← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 43

Sashe 23

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigowar Jaheed yasa ya bu’de birkitattun idanunsa da suka masa nauyi tsabar tunanin da ya masa nauyi a zuciya. Jaheed ba tare da ya nuna ya san komai ba ya ce “Mr. Man am going home now na bar Khaireey ita ka’dai a gida.” Da sauri Murad ya ja hannunsa ya finciko shi bakin gadon ya zauna don dole shima ya mik’e a kasalance yana duban Jaheed d’in ya ce “Don Allah ka taimakeni Jaheed ka bani numberr k’anwar Umman can da na gani a parlour sannan don Allah ka saka su su janye batun aura min mummunar can wallahi zan baka duk abinda kake so har sarautar Gabas zan bar maka ita Please Jaheed am in love…..” Ya fa’da yana lumshe idon sa wasu tarin hawaye da bai san na meye ba suna zubo masa, tunda yake bai tab’a tsintar kansa a masifaffiyar soyayya irin wannan ba da yake jin hucin numfashinta kamar zai k’iba masa zuciya. “Me yasa zaka amshi numberrta alhali akwai matar da aka maka baiko da ita, Auren Najwa alheri ne fa a gareka….” “Uban alherin? Kai me yasa baka yi halaccin ka aureta ba ina ce kai ma Nene Uwarka ce kai ka san ma wahalar da yarinyar ta yi da ita don haka kai yafi cancanta ka aureta ka ji min banza…” Jaheed ya waro ido ya ce “Ni ne banza? Ai shikkenan sai ka nemi me samo maka numberr don ba zan bayar ba kuma duk gidan nan ni nake da numberr ta bata bawa kowa numberr ta saboda masifaffen ajin da take da shi gata dai yarinya k’arama sai ajin tsiya…” Da sauri ya rik’e hannunsa ya ce “Na shaida wallahi Jaheed Na shaida kuma don Allah ka yi hak’urin zagin da na maka wallahi sharrin shaid’an ne.” Jaheed ya saki murmushi ganin yarda ya yi rauni ya ce “Babu amfanin baka numberrta Murad ka tuna k’anwar Umma ce ta ya zaka k’i y’arta kace k’anwarta kake so Ina ga hakan kamar Impossible ne…..” “In ji Uban wa? Aurenta na yi?” “In ji Ubana Murad bari dai na mik’e kafin ta kai ga ka kai min duka…” Murad ya saki tsaki yana furta “Ka yi ta tafiya amma ina tabbatar muku kuka sake kuka aura min witch d’in nan sai na tattara na bar garin nan mugu kawai.” Jaheed ya k’unshe bakinsa saboda yarda dariya yake neman sub’uce masa ya fice daga d’akin yana fa’din “Asuba ta gari Angon Najee….” Wani ashar Murad ya mulmula masa yana fa’din “Na ga Uban da zai sa ni dole na aureta….

JIKAR NASHE✍🏽🥳

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ganin wanda yake tsaye ya sata saurin juyowa k’irjinta na bugu mai tsanani, Allah yasa bai ganta ba don gaba ‘d’aya hankalinsa ba a kanta yake ba, yana kan Inno da yake shirin zolaya, duk da ya ji muryarta bai mai da hankali ya san ko wacece ba, sanda ya juyo kuma da niyyar ganin wacece ta juya fuskarta ta shige kitchen gaba d’aya. Ya d’an tab’e bakinsa yana zama daf da Inno da take kallonsa cikin mamaki Nene ta ce “Murad nan ma biyo mu ka yi.” Ya d’aga murya a nutse ya ce “Ke ma ba kin biyo Mamanki ba, shi yasa na biyoki I want to have your caring.” Da sauri ta janye idonta daga kansa kunyar Tauraruwa da take zaune yasa ta kasa furta komai. Tauraruwa kuwa murmushi ta saki ta ce “Kana da gaskiya Murad ya kamata kaima ta baka dukkan kulawa da bata baka ba a baya, duk da Alhamdulillah Uwar goyonka ta maka rik’on da ya dace, amma ita kulawar mahaifiya itace abu na musamman ga yaro don haka ban ga laifinka ba, ke kuma Nene ki cire kunyar Fulani ki bawa d’anki kulawa.” Da sauri ta girgiza kai “Ni ba d’ana ba ne, na bar muku ke da Fulani Saddik’a kamar yarda Jaheed yake d’an Ummansa ni tawa y’ar Najwa ce.” Tauraruwa ta ji dad’in furucin Nenen har haka ya bayyana akan fuskarta. Shi kuwa Murad cikin fushi ya ce “Wacece kuma Najwa?” Murmushi Nene ta yi tace “Itace y’ata mafi soyuwa a zuciyata fiye da ku, don haka duk wanda yake son albarka ta ya zama dole yaso Najee ya bata dukkan farin ciki a rayuwa.” Murad kansa ya sake d’aurewa yana kallon Tauraruwa da son k’arin bayani. Gane alamun hakan yasa Tauraruwa furta “Najwa yarinyar gidan nan ce, Uwa d’aya ce ta rik’esu da Jaheed sai dai dukkan Kulawar Najee yana wajen Nene ne, tana sonta fiye da k’ima.” Ya d’an tab’e baki ya ce “Tana ina?” Tauraruwa da sauri ta basar da zancen ta hanyar kallon Inno tana furta “Wannan jikan naki akwai tab’ara ban san yarda zai yi ba ranar da zai ga matarsa a d’aki, Najee itace matar da muka zab’a maka anjima kuma In sha Allah zaku ha’du ku gaisa ku fahimci juna.” Ya yi shiru ransa da zuciyarsa na masa da’di da jin sunan duk da bai san waccece ba amma kawai sai yake ji a ransa koma wacece kyakykyawa ce kuma y’ar gayu don haka bai ji ko d’ar a zuciyarsa ba sai fatan Allah ya kai shi anjima ya ga zuk’ek’iyar budurwar kuma cikakkiya mai shekarun hankali kamar 22 haka ya tabbata zata d’auke duk wasu buk’atunsa baya shaawar auren yara mata k’anana ya fi son irin kamar degree holders haka. Tauraruwa ta saki murmushi kawai ganin yarda Murad d’in ya nausa cikin tunani da alama hasasho matar da zai aura yake. Tab’ ko ya za’a k’arke zai so Najwa ko kuwa zai ba su kunya.

