Sashe 4
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
JIKAR NASHE.✍🏽🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Jikin Nene ne ya fara rawa ganin yarda Murad ya gigije hannunsa na rawa ya damk’i nata hannun, cikin rashin nutsuwa ya fara furta gaya min mana, gaya min ta yarda nazo duniya ina son sani please!” Nene damk’e nata hannun ta yi cikin nasa zuciyarsu na bugawa lokaci guda kamar yau suka fara ganin juna haka suka zubawa junansu ido, kafin Murad ya kai mata wata irin runguma yana sakin numfashi a hankali wata irin nutsuwa da sanyi na shiga zuciyarsa daga jin yarda jikinsa yake amsar sak’on bugun zuciyarta ya tabbata da gaske itace mahaifiyarsa, yarda ya lura tun fara ganin matar ya ji duk duniya ba abu mafi soyuwa a wajensa kamar ita, baya gajiya da kallonta kamar yarda kunnuwansa basa gajiya wajen saurarar tausasan lafazinta. Shiru Nene ta yi itama wani farin ciki na ratsa zuciya da gangar jikinta sai yau ta tabbatar da mafarki yana iya zama gaske ashe, ta sha yin irin wannan mafarkin tana ganin Murad kwance a jikinta yana kuka da farin cikin ganinta. Fulani Saddik’a har ma da Najee hawaye suke sharewa ba na komai ba sai na zallar tausayinsu da gaske duk wanda ya raba uwa da mahaifiya akwai cutarwa mai girman gaske zai kuma gamu da Allah. Tunda take ba ta tab’a ganin raunin Murad ba kamar yarda ta gani a idanunsa yanzun. Tsawon lokaci yana kukan da ba wanda ya hana shi ya da’de a rayuwarsa zuciyarsa cikin k’unci da rashin walwala sai dai yana b’oye hakan gudun b’acin ran Mamma da take ba shi duk wata kulawa da d’a yake buk’ata ga mahaifiyarsa, amma yau ya gaza ya kasa danne abinda yake ransa har sai da rauninsa ya bayyana akan idanunsa da fuskarsa bai ji kunyar Mamma ba ya rungume Uwar da ya da’de yana mafarkin jin d’umin jikinta cikin nasa jikin. Tsawon lokaci yana haka kafin ya zame jikinsa yana mayar da ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa a hankali yana furta “Ina son sanin yarda nazo duniya, ina kuma jin tsoron a furta ni shege ne tunda Maimartaba ya tabbatar bai aureki ba, ta yaya kika samu cikin mai martaba a jikin ki ba tare da aure ba?” Ya fa’da idanunsa akan Najee data zuba masa ido ya zabga mata harara kafin ya d’auke kai yana furta “Bar nan wajen kafin na saka k’afa na doke shegen dogon bakin ki.” Bakin ta sake turowa gaba ta mik’e ta fice daga d’akin. Murad ya bita da kallo yana tsaki k’asa k’asa baya fatan Najee ta zama k’anwarsa ta jini. Mamma kafa masa ido ta yi tana hango irin yarda fuskarsa ta washe daga wancan duhun da take gani a lokutan baya, wannan Murad d’in wani ne daban mai matsananciyar fara’a da walwala, fuskarsa ta nuna d’okin son sanin asalinsa, itama tana da burin sanin hakan don haka bata togaceshi daga tambayar ba suka taru suka zubawa Nene ido suna jiran k’arin bayani, duk da ta san Nenen ba ta da ta cewa kamar yarda ta sanar da ita bata san komai ba, ta dai wayi gari taga ciki a jikinta aka kuma tabbatar mata da cikin d’an sarki ne na halak a jikinta. Murya cikin rashin karsashi Nene ta ce “Ban sani ba Murad, ban san duk yarda abubuwan nan suka kasance ba, abu guda na sani ni na yi nak’udarka na haifeka da kai na Wallahi har a yanzu ban mance ra’dad’in nak’udarka ba.” Murad shiru ya yi yana murza hab’arsa yana nazarin maganar Nene zuciyarsa na sake gasgata masa abinda yake tunani DASHEN CIKIN aka mata amma wanene kuma menene dalili? Idan har dashe ne zai zama daga matan sarki tunda ance shi d’in DAN HALAK NE BA SHEGE BA. Wacece waccan matar? Da sauri ya mik’e ya fara nufar tafiya burinsa ya je wajen mai martaba ya sanar da shi wacece tauraruwa?
____________