← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru ya biyo baya a parlourn ba don komai ba sai don mamakin kalamanta, da Suka shiga kunnuwansu a bazata. Umma a fusace ta daka mata Tsawar da ta sata saurin yin shiru daga surutun da take zubawa ba ruwanta iyakar gaskiyarta take fa’da kamar bata son me ke tsakanin jama’ar da ke gabanta da Murad ba, Uwa da ta haifeshi da k’anwar Ubansa da yake matuk’ar so sai marik’iyar da haihuwarsa ne kawai bata yi ba, su ta kalla k’iri da muzu take furta musu ba ta son d’an su, kuma ba abinda ya dameta. Shiru ta yi tana kallon Umman da ta tsatstsareta da ido. Hakan yasa Tauraruwa sakin murmushi ta ce “Kyaleta Umman yara ra’ayinta ta fa’da kuma ko bakomai har yanzu akwai yarinta a kanta, don haka dole a mata uziri amma ina tabbatar miki na lokaci ka’dan ne zata yi rigima daga baya zata so auren nan zata so Murad fiye da k’ima sai dai mu bi su da addu’a kawai dafatan Allah yasa abinda muka k’ulla ya zame musu alheri. Zo nan Daughter.” Sai a sannan kuma sai ta ji kamar bata kyauta ba, kamar bai kamata ta gaya musu hakan ba, kunya ta kamata. Ta kasa k’arasawa wajen Tauraruwa da take ta kiranta har sai da Tauraruwar ta mik’e da nufin kamota sai ta yi saurin shiga ciki da sauri. Tauraruwa tana dariya ta bita har cikin d’akin Umman inda ta tarar da ita ta zauna a gefen gadon ta takure kanta. Tauraruwa ta saki murmushi ta ce “Tashi Najwa magana za mu yi. Bana son kunyar nan ni y’a na d’auke ki ba surika ba. Saddik’a ce surikarki. Ta shi maza mu yi magana.” Idonta a lumshe ta d’an mik’e Tauraruwar ta saka hannu ta d’aga hab’arta ta ce “Bu’de idanunki Najwa Umarni nake baki ba rok’o ba.” Najee ta bu’de idanunta da gashin idon ya musu gazar gazar. Tauraruwa ta saki murmushi a zuciyarta tana yaba kyawun Najeen duk da bata da haske amma fatarta mai kyau ce da gaske irin fatar nan da take da tsada sosai a cikin mutane d’ari da k’yar zaka samu mutum guda mai golden skin d’in nan sai me rabo. “Yauwa gaya min ba kya son Murad ne?” Da sauri ta d’aga kai. Tauraruwa ta saki murmushi tana hango tsagwaron yarinta a idanunta ta ce “Me yasa ba kya son sa?” “Saboda shima baya sona ya tsaneni, duk sanda muka ha’du hararara yake yi da tsaki kuma yana ce min Witch….” Tauraruwa ta waro ido ta ce “Witch kuma? Shi Murad d’in ne yake ce miki witch?” Ta d’aga kanta har tana sakin hawaye tsanar Murad na sake k’arfi a zuciyarta, da gaske bata son sa bata tab’a kuma raya shi a ranta ba kamar yarda take raya Jaheed a matsayin Miji. “Ni Jaheed nake so…” ta fa’da cikin k’arfin gwiwa da karayar harshe duk don Tauraruwa ta tausaya mata. “Duk wanda ya so Jaheed zai so Murad Najee saboda abu guda ya yi su, kuma ko a b’angaren halitta ba su da banbanci, ni kuma da zan baki shawara sai na ce ki aureshi ko don ki rama mayyar da ya kira ki da ita ki cusa masa bak’in ciki….” Ta fa’da tana kallon cikin k’wayar idon Najee da ta fara hango alamun zata yi nasara zata cigaba da d’ora zuciyarta akan cewa zata Auri Murad ne don ta yi ramuwa tana ganin da wannan kawai za su samu lagonta, “Wai ma duk yaushe kuka ha’du har yake kiranki da witch kuma me yasa?” Wata irin dariya Najee ta saki da ta bayyana siraran hak’oranta ta kuma lob’a k’aramin bakinta, kamanninta na wancan lokacin da ta b’atar da kama ta tuna. Da sauri ta mik’e ta janyo wayar Umma da take saman mudubi ta bu’de ma’adanar ajiye hotunanta sai ga kamanninta na waccan Najeen ta gidan sarautar gabas sun bayyana a hoton ta mik’awa Tauraruwa wayar tana furta “Ba ni ya gani ba, wannan Najwar ya gani haka kawai ya kafa min karan tsana ya zata haka nake…” Tauraruwa kanta sai da ta dara ta tabbatar kuma ko Karen hauka ne ya ciji Murad ba zai yarda ya auri me wannan siffar ba yarda yake dan gayu na bugawa a jarida. Dariya ta yi sosai Najwan na sake bata labarin dramar da
