Sashe 11
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani dare da ba zan tab’a mantawa da shi ba cikin talatainin dare na dinga jin motsi ana shigowa b’angaren da nake, ban tsorata ba don na san Amintacce ne, na mik’e zuwa parlourn ina haska y’ar k’aramar torch light da take hannuna. A zaune na gan shi jikinsa sai rawa yake ba shi da nutsuwa sam a lokacin. Nima na tsorata na zauna ina kallonsa a raunane na ce “Gaya min me ya faru?” Ya d’ago idanunsa da suka raunata a hankali ya ce “Sun gane ni Tauraruwa sun gane ni malek’in sirrinsu ne ina tsoron cutarwarsu gare ni.” Shiru na yi ina kallon idanunsa da yarda suka bayyana raunin da zuciyarsa take ciki na girgiza kai ina furta “Allah ya fi k’arfin su ka nutsu ka gaya min me suka ce maka?” Ya lumshe idanunsa hawaye na bin fuskarsa ya ce “Sun sace y’ata Tauraruwa ban san me za su je su aikata mata ba….. Sun kuma rantse idan na gayawa wani za su kashe ni su kuma kashe dukka iyalina….” Na bu’de ido ina kallonsa na ce “Y’arka fa ka ce sun sace? Wace y’ar taka? Y’a mace d’aya da ka mallaka daga cikin yaranka?” Ya d’aga kai rauninsa na sake na bayyana…….
Na girgiza kai na ina sakin murmushi na ce “Ka share hawayenka Amintacce ba abinda zai samu y’arka In sha Allah sai alheri, ina son ka je ka cigaba da saka musu ido, babu abinda zai samu y’arka In sha Allah sai alheri.” Gwauron ajiyar zuciya ya sauke yana kallo na da raunatattun idanunsa kafin ya girgiza kai ya ce “Na yarda da ke Tauraruwa, na yarda ba zaki bar wani abin cutarwa ya samu y’ata amma ina tsoro ina jin firgici kada su tozarta mutuncin y’ata.” Shiru na masa cike da tausayinsa na Kuma ji a raina ina son taimaka masa ba kuma na son wani abu ya samu y’ar tasa. “Tashi ka je amintacce a daren nan zan san abin yi.” Na fa’da masa cike da k’warin gwiwa. Jikinsa ba k’wari ya mik’e ya fita daga b’angaren nawa. Tunda ya fita ya bar ni na kasa mik’ewa daga inda nake zaune, zuciyata cike take da tunanin samun mafita, da gaske kuma bana son wani abu ya samu zuri’ar amintacce don na san idan har wani abu ya samesu ni ce sila, kai tsaye zan iya cewa ni ce na jawo musu. Ban samu mafita ba don gaba d’aya a daren sai kwanyata ta zama kamar bata aikin da ya kamata.
Har washegari ba ma fitar a gareni sai ga shi a daren ranar ya sake dawo min jikinsa ba k’wari. Zama na yi ina kallon yanayinsa zuciyata na wani irin bugu, murya a tausashe na ce “Sun saketa?” Ya girgiza min kai “Ba su saketa ba ranki ya da’de asalima sun bijiro min da buk’atar da ta razana tunani na, sun ce kuma dole na yarda idan ba haka ba za su kashe yarinyar.” Da sauri na d’ago ido ina kallonsa na ce “Me suka ce maka?” “Sun buk’aci lallai sai na amince an dasa k’waya k’wayan haihuwar Sarki a jikinta za’a ha’da da na Fulani Raheena idan ta haife abinda ta haifa za su karb’e sai su sallameta na bar garin da ita idan kuma ba haka ba, sai dai su kasheta don gudun fallasuwar sirrinsu.” A kishingi’de nake ban san sanda na mik’e ba ina kallonsa na ce “Dashen ciki fa ka ce Amintacce? Cikin ma
Kuma na Raheena? A yaushe suka ce za su yi mata?” Ya girgiza kai a hankali ya furta “A yau cikin dare suka ce za su mata…” “A ina kake tunanin sun ajiyeta?” Na fa’da hankalina a tashe. Cikin raunin zuciya ya ce “Ban sani ba, sun b’oye hakan daga gareni.” “Ka je ka bi diddigi amintacce idan ka samu inda take kazo ka sanar min, a yau ba sai gobe ba ya kamata mu fatattaki shirinsu ta hanyar da har abada zamu musu lahani.” D’aga min kai ya yi kafin ya mik’e gwiyoyinsa a salub’e ya fice daga wajen, na bi shi da kallon tausayi ina addu’ar kada Allah ya basu ikon cutar da baiwarsa.
A ru’de cikin tashin hankali ya dawo a cikin daren jikinsa na kakkarwa ya zube a gaba na yana furta “Shikkenan Tauraruwa burinsu zai cika sun shiga da ita inda zaa mata dashen su da wata likita…..” Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna shine abinda na furta kawai ina rik’e kai na…..
A min afuwa don Allah na sab’a alk’awarin da na yi jiya uziri ne Babba ya rik’e ni. Wanda na sanar muku jiya. Na gode da ha’din kan da kuma ba ni da addu’ar da mamaci ya sha zan muku typing gobe In sha Allah don na cike gurbi. Na gode sosai.
JIKAR NASHE✍🏽🥳
08033748387.
