← Book details Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 43

Sashe 3

Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

**Najwa kuwa zubawa Nene ido ta yi tana mamakin yanayin da ta shiga na dogon tunani. Murya a raunane ta dafata tana furta “Kada ki sawa kan ki damuwa fa Nene.” Girgiza kai ta yi “Ba damuwa na yi ba Najee, ina tunanin yarda k’addara ke watangaririya da rayuwata ne yau fari gobe tsumma, babban takaici na rashin sanin takaimaimai inda Iyayena suke suna raye ko sun mutu.” Najee ta d’aga kai ta ce “Dole za ki damu na sani amma ki saka a ranki duk wani bawa baya wuce k’addararsa mai kyau ko akasinta, ta ki jarrabwarce ta zo a haka In sha Allah kuma kin kusa amsata daidai nasara na tafe In sha Allah.” Nene ta zuba mata ido cike da k’aunarta ta ce “Allah yasa Najee, idan kuma k’addara ta sa Sarki ya min mummunan hukunci ina rok’on Ubangiji ya baku wuyan d’auka.” Ta fa’da tana share zufar da take kwaranyo mata har saman wuyanta. “Kira min Umma d’azu kin ce ta kira bana cikin yanayin da zan iya amsa waya, yanzu kuwa na samu nutsuwa kad’an da na sanar da Murad nice mahaifiyarsa.” Najee ta ciro wayar a jakarta tana danna kiran layin Umma tana sake maimaita sunan Murad a ranta zuciyarta cike da tsanarsa da jin haushin kallon wulak’ancin da yake mata “Matarka ta shiga uku!” Ta furta a zuciyarta ba tare da sanin cewa maganar tata ta fito fili ba. Nene ta bita da kallo tana murmushi ta ce “Wa kenan?” Da sauri Najee ta jijjiga kai sai kuma kunya ta kamata ganin kamar Nene ta gano wanda take nufi ba zata so ace ta zagi d’an a gaban Uwarsa ba don haka ta bagarar da zancen tana kara wayar a kunnen Nene ta ce “Ga Umman.” Nene ta amsa tana sakin murmushi zuciyarta na sak’a mata abinda kai tsaye zata kira almara auren Murad da Najee gwara ma dai a tsaya a Jaheed d’in shine mai sanyin hali, ba Murad mai zafin zuciya ga k’arfin izzar mulki da na Soja a tare da shi, ya yiwa Najee girma halayensa bana rik’on k’aramar yarinya mai k’ananun shekaru irin Najee ba ne. “Nene ba kya ji ne?” Umma ta fa’da daga d’ayan b’angaren jin Nenen ta yi shiru bata ce komai ba. Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauke kafin ta ce “Ina ji Umman yara, an yi sallah lafiya? Kin ji ba mu kira ba ko wani al’amarine mai girma ya hana mu kira.” Nan ta shiga bawa Umman labari. Cikin mamaki da al’ajabi Umman ta ce “Ikon rabbi! Yanzu ya kenan? Ga shi Baffa gobe zai dawo bana son ya dawo bai tarar da ku ba, ko Najee zan saka a d’auko min idan yaso ke sai ince kina wajen Hajja Kaka bana son ya gane kuna masarauta.” Nene ta d’an yi Jim don sam bata son Najeen ta tafi, sai dai Umma ta fita gaskiya tabbas idan Baffa ya koma ba su koma ba akwai matsala don haka murya a raunane ta ce “Ko dai mu taho gaba d’aya?” Umma ta girgiza kai kamar Nenen na ganinta ta ce “A’a Ai ke bai kamata ki taho ba ki yi zamanki mu ga abinda hali ya yi, idan da yiwuwar mu taho taya murna sai mu rankayo gaba d’aya…” Nene dai ta saki murmushi kawai ba tare da zuciyarta ta amince za’a zo tayata murnar ba, ba mamaki ma a mata d’aurin talala. “Faruk zai zo yau komai dare ya taho da ita, don Allah Nene ki kula kada a samu matsala.” Muryarta cike da rauni ta ce “To” ta zare wayar a kunnenta tana jin duk gangar jikinta na sanyi saboda rashin sanin madafa. Najee idanunta tsura mata tana mamakin canjawarta “Nene me ya faru?” Nenen ta d’ago tana kallonta sai ta ke ji a ranta kamar ta rabu da Najeen kenan idan suka tafi ba zasu sake waiwayarta ba, wani babban al’amarin zai faru. A sanyaye ta ce “Umma ta ce ki shirya yau Faruk zai zo ya tafi da ke gobe Baffa zai dawo kada ya dawo bai samemu ba.” Najee wani irin dum ta ji kanta ya yi, sai ta ji zuciyarta bata son rabuwa da Nenen wasu tarin k’walla suka fara karakaina akan k’uncinta. Murya a raunane ta ce “Bana son na bar ki Nene.” “Nima bana so Najee amma haka dole zamu hak’ura kada mu jawowa Umma matsala.” Najee ta yi shiru tun daga wannan maganar sai jikinsu ya yi sanyi suka zauna a d’akin ba mai cewa komai.

