Sashe 27
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
JIKAR Nashe Love you all… 🥳🤗
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Lab’bansa a kusa da nata da sauri ta ja baya tana runtse idonta da mugun k’arfi. Kafin ta ware idon a kan Food warmers d’in da Suka wancakale a gefe Allah yasa na a rufe suke b’am ba su bu’de ba. Ta tura shi da k’arfin gaske kafin ta mik’e tana harararsa k’asa k’asa. “An gaya maka ni y’ar iska ce? Ko irin matan da ka saba hul’da da su? Kada ka sake kusanto ni bana so.” Ta fa’da zuciyarta na mata wani irin zafi da takaicin abinda ya mata, take ta sawa zuciyarta tabbas Murad manemin mata ne idan banda haka ta yaya yake nuna maitarsa akan jikinta. Idan kuwa haka ne ashe an ha’data da babban aiki. Yana kallonta ta tattare kayan ya kasa aikata komai illa zuba mata nauyayyun idanunsa da ya yi. Itama jikinta rawa yake sosai don abinda baa saba mata ba ne, hasalima bata san haka auren yake ba ta d’auka kawai dai zata je ta yi girki ne da su aikin gida, bata zo nan ba ko a islamiyya a tv kuwa wajen turawa idan taga an yi hakan ta kan kwatanta su a matsayin y’an iska. Kuma ba musulmai ba a tunaninta musulmai ba zasu aikata haka ba. Ya mik’e da k’yar ya bi bayanta zuwa cikin parlourn ba don komai ba sai don kar Baffa ya ce me yasa bai shigo ya karya ba, amma yarda yake jin jikinsa kamar lafiya ta masa k’aranci. Tana dire abincin ta juyo suka kusa gabza karo harara ta zuba masa ta wuce. Murad ya bi bayanta da kallo yana sakin ajiyar zuciya. Bai iya cin komai ba illa ruwan black tea da ya sha kawai. So yake kawai ya gan shi a Garin Gabas a gaban Maimartaba ya sanar masa baya son zab’insu shi ga wacce Allah ya jarrabeshi da so. Baffa yana kallon yarda ya kasa cin komai don haka cike da kulawa ya ce “Malam Murad ka ci abinci mana.” Girgiza kansa ya yi a hankali ya furta “Tea d’in ma is enough ban saba cin abinci da safe ba.” Baffa ya yarda da batunsa don ya san mutane ireirensa da yawa. Yana gama sha ya mik’e yana kallon agogo ya ce “Babi yakamata ku zama ready mu wuce da wuri.” Babi ya d’aga kai yana furta “Yanzu kuwa In sha Allah. Yauwa Alhaji nace ya maganar ita Babar tasu yaushe ta shirya komawa masarauta don sun zo min da maganar nace a bari a sameka don yanzu dukkan wata ragama tata tana hannunka don kular da ka bata ko mu iyayenta ba mu bata ba.” Baffa ya girgiza kai “Zata koma In sha Allah, amma sai an yi addu’a ka san zaman masarauta dole sai da neman tsarin kai. Ba zata shiga sama ta ka ba.” Babi ya gasgata da zancensa don ya san gaskiya ya fa’da “Allah ya mana jagora ya fa’da yana kallon Murad “Maza ka je ka sanar da su su hanzarta mu tafi kada a ga rashin hankalinmu mun wuni mun kwana a gidan surukai.” Baffa ya girgiza kai ya ce “Mu dai bama gajiya da mutane balle ku bak’i masu alfarma.”
Tsaf suka gama shiri suka fito harabar gidan, Tauraruwa tana kallon Murad tace “Ka yi sallama da mutuniyar taka?” Murad ya tattare duk fara’ar fuskarsa ta gintse ko zancenta ba ya son a masa balle tuna mummunar fuskarta. Murmushi duka suka yi a wajen suka fita harabar gidan. Tauraruwa ce ta tsaya daga bakin sashen Mahmeey ta ce Jaheed ya kira mata Najma. Kallon Jaheed ya yi da alamun son k’arin bayani. “Ko ba zaka kira min ita ba ne?” Ya girgiza kai yana furta “Bari yanzu na kira ta.” Ya yi nocking k’ofar sashen Nasma ce ta bu’de muryarta a k’asa ta gaishe da Jaheed d’in. Ya amsa fuskar sa ba yabo ba fallasa. “Kira Najma In ji Ammeey.” Nasma ta amsa da to ta juya cike da zumu’di don kiran Yayarta don rashin nutsuwar da Yayarta take ciki itama abin yana tab’a mata zuciya matuk’a da gaske. A zaune ta ganta idanunta gaba d’aya sun fa’da ciki don tsananin rama ga cikinta da ya turo a gabanta. Nasma ta saki ajiyar zuciya cike da tausayi ta ce “Ya Najma ki zo in ji Yaya Jaheed….” Wani irin d’agowa ta yi tana kallon Nasman ta ce “Da gaske?” Ta d’aga mata kai cikin rawar jiki ta yafa mayafin ta ta mik’e a hankali ta fita harabar gidan. Sosai