Sashe 18
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tun kafin su shiga gida ta lura da yarda Umma take sake hawa ta san idan ta barta zuwa zata yi ta daki Najee don haka suna shiga ta yi wuf ta fa’da d’akin ta ja hannun Najee tana furta “Fito maza Uwarki ta dawo ba mai dukar min ke alhali ke aka yi wa lefi da aka ha’da aurenki da mur’dadden mutum da ya ninka shekarunki, sannan kice zaki zo ki sauke mata wani fa’dan da ne zata ji? Daga yau ma ta yiwa d’akin naki k’aura wajena zata koma har zuwa sanda zata tare a d’akin Mijin nata. Ina goyon bayanki Najwa ki rama abinda ya miki ba sassauci ko ka’dan kin ji tunda a gaba na aka yi komai ni shaida ce.” Umma turus ta yi da wayar chargerr da zata yi dukan da ita tana kallon Nenen da take ta fa’da ba ji ba gani. “Amma hakan da kika yi da ba daidai ba ne da kan ki kike cewa ta yiwa Mijinta rashin kunya?” “Ni bance ta masa rashin kunya ba, na dai ce ta rama abinda ya mata ko ta ji sanyi a zuciyarta” Umma ta tab’e baki tana furta “Ku kuka sani idan ta yi ba daidai ba Allah yana gani ba da yawuna ba wallahi.” Ta zagayesu ta wuce kitchen bayan ta wurgawa Najee harara. Sake lafewa Najeen ta yi a bayan Nene tana furta kuma idan ya sani abu kamar dafa abinci na lafta gishiri ko?” Nene tace har da yaji ma duka ki lafta Ai shi ya janyo. Najee ta daka tsalle tana jin zuciyarta wasai ta bi Nene d’akinta suka cigaba da hira duka dai zancen Najeen ta inda zata gallazawa Murad idan an yi auren… Nene kuwa biye mata take tana dariya a zuciyarta sanin cewa har yanzu Najee bata san meye aure ba jin sa kawai take a baki don Umma jajirtacciyar mace ce mai yin iya iyawarta wajen takatsantsan da tarbiyyar yaranta, a kullum tana gode wa Allah da Jaheed ya tashi a hannun Umman ta kuma ba shi tarbiyya irin tarbiyyar da yake bawa yaranta. Shi yasa ta so auren Jaheed da Najee ba don komai ba sai don ta san zata samu nutsuwa Murad kuwa ta lura duk da yana da tarbiyya sangartacce ne da ya tashi cikin rayuwar gata yake ganin kuma duk abinda ya aikata daidai ne, shi yasa take tunanin wace irin kwamacalar zaman aure za’a yi a gidan Murad da Najee?
Ni ma dai tambayar da nake wa kaina kenan.. mu ha’du gobe. Kun san bana typing Week end ku yi hak’uri da abinda ya samu.
JIKAR NASHE✍🏽🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Gaba d’aya jama’ar parlourn suka d’ago suna mata kallon mamaki ganin yarda ta yi furucin da alamar kamar akwai sanayya a tsakaninsu. Baffa ma kallonta yake yana sakin murmushi ya ce “Lokacin amsar ajiyar taki ya yi kenan?” Ta d’aga kai tana sakin dariya sosai. “Na gode sosai da amanar da ka rik’e min har zuwa yanzu, ajiyata kuma tabbas lokacin amsarta ya yi kamar yarda muka k’ulla al’kawari da kai, na gani na yaba kuma tabbas za’a dace anan gaba.” Baffa ya d’aga kai yana sakin murmushi a hankali.
Wayar Murad da ta yi k’ara ita tasa ya mik’e ya fice daga parlourn don amsa wayar. Hakan yasa Tauraruwa gyara zamanta don ta ji da’din barin Murad wajen dama sam bata son ya ji zancen.
