Sashe 25
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba barcin take ba kamar yarda ya tsammata a zaune take fuskarta ko ka’dan ba annuri. Ya yi sallama yana kallon yarda duk ta rame da alama damuwar da ta sawa zuciyarta ta fara tab’a lafiyar ta. A zafafe ta d’ago tana kallonsa dama shi take jira don ta san dole yana shigowa a irin wannan lokacin koda kece da girki kuwa sai ya shiga ya duba lafiyar yaransa. “Baki cire banzar damuwar da kika sakawa zuciyarki ba ko? Da alama kin shirya fara shan maganin hawan jini ne.” Kukan da take ta yi tun cikin dare shi ta sake saki wanda yake bayyana k’unar da zuciyarta take ciki. “Me yasa ka ba zaka bi abinda na ce maka ba, laifine mun yi maka amma Ai mun baka hak’uri ka bawa yaron nan hak’uri ya koma da matarsa amma ka k’i, fisabilillah ina zaka saka hakkin yarinyar nan da take cikin damuwa kullum duk ta bi ta lallace bata da nutsuwa ko ka’dan ga tsohon ciki a gabanta.” Tsaki Baffa ya ja yana furya “Yanzu da kika san asalinsa kika san ko wanene Ubansa mai ku’din gaske irin wanda kike so shine zaki d’aga hankalinki sai ta koma? To ba dani ba ni akwai kunya da kawaici a tsarina ba zan iya duban idonsa na tursasashi ya mayar da ita ba bayan rashin mutuncin da kuma masa, har abada shi yasa komai kasawar bawa ake son ka kyautata mu’amalaka da shi saboda watan wata rana kamar dai irin wannan baka san darajar da Allah ya yiwa bawa ba anan duniya ko a lahira sabida kawai kuna da fifiko ta halitta ko ta ku’di sai ka d’au fankama da girman kai ka d’orawa kanka Ina kika bar fir’auna da k’aruna? Idan arziki ne da girman kai duk duniya ba za’a sake kamarsu ba yau ina suke sun gushe kuma arzikin nasu da girman kan ba inda ya kai su. Don haka ni dai da bakina ba Zan ba shi hak’uri ba balle ya yi tunanin tursasashi na yi har ya yi min alfarma na cutar da zuciyarsa, ki nemo shi da kan ki ki bashi hak’uri ku je kuma ku bawa Uwarsa hak’uri idan ta yarda falillahil hamdu idan kuwa ba su yarda ba kada ki sake jefa ni a cikin maganarku.” Daga haka ya saka kai ya fice daga d’akin yana jin kukanta yana sake yawaita duk da zuciyarsa ta yi rauni ya fara tausaya mata amma ba zai bari tausayinta ya yi tasirin da zai kasa yiwa Jaheed adalci ba. Ya samu Murad duk ya gaji da jiransa burinsa kawai su shiga d’aya b’angaren ya ga sanyin idaniyarsa. Don haka d’akin yaran lek’awa kawai ya yi suka gaishehi ya amsa a tsaye yana kallon Najma da fa’din “Ba dai matsala ko?” Najma ta d’aga kai tana lumshe idonta da ya mata nauyi sabida rashin barci. “Allah ya muku albarka a kula da cin abinci sabida bawan Allah da kike tare da shi.” Bai jira ta cewarta ba ya yi saurin fita daga d’akin har ga Allah baya son ganin Najma a cikin halin da take ciki dukkan gazawatta da damuwarta sun bayyana akan fuskarta b’aro b’aro.
“Mu je Murad ka yi hak’uri na barka da jira.” Murad ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai ha’de da fa’din Bakomai Baffa.” Gaba d’aya halayen dattijon sun shiga ransa har yana jin da zarar ya mallaki iyali shima irin rayuwar da zai yi a gidansa kenan, ba zai zamo daga cikin maza masu girman kai ba zai zama mai sauk’in hali ga iyalinsa musamman idan ya samu wacce yake so.