Suka dinga yi da Murad a gidan Sarkin. Tauraruwa ta jinjina kai tana furta. “Yauwa abinda nake so da ke ki amince ki auresa cikin ruwan sanyi sai ki rama abinda ya miki, kina gama ramuwar sai a raba auren.” Najwa ta d’aga kai “Na yarda amma idan kun amince zan je masa a kamannin waccan Najeen me basaja ba don komai ba sai don na jarrabashi idan ya ci jarrabawar zan amince na zauna da shi idan kuma bai ci ba ya wulak’anta ni zan bayyana masa kai na kuma ko ya dawo yana so na sai ya sake ni.” Tauraruwa ta d’aga kai tana jinjina wautar Najee ita kuma dariya kawai take tana hango ranar da Murad zai shiga gidansa ya ganta a matsayin matarsa, sai ta samu kanta da sakin dariya sosai ta ji tana son auren har ma tana jin kamar ta janyo ranar. Tauraruwa dai da taga ta samu nasara sai ta mik’e ta fita parlourn fuskarta d’auke da murmushi ta kalli Nene ta ce “Wannan y’ar taki sai kin yi da gaske Nene zata yi zaman aure.” Nene dariya ta yi kawai tana jin wani sanyi a ranta da zata ha’da jini d Najee zata haifa mata jikoki, ashe hikimar Ubangiji kenan da ya Kimtsa mata k’aunar Najee a ranta ashe zata zama surikarta. A hankali ta furta “Y’ata gangariya ce Ammin yara sai kun yi da gaske zaku samu soyayyarta.” Tauraruwa ta ce “Ai naga alama Raheena sai ki shirya. Yanzu dai ku tashi mu tafi tunda na samu damar shawo kanta sai dai akan yarjejiniyar ba zai ganta ba sai ranar da aka kaita gidansa sannan zai ga Najee amma bisa b’atacciyar kamar da kuka shiga da ita masarauta.” Nene da Raheena suka waro ido kafin Raheena ta ce “Kina son ya sakar mata y’a a daren kenan? Ta ina Yareema zai amince da auren waccan Najeen?” To ya zan mata tunda yarinya ce ai dole a bi ra’ayinta kafin komai ya daidaita yanzu idan aka ce dole za’a mata wallahi ba za’a ga da kyau ba, a hakan ma a zuwan auren d’aukar fansa za’a yi sannan fa ta amince.” Kowa a wajen dariya yake banda Umma da ranta ya b’aci ta jinjina wautar Najee a ranta da tunanin kalar fa’dan da zata mata idan sun tafi. Yarda take cizon yatsanta ne yasa Tauraruwa kallonta ta ce “A’a fa Hajiya kada ki mata komai don Allah, a hankali za’a bi da ita yarinya ce.” Umma ta saki murmushi kawai suka mik’e suka raka su har mota anan Nene ta ja ta tsaya. Har sai Tauraruwa ta kalleta ta ce “Shigo mana Nene.” Ta girgiza kai ta ce “Ai ni nazo gida..” Da sauri Maimartaba ya d’an juyo ya kalleta. Aka ka’da aka raya ta shiga ta ce “Aa ba inda zata dama shima Jaheed ba komawa zai yi ba sai an kwana biyu zai je da iyalinsa su gaisa da danginsa. Ganin ta turje sai Baffa ya yi murmushi ya ce “Ku k’yale ta idan komai ya daidaita aka samar mata d’akin da zata zauna aka kuma jaddada aurensu da maimartaba da kaina zan kai ta har d’akinta In sha Allah, kafin nan a bamu kwatancen inda iyayenta suke a yola zamu kai musu ziyarar Bazata In sha Allah.” Tauraruwa ta jinjina kai duk da bata so haka ba amma hakan shi ya kamata don haka ta ce zata aiko da wanda zai musu jagora har Yola inda Babi su ke da Inno cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali.” Suka sake jaddada godiyarsu ga Baffa da Umma sannan suka ja Mota suka tafi Murad yana jin kamar ya musu tawa ye ya k’i bin su sai dai kaifin idanun Fulani Saddika ya hana shi tasiri ba zai iya bujire mata a gab’ar da take neman mai rarrashinta don haka sai kawai ya d’agawa Nene da su Jaheed hannu suka fita daga harabar gidan. Nene ta saki ajiyar zuciya tana jin k’irjinta wasai ba wannan tarin cunkoson b’acin ran sai farin ciki da annashuwa kamar an mata albishira da aljanna.
Chapter 17 · 0% Book details