Sashe 7
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fulani Saddik’a cikin d’akinta ta shigar da shi. Kafin ta koma kitchen ta ha’da masa tea mai lipton zalla don dai ta san cikinsa yau kam bai ga abinci ba, kamar yarda nata itama bai gani ba. Kanta a d’aure yake da tarin tambayoyi sai dai bata bari hakan ya bayyana akan fuskarta ba. Ta d’ebo tea d’in bayan ta soya masa scramble egg ta fito da su zuwa d’akin nata. A zube yake a k’asan carpet ya yi pillowa da hannayensa yana kallon ceiling. Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Murad me ye haka? Sarki guda mai jiran gado a zube a k’asa, tashi maza ka sha tea idan ba so kake ka sake d’aga min hankali ba.” Ya mik’e kamar yarda take so ya kuma karb’i cup d’in a hannunta bai yi la’akari da zafin sa ba ya kafa
A bakinsa. Da sauri ta kalleshi sai dai kafin ta yi magana ya zuk’eshi tas yana mayar da numfashi. A tsorace ta kalleshi “Me ye haka Murad?
Kana cikin hankalinka kuwa?” Da k’arfin gaske ya runtse idonsa ya furta “Bana ciki Mamma, ina son sanin wacece waccan matar?” Da sauri Fulani Saddik’a ta kafa masa ido, tana son karantar yanayin da yake ciki. Tsoro ne ya kamata ganin kamar Murad cikin zakwa’din son sanin mahaifiyarsa yake, idan kuwa hakane ya zama na ita zata tashi a tutar babu. Da sauri ta dakatar da zuciyar ta ta kuma ha’de rai tana kallonsa ta ce “Me kake son sani game da ita? Kana son ka san ko itace mahaifiyarka a zahiri? Me hakan yake nufi akwai inda na tauyeka ne?” Ta fa’da cikin yanayi mai nuna zallar b’acin ranta. Wannan karan abin da ta yi bai da Murad ya ji zuciyarsa ta canja daga zakwa’din son sanin ainahin mahaifiyarsa ba da ma d’an uwansa guda da zai kira tilo, sai dai gudun b’acin ranta sai ya danne damuwarsa ya koma ya kwanta kamar yarda yake a da, sai dai yanzu ya lumshe ido ne yana cigaba da saurarar sak’a da warwara da zuciyarsa take masa. Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa ganin kamar barci ya d’aukeshi ta fice daga d’akin da sauri don isa wajen su Nene da take tunanin acan duk amsoshin tambayoyinta su ke.
Yanayin da ta bu’de k’ofar zai tabbatar maka da ta na cikin rashin nutsuwa. Nene da suma suke cikin rashin nutsuwar suka d’ago da sauri suna kallonta. Fuska ba walwala ta isa wajen su, ba tare da ta rufe k’ofar ba. Ta zauna idanunta cikin na Nene ta ce “Ki sanar da ni wacece ke? Sannan kuma ina son sanin shin abinda kika fa’da min da gaske ne ke kika haifi Murad ko kuwa?” Nene ta saukar da idanunta k’asa kafin ta jijjiga kai ta ce “K’warai har a yanzu bana manta rad’ad’i da zafin naku’dar haihuwar Murad da na yi nice mahaifiyarsa abinda yake bani tsoro waccen matar da ta bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tabbas shine irin turaren da nake ji a jikin matar da ta taimakeni a wancan lokacin….” Da sauri Fulani Saddik’a ta bu’de manyan idanunta ta ce “Da gaske?” Nene ta ce k’warai kuwa ban mance ba, sanda ta ke taimakona ina nak’udar Murad ita kuma ta bani mak’udan ku’dad’e da gwalagwalai ta ce na nesanta kai na daga masarautar gabas kada na sake dawowa don akwai mutanen da suke jiran rayuwata abinda yasa kenan na yi nisa da garin nan, amma tabbas ni na yi nak’udar haihuwar Murad na kuma d’aukeshi a cikin tsawon watanni tar……. Yawun bakinta ne ya k’afe ganin Murad yana tsaye idanunsa cikin na Nene da ta ha’diye sauran maganar a cikinta. Yana nuna ta da yatsa ya ce “Ke ce magaifiyata? Me yasa kika b’oye min?” Ya fa’da yana zubewa a gabanta….