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Kallon da Yake mata kai tsaye yana bayyana tsananin mamaki da ru’danjn da zuciyarsa take ciki, bayan abinda ya kira rainin hankali daga gareta sai kuma mamakin tsananin kamanninsu da ya ru’dashi don haka abin ya ha’du ya masa yawa, har ya gaza furta ko kalmar a daga tarun maganganun da suke dank’are a zuciyarsa wanda ya kamata ya gaya mata su a take. Lallai matar nan da k’arfin hali take ya furta a hankali amma kuma zan shayar da ke kalar nawa mamakin. Murmushin shima ya yi mata yana kama hannunta da take mik’o masa. “Kada ka yarda da duk abinda ta fa’da Jaheed!” Ya juyo muryar da ko bai juya ba ya san Jaheed ne, bai fasa abinda ya yi niyya d’in ba na kama hannunta ya rik’e lokaci guda yana sake jifanta da mayaudarin murmushi da yake k’ak’aro shi da k’yar. “Ke ce Umma na da gaske?” Ta d’aga masa kai “Tabbas ni ce Ummanka Jaheed, Nene ni ta haifawa ku.” “Ta yaya?” Jaheed ya fa’da yana jefa mata tambayar da ta saka ta kallon k’wayar idanunsa ta furta “KUDIRAR ALLAH.” Girgiza kansa ya yi yana juyawa yana kallon Murad da ya k’araso wajen da d’an hanzarinsa ya fincike hannun Jaheed d’in yana furta “Baka ji abinda na ce maka ba ne? Ta yaya zaka amince da ita? Ka tab’a ganin yarda Mace biyu suka samar da haihuwar mutum guda?” Madadin Jaheed ya saurare shi gani ya yi kawai ya rungume shi da sauri cikin murna yana furta “Alhamdulillah Allah, Alhamdulillah for today and forever.” Wasu hawaye suna zubo masa. Murad ya saka hannu yana bubbuga bayansa gefe guda kuma yana wurgawa Tauraruwa harara da itama take kallonsu tana sakin nata murmushin wani farin ciki marar misali yana sake rub’anya a zuciyarta yau gata ga jinin su ita da Maimartaba abinda suka cire tsammanin faruwarsa. Ji suka yi kawai ta rungumesu itama. Da sauri Murad ya saka hannu ya d’an tureta kafin ya ja gefe yana watsa mata kallo ya kuma finciki hannun Jaheed suka bar wajen a d’an hanzarce Jaheed ya ja hannun Faruk da yake tsaye yana kallonsu cike da murna shi ma, tabbas ba sai an fad’a ba kana ganinsu ka ga y’an biyun da ake kira identical twins.
Mutanen wajen da dama bin su suka yi da kallo, nan da nan gulma ta samu wajen zama a masarauta kowa yana jinjina girma ga k’udirar Ubangiji, ga duk wanda ya san Tauraruwa da irin soyayyar da suke wa junansu ita da mai martaba ya kwana da sanin cewa zata iya sarayar da dukkan farin cikinta don farin cikin sarki, amma ba su yi tsammanin har zata iya sarayar da rayuwarta ba tsawon lokaci ta b’ace b’at sai yanzu ta bayyana da abin ban mamaki yara har biyu kuma halattattun
Jinin sarki, kan su ya d’aure ga wanda ya san mafarin abin ga wanda bai sani ba kuwa sai ya zama kansa a cikin duhu yana kuma lalube a duhun da son sanin ta yaya aka haihu a ragaya? Shirun shine ya fi alheri har zuwa ranar da tauraruwar zata gaji ta bayyana sirrin da take k’udundunewa. Ta bi bayansu da kallo kafin ta ja k’afafunta ta wuce tana sakin murmushi so take ta je ta isar wa da Maimartaba da kyakykyawan albishir da bata son wani ya rigata. Zata sanar da shi zuwan Jaheed yaron da bai tab’a ganinsa ba a rayuwarsa. Gwara ita tana yawan ganinsa a sigar da bai zama lallai ya san wacece ita ba, tana da hotunansu da komai nasa ba tare da ko su iyayen rik’o nsa suna da masaniya akan bibiyar da take musu ba.
Tunda labarin iso watsi ya shiga kunnen Nene da Fulani Saddik’a daga bakin amintattun bayin fulanin murna ta cika zuk’atansu dafatan Allah yasa wannan karan asirin komai ya fallasu a kuma tabbatar da su matsayin y’ay’an Nenen halastattun y’ay’a. Shigowar Jaheed yasa su mik’ewa Fulani ta dinga kallonsu cikin mamaki da k’udirar Allah, kamaninsu kwabo da kwabo sun bayyana k’arara ta yarda dole a kira su jini guda. Banda yanzu Murad ya bar parlourn tabbas da ba zata iya banbance su ba, sai dai shi Jaheed fuskarsa a sake take koda yaushe cikin yalwar fara’a sab’anin Murad da fuskarsa take a tsare mai nuni cikar mazantakar d’a namiji. Jaheed ya isa gaban Nene yana fa’dawa jikinta cikin murnar ganinta ta sake haske sosai don tuni ta wanke duk wani abu da ya b’oye kamanninta tun bayyanar sirrinta. Murmushi kawai ta saki tana kallon Faruk da masa alamar ya shigo. Wajen zama ta ba shi sannan ta zauna itama Murad da Jaheed suka zauna Jaheed kusa da Nenen daf shi kuma Murad sai ya koma kusa da Fulani da ya ji kunyar yi mata butulci. Hakan da ya yi kuwa, sai ta ji ya burgeta.