Shigowar Najma da Nasma ya sa shi saurin juya kai wata irin ajiyar zuciya ya saki da yaga Nasma kyakykyawar yarinya irin yarinyar da yake so mai dirin jiki irin dirin da ake cewa Coca Cola shape ya lumshe ido yana fatan ta kasance itace Najwa. Don haka ya hau gyara zama har da su saita k’wayar idanunsa akanta yana sakin murmushinsa tsadadde da ba a ko ina yake yin sa ba sai an ci mugun sa’a.

Najma cikin nutsuwa da rashin kuzari ta k’arasa gefen kujera ta zauna a k’asa idanunta na kallon k’asa ta fara gaishesu. Ba wani alamar b’acin rai a fuskar kowa suka amsa gaisuwarta har Tauraruwa da ta ce “Ya jikin jikin? To Allah ya raba lafiya.” Kasa amsawa a fili ta yi sai a zuciya. Inno kuwa kasa yin shiru ta yi ta ce “Ma sha Allah tabarakarrahman suma wa’dannan yaran gidan nan ne?” Nene ta d’aga kai Tauraruwa ce ta d’ora da cewa “Wannan ita Jaheed ya fara aure kafin su samu sab’ani su rabu yanzu haka cikinsa ne a jikinta.” Inno da Murad a tare suka waro ido Murad ya ce “Rabuwa kuma?” A zuciyarsa yana jaddada wauta irin ta Jaheed ka samu wannan kyakykyawar yarinyar ka saketa haka siddan cabd’i. Tauraruwa bata ce komai ba ganin su Najman suna nan haka kawai sai ta ji ta fara jin tausayin yarinyar. “Tashi ku je Najma, ki dinga kula dai da kan ki ki gaida Mamanki kin ji.” K’wallar idonta ta share a hankali sannan ta mik’e jiri na d’ibarta haka Nasma ta rik’e hannunta suka fice daga parlourn. Murad kuwa bai d’auke idonsa daga kan Nasma ba, Tauraruwa da kowa na parlourn ya lura da kallon da yake mata. Suna fita ya juyo ya ce “Amma Ammeey me ya raba su?” K’addara da kuma Uwarta da ta zugata akan ba zasu yi zaman aure da d’an mahaukaciya ba marar asali, yanzu ga shi nan ta bar y’arta da damuwa don daga gani yarinyar nan tana son komawa gidan aurenta.” Murad ya kasa daurewa har sai da ya furta “Ita wannan kyakykyawar da ta fita itace matar tawa?” Sak kowa ya yi a parlourn har Umma da take zaune sai da gabanta ya fa’di suka zuba masa ido har ya tsargu ya yi saurin cusa hannunsa cikin tarin sumar kansa yana sunkuyar da kai da sakin murmushi a hankali. Tauraruwa ta harareshi ta ce “Futa daga nan Murad, na lura kai kyau kake so ba kyan hali ba, ba itace matarka ba ka je nan da bayan Magriba matar taka zata zo ta sameka ina tabbatar maka ta fi wannan duk abinda kake tunani kar dai Uwa Uba addini da tarbiyya su ji labari.” Murnarsa ce ta koma ciki jin abinda ta ce ya yi k’asa da muryarsa yana furta “Allah idan bata yi min ba sakinta zan yi na auri y’ar uwarta, ai ba wani abu bane tunda duk gida d’aya suke…” hararar da Nene ta wurga masa ce ya sa shi yin shiru da k’arashen zancen da ya yi niyya ya fita yana dariya. Zuciyarsa na sake jaddada masa in dai bai gamsu da zab’insu ba tabbas da sake!

Tauraruwa ganin duk kamar zuciyarsu a dame take ya sata sakin murmushi tana furta “Kada fa ku damu da abinda yace ba abinda zai faru In sha Allah sai alheri.” Allah yasa suka furta kusan duk a tare.
Chapter 23 · 0% Book details