Fulani Saddik’a kuwa tun da lamarin ya faru ta kasa gasgata abinda idanunta suka gani, Tauraruwa a raye? Kada dai fa duk wa’dancan Umarnin da ake bata Tauraruwar ce take bata, idan haka ne me yasa ta nunawa jama’a cewa ta mutu alhali tana raye. Ta janyo wayarta tana kallon numberr da kai tsaye ake kiranta zuciyarta na sake tsinke wa idan har ta tabbata tauraruwa ce take bata umarnin tabbas akwai lauje cikin na’di. Ta kai gwauro ta kai mari cikin d’akin tana sake kiran wayar da har a lokacin ake sanar da ita a kashe take wayar, kamar lokutan baya da take yawan kiran layin baya shiga in dai ba su suka kira ta ba. Bata san sanda ta yi cilli da wayar ba cikin takaici tana bin wayar da harara kamar ita ta mata laifi.

** K’arfe hu’du Faruk ya isa Fadar suka gaisa da Bafaden nan mutuminsa mai karb’ar cin hanci. Sannan ya kira Nene ya sanar da shi zuwansa cikin masarautar. Nene hankali tashe ta dubi Najee da take zaune tsuru fuskarta a ha’de alamu sun nuna sam bata son tafiya. Dafata ta yi tana furta mu je ki yiwa Fulani sallama.

A k’aramin parlourn Fulanin suka tarar da ita. Ta zuba musu ido kawai har suka gama bayani bata dakatar da su ba, sai da ta tabbatar sun gama sannan ta ja ajiyar zuciya ta mik’e ta isa d’aki wata sark’a mai kyau ta d’auko ta gold ta mik’awa Najee tana furta “Ki gaida Mamanki kafin mu zo har gida yi musu godiya.” Najee ta amsa tana d’aga kai. Suka fice daga d’akin.

Tun daga nesa Faruk yake kallonsu dariya yake sosai ganin yarda kamannin Najee suka sauya gaba d’aya. Baki ta turo gaba ta ce “Ya Faruk bana so fa!” Ya gaisa da Nene sannan suka mata sallama tana d’aga musu hannu suka fice da motar. Hawaye ta ji yana bin k’uncinta.

Baffa ya dawo cikin k’oshin lafiya bai lura da rashin Nene ba don ko tambayar ta bai yi ba. Yana zaune yana cin alkubus da miyar taushe. Umma ta ce “Baffan Yara Najma fa ciki ne da ita” Da sauri ya d’ago kai yana kallonta kafin ya furta “Da gaske?” Umma ta d’aga masa kai “Allah ya nufa dole sai ta samu d’a da Jaheed sai dai ayi fatan Allah ya raba lafiya… sai kuma ka sanar da Jaheed d’in” Baffa ya d’aga kai yana furta “Shima yana daf da zuwa, haka ya ce min In sha Allah.” Ya wanke hannunsa yana dawowa ya d’au cup d’in zob’on yana sha kafin ya kalli cikin idon Umma ya ce “Ina Nene kira min ita…..”
Chapter 3 · 0% Book details