ta yi nufin durk’usawa Tauraruwa ta yi saurin saka hannunta ta tayar da ita tausayin yarinyar take ji yanzu. Suka amsa gaisuwar ta kalli Jaheed ta ce “Ka mayar da matarka yanzun nan bana son wata doguwar magana, ko bakomai ta ci albarkacin mahaifinta da ya baka dukkannin gata ga kuma d’an tahalik’in da yake cikinta da bai san hawa bai san sauka ba, don hk bn son wata magana data zarce ta na mai dake dakinki fak’at kuma bana son wata tashin tashina ta yi laifi kuma ta amsa laifin ta har ta baka hak’uri kuma ta yi nadama, ban ga amfanin rik’on ba. Allahn da ya haliccemu ma hak’uri yake da mu.” Jaheed ya d’ago yana kallon Najma da take zubar da hawayenta ba k’akkautawa tsimammiyar k’aunar da yake mata ta tashi sai ya ji hankalinsa ta tashi da ganin hawayenta shi kansa ya da’de da fara tausayinta cijewa kawai yake ya kasa furtawa. “Ba yafe mata kuma na mayar da ita d’akinta Allah ya sa mu zama abin alfahari a wajenku ya ba mu zaman lafiya.” Wata irin k’akkarfan ajiyar zuciya Najma ta sauke shi kansa Baffan ajiyar zuciyar ya saki ya da’de da tausaya mata k’arfin hali da dattako irin nasa ne yasa ya kasa furtawa Jaheed ya yi hak’uri ya mayar da matarsa. Najma ta dinga Jin wani sanyi na Ratsa sassan jikinta. Tauraruwa ta sake musu addu’a sannan ta kalli Najman ta ce “Sai ki hanzarta ki koma d’akinki a cikin satin nan kada ki haihu musu a gida.” Ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, murya a tausashe ta ce “Nagode” ta musu Fatan sauka lafiya kafin ta shige gida kai tsaye jikin Mahmeey ta fa’da tana sakin dariyar farin ciki. Itama Mahmeeyn dariya take ta dafa bayanta ta ce “Allah ya yi kenan Tabbas na san Allah ne ya jarrabemu ba don komai ba sai don tsana da k’yamar da muka nunawa Jaheed sai ga shi yau da kan mu muke rok’onsa ya mayar da ke d’akin ki, tabbas yanzu na shaida d’agawa da girman kai ba inda suke kai bawa sai tashar dana sani, Allah ya Raba mu da wad’annan halayen.” Ameen yaran suka ha’da baki wajen fa’da shikkenan sai kuma suka fara shirin yarda zata koma gidanta bayan bikin Najee In sha Allah.
A masarautar gabas fa duk wasu shirye shirye sun kankama. Murad kawai kallonsu yake yi yana jin ba abinda zai saka shi zama da wannan yarinyar mai kama da……. Don haka ana Gobe d’aurin aure ya isa sashen mai martaba ransa a b’ace gaba d’aya har rama ya yi saboda rashin nutsuwar zuciya ya samu Mommahn sa Saddik’a da zancen ta rigime ta ce bata san wannan zancen ba dole ya auri zab’insu idan ba so yake ya ha’da rigimar da ba zata mutu ba. A zaune ya samu Maimartaba da Tauraruwa sai Fulani Saddik’a a gefe suna cigaba da tsare tsaren yarda za’a Gudanar da biki. Tauraruwa tana ganinsa ta saki murmushi ta ce “Dama tun d’azu nace Yayanku ya nemo min kai,(tana nufin d’anta) zancen Dinner ban ji kace komai ba, ko baka son nunawa abokan ka amaryar ne?” Fuskarsa ya sake ha’dewa sosai ya furta “Ba wata dinner da zan yi, a bari sanda na auri zab’in raina na yi dinnerr…” Tauraruwa tana murmushi ta ce “Shikkenan Ai hutaroro dama shima Baffanta ba son bidi’a yake a biki ba, sai ma da ya rok’emu kada mu yi wata bidi’a…” “Idan auren ya yi yu ba.” Murad ya furta a hankali…. “Me kace?” Maimartaba ya fa’da yana kallonsa. Murad kansa tsaye ya ce “Ni dai Bahbah a min afuwa bana son yarinyar nan kuma idan aka matsa na aureta zan iya ha’duwa da ciwon zuciya…” Maimartaba da dama ya Riga ya san zancen sai ya saki murmushi ya ce “Ai kuwa sai fatan Allah ya baka lafiya don aure kamar an d’aura shi idan ba so kake na yi fushi da kai ba wani irin zancen banza ne wannan, ana gobe d’aurin aure kace baka son matar sabida ka raina mutane….” Murad bai furta komai ba illa mik’ewa da ya yi yana jin wani irin jiri na d’ibarsa haka ya fice. Suka bi shi da kallo duk tausayinsa ya kama Fulani Saddik’a ji take kamar ta je ta gaya masa gaskiya. Maimartaba da Tauraruwa kuwa dariya suka saki gaba d’aya suna hango Murad a gobe idan ya je yaga wacece amaryar tasa? Wani irin farin ciki zai yi?