Sashe 31
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ku yi hak’uri mutuwa aka mana sai yanzu da na dawo na samu damar typing d’in saboda bana son na b’ata muku rai. Sakamakon Aljanna gareku In sha Allah. A kuma sanya iyayenmu a addu’a pls 🙏😭
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Jikinsa ne ya fara rawa bai San sanda ya tura k’ofar d’akin ya shiga Kansa tsaye ba, bai damu da irin kallon da suke masa ba, samun kansa ya yi kawai da durk’ushewa a gabansu idanunsa cikin na Najwa da take zaune tana danna wayarta bata ko d’ago ta kalleshi ba. Tauraruwa idanu ta zuba masa tana hango yarda ya nuna galabaitar da zuciyarsa take ciki, koma me ya faru ta tabbata a yanzu yanayin da zuciyarsa take ciki abu ne mai girman gaske ba mamaki ma bata bugu yarda ake so. “Ku yi hak’uri Nene kada ku raba ni da ita ba saki uku na mata ba ina da ikon na mayar da ma….” Kallon da Nene ta masa ne ya saka shi jan bakinsa ya tsuke jiki da zuciyarsa ya ji suna kakkarwa ba tare da ya shirya hakan ba. Kallo ne mai nuni da abubuwa da dama, kallo ne da yake bayyana takaicinta da jin haushinta game da k’uncin da zuciyarta take ciki. Ya sani ya raunata zuciyarta ya kuma kassara wani sashe na farin cikinta zuwa bak’in ciki mara misaltuwa duk da bata fito ta gaya masa ba ya san gefe guda na zuciyarta yana takaicin zamowarsa jininta. Da k’yar ta ha’diye kakkauran yawun da ya tsaya mata a mak’oshi ta lumshe idonta kawai duk da k’ok’arin da take na yak’i da k’wallar idanunta hakan bai hanasu zuba sharrrr akan k’uncinta ba. Hakan yasa zuk’atan duka d’aki suka yi sanyi tausayinta ya shiga zuciyarsu musamman Najee da take jin kamar nata idanun suma suna daf da zubar da hawaye. A rayuwarta tana son Nene bata kuma k’aunar abu komai k’ank’antarsa ya b’ata mata rai. Sai ta sake jin haushin Murad ya sake rub’anya a zuciyarta ta zuba masa ido tana hak’ilo da kawar da tata k’wallar don sam bata son yaga gazawarta balle yace ta damu da rabuwar da suka yi. “Ba zata komawa aurenka ba Murad! Ko da kai ne ya rage Autan maza a duniya…..” Nenen ta fa’da idanunta a runtse cikin wata irin Amon murya mai kaurin gaske. K’iris zuciyar Murad ta rage ta buga… bai dawo daga waccar razanar ba ta sake jefa shi a wata “koda wasa kada ka sake kace ka mayar da ita idan ba haka ba ba zan tab’a yafe maka ba har abada!” Wani irin shiru ne ya ratsa d’akin shirun da yake bayyana tashin hankalin da girgizar da zuciyoyin Tauraruwa da Murad suke ciki. Jikinsa a salub’e ya mik’e yana jin jiri na shirin kada shi ya dafa bango ya fice daga d’akin ya zama dole ya bar k’asar nan barin da yake tunanin na har abada…. Don ba zai jure ganin ranar da za’a ce Najwa zata auri wani ba shi ba..
Yana fita Tauraruwa ta dubi Nene cikin b’acin rai ta ce “Hukuncin da kika yanke sai nake ganin ya yi girma, kada ki yi abinda zaki zo ki rasa ranki kin san dai k’addarar Ubangiji girma gareta Kuma wanda ya hana aure idan Allah ya nufa sai anyi sai kiga anzo an yi babu shi. Laifinsa bai kai a masa irin wannan hukuncin ba, mune da laifi mu da muka k’i bayyana masa gaskiya muna tunanin wasa yake a kalaminsa sai ga shi yazo ya zartar da gaske, don haka ki janye kalamanki a mayar masa da matarsa tunda ya gane kuskurensa….” Wani kallo Nene ta mata sai da ya sata yin shiru bata shirya ba.. “Ba zata koma ba hasalima da ni da ita barin garin za mu yi kuma ina rok’onki kada ki sanar da kowa mutuwar aurennan bayan ku da kuka sani bana son maganar ta je gun Baffanta har sai na samar mata nagartaccen Miji da zai yi alfahari da shi In sha Allah. Idan kuma kin k’i ina tabbatar miki nima zan barranta kai na da auren Mai martaba!” Shiru Tauraruwa ta yi don ta lura a wannan k’adamin zuciyar Nene ba zata ji lallashi ba ta yi k’ok’on b’acin rai… “Ba zan fa’da ba, amma nima ki min alk’awarin ba zaki ko ina ba daga masarautar nan zaki zo ki tare a gidanki idan yaso Najwa ta zauna a wajenki har zuwa sanda zaki samar mata mijin.” Nene bata kawo komai a ranta ba ta ce “shikkenan zan iya yarda da hakan, bisa alk’awarin koda wasa kada Murad yazo sashena har sai bayan Najwa ta gama idda na samar mata Miji.” D’aga kai Tauraruwa ta yi alamar amsawa daga nan Nene ta mik’e tana d’aukan jakanta “Zan tafi da ita zan ajiyeta gidan k’awata don ba zan zauna anan ba har sai Baffa ya kawo ni da kansa, ba kuma zan bar Najwa anan ba don ban yarda da ke ba..” Ido Tauraruwa ta zuba mata fuskarta na nuna rashin jin da’din samun cikar burinta me yasa duk ta inda ta biyo sai Nene ta toshe mata hanya kamar mai ganin zuciyar mutane. “Tashi Najee mu tafi.” Nene ta fa’da tana kallon Najeen. Da sauri Najee ta mik’e ta zura doguwar rigar abayarta ta bi bayan Nene bayan ta ja k’aramar trollynta mai d’auke da kayanta kala biyar a ciki wanda Tauraruwa da kanta yau ta je sashenta ta d’auko mata. Tauraruwa na kallonsu suka fice ta bi bayansu da sauri don saka Drivernta ya kai su.