Maimartaba kuwa kasa barin maganar ya yi a cikinsa yana duban Tauraruwa ya ce “To dama kun san juna kenan?” Tauraruwa ta d’aga kai cike da tabbatarwa ta furta “Shekaru biyar baya na bayyana kaina gareshi, na kuma sanar da shi dukkan abinda na sanar da ku, ya so tun a lokacin ya turje da son lallai sai an bayyana hakan ga Jaheed saboda halin da yake ciki na damuwa da rashin iyayensa, ni na togace shi na kuma nemi alfarma a gareshi akan ya bari har zuwa sanda zan bayyana hakan ga al’ummar gabas a yanzu kuma lokaci ya yi. Sanda na ji labarin za’a yi wa Murad aure na tashi hankalina hakan yasa na zo wajensa da niyyar in dai yana da y’a ya taimaka ya aurawa Murad kamar yarda ya aurawa Jaheed d’aya daga cikin y’ay’ansa. Shiru ya yi a lokacin ya nuna min yarinyar da zai iya cewa kai tsaye ya amince Murad ya aureta ba kowa ba ce sai y’ar marik’iyar Jaheed sai dai kuma bayan rabuwar auren Jaheed da Najma sai yayi nufin yi masa musaya da Najwa to sab’anin da aka samu sai ya zama matar Jaheed d’in tana da ciki. Hakan yasa tun a lokacin nace masa ina nemawa Murad auren y’arsa. Bai so ba naga Kuma hakan a idanunsa na tambayeshi dalili ya nuna min yana tsoron ya ha’da Najee da yaron da ba shi ya furta yana son ta ba ba don komai sai dan yarinya ce k’arama ya buk’aci ya ba shi Nasma ni na k’i yarda na ce Najee ita ta dace da Murad duk k’ank’antar ta shekaru sha biyar tsaf zata iya aure ba miskila. Amma don Allah ina son wannan ya zama sirri tsakanina da ku bana son Murad ya san zancen nan har zuwa ranar da za’a d’aura auren ta tare a gidansa ba don komai ba sai don ina tsoron ya ce ta masa k’ank’anta ni kuwa a d’abiu irin na Umma tabbas zan so mu ha’da zuri’a da ita ba don komai ba sai don mu sakanta mata da d’inbin alherinta garemu, bana son kowa ya ji koda a cikin gidan nan kuwa ina nufin y’ay’an waccan shiyyar.” Shiru kowa ya yi kuma duka zuk’atansu sun amince da maganar musamman Nene da take ganin hakan shine mafi dacewa Murad da Najee su yi aure ranar zata fi kowa farin ciki. Umma kuwa ita kadaran kadahan ne farin cikin nata, a wani gefe can na zuciyarta kuma tana jin taraddadi da tsoron auren Najee da Murad Najee a gidan sarauta bata san tab’argazar da zata shuka ba ba don komai ba sai don ta san Najee da tab’ara irin ta y’an auta ba zata ragawa duk wanda ya shiga shirginta ba, banda haka bata da wani aibu ta iya girki ta iya komai kwalliyace ma bata fiye damunta ba sau tari ta fi son zamanta da fuskarta a haka ba tare da ta goga ko kwalli ba sai kuma hakan ya zame mata jiki ko kwalliyar ta yi bata fiye kyau ba, jambaki ne kawai yake mata kyau a d’an cute lips d’inta masu lob’awa idan tana magana, abu mafi kyau a fuskar Najee kenan tattausun lab’b’a da dara daran ido masu yalwar haske bak’in kuma si’dik. Gazar gazar gashin gira da na ido da gargasa a gefen fusktara shi ya k’arawa kyawunta kyau. Ta dai saki ajiyar zuciya kawai tana fatan hakan ya zama alheri ga Najee ga ma duka ahalin b’angare biyun.
Haka aka cigaba da tattaunawa su ka ce dukkan abinda aka ajiye musu sannan aka tsayar da ranar bikin kwanaki biyar kacal, inda komai za’a sha shagalin bikin da baa tab’a kwatankwacinsa a masarautar gabas ba. Kwana biyar za’a yi ana bikin da zai zagaye duka fa’din k’asar Nigeria. A take a wajen kuma Maimartaba ya bada Sadaki ba tare da Murad ya san sadakin menene ba.
Matan cikin gida suka shiga, don su yi Sallah su kuma sake gaisawa da Umma.