Tun daga harabar sashen Umma suka dinga jin wani irin masifaffen k’amshin turaren wutan da ake yi. Murad har d’an lumshe idonsa ya yi sanda suka bu’de k’ofar tattausan k’amshin da ya caku’de da na room freshner da na sanyin a.c ya dakar masa fuskar sa. Har ga Allah yana son k’amshi, hakan a jininsa yake kamar ma ya zama addicted da shi. A tsaye take daga ita sai wata y’ar rigar barci da ka’dan ta wuce gwiwa mara hannu gashin kanta a barbaje a bayanta aikinta take fisabilillah tana bin wak’ar da ta saka a wayarta. Ba abinda ya dameta duk da Umma ba yarda bata yi ba ta suturce jikinta ganin Umman ta shige kitchen yasa ta cire dogon Hijabin da ya bi ya addabeta ta saba zama haka a gidan sanin cewa ba mai shigo musu sai Baffa ko yaran gidan maza duk suna boarding school. Idanun Murad ne suka masa mugun gani da sauri ya juya baya jin Baffa ya ce “Ke me ye haka sau nawa zan hanaki zama a haka? Wai ke sam ba kya girma ne, sannan kin saka wak’a da sassafe alhali ba d’abiarki ba ce? Wuce ki suturce jikin ki.” Da azama ta ja hijab d’inta ta saka tana fa’din “Ka yi hak’uri Baffa na zafi ne ya yi yawa.” Ta fa’da tana kallon sashen da Murad yake ganin yarda ya juya baya. Ta d’an saki guntun tsaki “Maye da sassafen nan har ya wani shigowa mutane gida. Sannan ta durk’usa tana gaishe da Baffa sai da ta bari ya amsa ta Mik’e ta bi hanyar kitchen a zafafe Baffa ya ce “Ni ka’dai kika gani anan? Ko wani salon rashin tarbiyya zaki tsiro da shi na rashin gaisar da wanda ya girmeka?” Kamar ta tsunduma ihu haka ta juyo tana kallon Murad idanunsu suka fa’da cikin na juna, wani irin fisga zuciayrsa ta yi bai san sanda ya lumshe ido ba yana jin yarda muryarta take karad’e kunnensa duk da ba sosai muryar ta fita ta hanyar d’agawa leb’enta ya fuskanci me ta ce “Ina kwana?” Da k’yar ya saita kansa wajen fa’din “Lafiya lau.” Yana k’arashewa da My heart cikin zuciyarsa banda Baffa yana wajen baya jin akwai abinda zai togaceshi wajen janyota ya rungumeta tsam ya bata kyakykyawar sumbata a cutest lips d’inta. Bata sake kallonsa ba ta juya tana ba shi hararar gefen ido. Kitchen ta koma bayan ta kashe burner d’in turaren wutar da ta kunna. Sai ga Baffa ya biyo bayanta a kitchen d’in ya tsaya kafin ya saka yatsa ya murd’e kunnenta “Najwa ba kya girma ko? Mijin da zaki aura kike harara ko kin zata ban gan ki ba ne?” Da sauri ta furta “Am sorry Baffa, ni wallahi bana son sa da na fi son Yaya Jaheed.” “Shi kuwa zaki aura nan da kwana uku Jaheed yanzu ya miki nisa tunda ga Najma da ciki, ana barin halas ko don kunya.” Umma ta fa’da tana zabga mata harara. Baffa dariya ya d’an yi yana fa’din “Ki bata break fast ta kawo mana sitroom yanzu zamu zauna mu karya da Murad da Babi.” Umma ta amsa masa shi kuma ya saka kai ya fita daga kitchen d’in. “Mu je sitroom Murad naga iyayen naka ma basu tashi ba mu je wajen Babi kafin a kawo mana breakfast.” Murad ya mik’e ya bi bayansa yana waiwayen yarda zai sake ganinta.
Suna fita Umma ta watsa mata harara “Shashasha na sake jin kalmar Jaheed kike so a bakinki kiga yarda zan miki a gidan nan. Kuma ki wuce ki je ki yi wanka yanzun nan kizo ki kai musu breakfast.” Ta d’an turo bakinta tana ficewa daga kitchen d’in.
Wankan ta yi sosai don duk abinta tana da tsafta sosai. Ta saka wani pink lace da ya yi daidai da surarta straight gown ce ta d’an kamata ka’dan ta fitar da tudun hips d’inta, don akwai baiwar hips tun tana yarinya ma kenan. Bata saka d’ankwali ba don yana daga cikin abinda yake takurata. Ta yane kanta da very light veil, sannan ta fice bayan ta goga wet lip a cute lips d’inta.
Basket biyu ne da suke d’auke da manyan flask a cikinsu, da k’yar take tafiyar da su kamar su yar da ita. Su Babi na cikin sitroom d’in shi kuwa ya kasa ya tsare a balcony kamar ya san ita zata kawo abincin. Tun daga nesa ya hangota yarda kwanukan suke rinjayarta sai yasa tana tafiya tana jin kamar zata kifa. Murmushi ya saki ya mik’e ya d’an b’uya a bayan wani lungu. Sai da ta k’araso wajen ya fito ya sha gabanta yana bin ta da wani irin rikitaccen kallon da ya sata kusan sakin baskets d’in. Idanunsa wani irin kaifi su ka mata. Da wata irin murya da bai san yana da ita ba ya matsa daf da ita cikin kunnenta ya furta mata “I love you….” Yana sakar mata hucin numfashi a cikin kunnenta wani irin harbawa zuciyarta ta yi kamar ta saki fitsari a wando. Ya janye jikinsa daga kusa da ita yana kallonta k’asa k’asa ta d’aga k’afarta zata wuce sai kawai gani ta yi kamar an jata zata kifa k’asa bai san sanda ya tare ta da hannunsa ta fa’da k’irjinsa ba wani irin shock ya d’ebesu gaba d’aya, Najee ta runtse idonta a hankali ta furta “Are you out of your senses? Ka san yarda muke da matar da zaka aura kake furta min kalmar love?” Madadin ya ji kururuwar zancensa ji yake kawai zuciyarsa na bashi umarnin ya yi kissing d’in lab’b’anta da suka fi tsone masa ido kafin ta yi aune ta ji…..