Ta window Murad ya hango fitowarsu ya runtse idanunsa yana jin kamar ya rabu da wani sashe na jikinsa ne, da bai aikata hakan ba ya tabbatar da yanzu suna nan manne da juna suna shan amarcinsu.
Tauraruwa sakin ajiyar zuciya ta yi kafin ta juya ta nufi sashen mai martaba don sanar da shi halin da ake ciki.
Shiru sashen sai Fulani Saddik’a da take ta shirya dinning dama fadawa sun saba a irin wannan lokacin ba sa zama kusa da Mai martaba suna barinsa ya sake ne da iyalinsa ya samu kulawa daga garesu. Ta bi Fulanin da kallo tana sakin murmushi kafin su gaisa ta ce mata “Sai kuma kika ji shirmen da d’anki ya yi..” Saddik’a ta saki ajiyar zuciya takaicin da yake cin ranta ne yasa ko maganar bata son a mata. “Allah ya kyauta ni ban san ma me zance ba tun d’azu nake son kiransa sai dai zuciyata tana gaya min na bari ta huce tukun don zan iya dukansa.” Fulanin ta fa’da kanta tsaye cikin muryar da ke bayyana gaskiyar abidna ke ranta kenan. “Dukan ne ya kama ce shi daga gareki don zai fi jin zafin dukan daga wajenki fiye da kowa Amma idan kin tashi dukan ki kirani na tayaki. Yanzu Nene tazo ta ‘d’auke y’arta kuma taja rantsuwa akan cewa har abada ba shi ba auren y’arta koda shine autan maza…” Saddik’a ta waro ido ta ce “Ya aka yi kika k’yaleta ta furta hakan cikin fushi Hasbunallah yanzu menene abin yi?” Tauraruwa tace “Hak’uri mana ba shi ya janyowa kansa ba sai yaje ya nemo mata da kansa ya aura zab’in ransa ba namu ba…” gyaran muryar Maimartaba ne ya saka su yin shiru daga zancen da suke. Ya shigo cikin rigar jallabiya mara nauyi sai zabga k’amshin turarensa na Usuli yake. Fuskarsa ba walwala ko ka’dan sai dai a washe take sosai ya zauna a saman babban kilishin da aka shimfi’da masa don cin abinci. Ba da’din bakina nake ji ba Fulani, kamar yarda zuciyata bata min da’di ko ka’dan ba ni tataccen ruwan inibi kawai na sha, ki kira min d’anki kuma yanzun nan…” Da k’yar Fulani ta nutsu saboda bugun da zuciyarta take bata san wani hukunci kuma Mai martaba zai yiwa Murad ba, tana fata koma menene ya zama mai sauk’i kada abin ya masa yawa. Ruwan inibin ta zuba masa a babban tumbler mai masifar kyau ta mik’a mas a cike da girmamawa sannan ta mik’e don gaywa hadiman su kira Murad sak’o daga mai martaba. Tauraruwa kanta a lokacin tsoron idanun sarki suke saboda yarda suka birkice lokaci guda da alama bai samu isashshshen barci ba.. “A masa afuwa ranka ya da’de…” wani kallo ya zuba mata yana ajiye cup d’in inibin. Tauraruwa ta yi k’asa da kanta tana jin tashin hankali yana ziyartarta zata iya cewa bata tab’a ganin maimartaba a kwatankwacin hali irin wannan ba… shiru suka zauna har zuwa sanda Fulani Saddik’a ta shigo da Murad suka k’arasa gaban Mai martaba Murad yana jin kamar ya shige cikin k’asa kada MaiMartaba ya samu damar yi masa zancen can. Idanu Mai martaban ya zuba masa ba tsawon lokaci kafin ya yi k’wafa ya ce “Mun baka kwana uku kacal ka tsayar da matar aure…. Abu na gaba na cire ka daga matsayin Yareema Magaji na na bawa Jaheed bana son a wannan karan ka sab’a umarni na ko ka’dan kwana uku kacal na baka kazo min da matar da kake so tunda mu ba mu iya zab’i ba…” Murad ya d’aga leb’e zai yi magana Mai martaba ya d’aga masa hannu “Bana son jin komai daga bakinka Kai ne babba a haka kake son k’annenka su yi koyi da kai, ba zan maka baki ba amma har abada ba zaka samu Matar da ta kai matar da ka saki ba…• Wani irin sarawa kan Murad ya yi ya mik’e jiki a sanyaye don bai hango sassauci a idanun mai martaba ba. Fulani Saddik’a ta mik’e zata bi shi mai martaba ya zuba mata wani kallon da ya sata zama ba shiri. Tana jin kamar ta zunduma ihu gani take hukuncin ya yi tsauri da yawa tasirin sa kuma zai iya kassara zuciyar Murad. “Hukuncin da zan masa na k’arshe kenan, idan kuma wani yasa ya bijirewa umarnina kai tsaye ya barranta kansa da ni.” Shiru suka yi kowa zuciayrsa da abinda yake sak’awa…..
__________