JIKAR NASHE✍🏽🥳
[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: “Au Hassan d’inka.” Nene ta fa’da tana kallon idon Murad da Yake mata nuni da alamar shine babba. Murmushi ya saki jin gyaran da Nenen ta yi ya amshi wayar yana gyara muryarsa da kyau don ta sake kaurara ya yiwa Jaheed barazana da ita. “Hello Yayanka Murad ke magana.” Jaheed daga can ya runtse idanunsa yana tunanin shin da gaske ne abinda kunnuwansa suke gaya masa ko kuwa k’ailular mafarkin da ya saba ce. “Murad da gaske kai ne?” “Point of correction Malam, Yaya Murad dai ko?” Jaheed ya saki dariya sosai daga jin muryar Murad ya san za’a yi rigimammen gaske sai ya dinga imagining d’insa a k’wayar idanunsa “Mhmn girman kwana nawa ka bani? Har na matsu nazo na ganka wallahi.” Kamar yarda nima na matsu na ga stubborn brother na da zan saka aiki ya yi kuma ko yana so ko baya so, dama ka shirya maza maza ka taho, ya kamata mu fuskanci mahaifinmu da wannan lamarin.” Jaheed ya saki ajiyar zuciya mai tafiyar da duk wani hucin bak’in ciki da yake cin ransa na shekara da shekaru ya furta “Wannan shine zance, zan zo Murad jibi ka saka ido In sha Allah.” Murad ya furta “Rabbi ya sha.” Kai tsaye yana kashe wayar idanunsa cikin na Nene da take kallonsa tana jifansa da murmushi mai bayyana tsananin soyayyar da take tsakanin uwa da yaranta. Wani irin Farin ciki ne yake sake kwaranya a zuciyarta wanda ba shi da misali. Murad ya kama hannayenta “Da zarar Jaheed ya zo ina so duk wani tsoro da shakka ya kauce daga wajenki Mah, Ina son ki jajirce komai ma zai faru ya faru amma ba zai yiwu kura da shan bugu….” Ya fa’da yana kallon tsakiyar idanunta sai kuma ya matsa yatsunta “Ki saka a ranki Sojan d’an ki na tare da ke, zan tsaye miki har sai naga an yi miki adalci a cikin duk wani hukunci da za’a zartar okay?” Idanu ta lumshe bayan ta d’aga masa kai kwanyarta na sake maimaita sunan Mah da ya kirata da ita, sunan ya yi da’di akan harshensa wato shi ba zai kirata da Nene ba sai Mah. Sai ta ji a ranta ta samu k’arfin zuciyar fuskantar duk abinda zai ma faru a gaba, ta shanye ma abubuwan fargaba da suka gabata balle yanzu. “Promise Mah?” Ya fa’da yana sanya mata hannunsa mai nuni da d’aura alk’awari nata yatsun k’arami ta saka ta sark’afe cikin nasa tana furta “In sha Allah Murad.” Ji kawai ta yi ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya a hankali ji yake ruwa da iska ba mai raba shi da mahaifiyarsa yarda yake jin son ta a dukkan sassan jikinta tun kafin ma ya san itace ta haifeshi balle yanzu da ya san itace ta d’au cikinsa ta kuma yi nak’udarsa. Tsawon lokaci yana jikinta yana jin d’umin jikinta da yake tafiya da dukkan damuwarsa, baya ta matar da aka aura masa abu guda ya sani in dai bata masa ba a daren zai bata red card don haka ba ta gabansa bai kuma damu ya san wacece ba, soyayyar Amra ce har yanzu a cikin ransa ita kuma take fusgar zuciyarsa.
**
Jaheed yana kashe wayar ya dubi Khaireey da take ta kallonsa ba ko k’iftawa, ya furta “Ki ha’da kayanki za mu wuce Nigeria.” “Nigeria kuma?” Ta furta idanunta cikin nasa “Ya d’aga mata kai, “Ya zama dole na je ne, duk da dai da ban yi niyyar zuwa ba sai kin haihu amma yanzu zuwan na dole ne, ana sa rai da ganin mahaifina a yau na yi magana da d’an uwana da ba ni da tamkar sa.” Cikin zallar farin ciki Khaireey ta daka tsalle tana furta “Alhamdulillah!” Da sauri ya rik’eta idanunsa a kan cikinta “Ya ce are you mad Khaireey? Kin manta ba ke ka’dai ba ce?” Ta d’an turo bakinta kafin ta d’ane cinyarsa ta ce “Habibi murna fa nake, duk dai bana son mu je Nigeria saboda yarinyar can da aka ce zaka aura Wallahi bana sonta sosai nake kishinta.” Ya kau da kai fuskarsa a ha’de sosai yana furya “Ni kuma ina sonta, don kuwa dole na so ta don Mamanta ta yi min halacci…” waro ido ta yi tana kallonsa zuciyarta na bugawa da saurin gaske ta ce “Habibi da gaske aurenta zaka yi kenan?” Bai amsa mata ba ya mik’e don ha’da musu kaya bayan ya yi requesting ticket a online. Ita kuwa tana zaune cikin b’acin rai kawai tana kallonsa har ya gama ya juya ya bata kallo d’aya kawai yana furta “Gwara ma ki cirewa kan ki damuwa don aure na Da Najee ki k’addara kamar an yi shi an gama..” yatsu ta saka kawai ta toshe kunnuwanta idanunta na zubar da hawaye Jaheed ya wurga mata harara kafin ya jata ta fa’da kansa ya rungumeta “Open your ears in tunatar da ke abinda kika manta, Iyayen Najee su suka mayar da ni mutum a lokacin da nake cikin tagayyarar rayuwa ta yaya kike son na zuba musu k’asa a ido, duk da ban tab’a son Najee a matsayin matar aure ba, amma ina jinta a jikina kamar wani sashe ce ita a rayuwata don haka ki nutsu kada ki sakawa kan ki zafin kishi aure na da Naji kin san abinda Bature ke kira confirm! To shine.” Daga haka ya yi kissing bakinta har da cizonta a leb’e yana furta “Jealous girl.” Ya nata cakulkulin da ya sata saka dariyar da bata shirya ba. Shima murmushin ya saki yana fita daga d’akin haka yake a rayuwarsa baya son yaga ran wani ya b’aci ta dalilinsa. Khaireey ta bi bayansa da kallo tana jin zafin kishinnata yana sake hauhawa..