah yarinyarsa da ake niyyar cuta. Da sauri na mik’e ina kallon Amintacce na ce “Ya kamata mu je mu samu mafita ka je wajen Baffa Liman yanzu don da shi ka’dai zuciyata ta aminta ka taho min da shi nan, kafin nan ka biya ta inda suke ko da cikin shigar sirrina ka tabbatar da k’udirinsu bai kai ga cika ba tukunna don duk abinda zan aikata in dai k’udirinsu ya cika ya zama na makara, ba ni da ikon cetonta. A yanzu ma fargaba ta ban san ta yaya aka yi Suka samu Sperm d’in sarki ba Anya kuwa Amintacce dashen za su mata ko dai wani mugun aikin za su aikata mata? Kuma da sperm d’in wa za su mata amfani?” Amintacce da bai gane duk tunani na ba ya mik’e kawai yana furta “Allah ne ya barwa kansa sani Tauraruwa bari na je can d’in duk yarda ake ciki zaki sani don yanzu zan dawo zan kuma taho da Baffa Liman kamar yarda kika buk’ata.” Na d’aga masa kai ganin baya cikin nutsuwar da zai gane inda zantukana suka tafi, bana tunanin dashe zasu mata don in dai dashen za su mata zai zama da sanin Sarki kenan? Alhali kuma na tabbatar katab’orar su bata kai su bari Maimartaba ya san da wannan aika aikar ta su ba.