Sashe 40
Kudirar Allah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yana fita parlourn ya ci sa’a ba kowa da sauri ya fice daga gidan ya nufi motarsa bayan ya kira Jaheed ya masa sending location na asibitin ya tafi yana jin duk wata fitina da take ransa ta fara mik’ewa da gaske matarsa yake da buk’ata kwana kusa, ya ‘dan cije leb’ensa a ransa yake jin kamar ya furta NA MATAR DA KE NAJWA… sai dai yana tsoron fushin Nene, don haka ya ha’diye furucinsa kawai yana driving yana murza goshinsa lokaci guda kuma yana sakin murmushi idan ya tuna wautar Najwa.
Da k’yar ta mik’e daga gadon jin yarda abu yake bin jikinta yasa kai tsaye ta shige toilet a zatonta period take duk da ba lokacinsa ba ne, sab’anin haka wani kalar ruwa ta gani da sauri ta yamutsa fuskarta tana furta “What is this? Bari na je na tambayi Umma Allah yasa ba wani ciwo ba ne.” Sai da ta yi fitsari ta fito sannan ta nufi d’akin Umma. Suna zaune da Tauraruwa da Nene ana ta lissafin kayan Babies da ake buk’ata a siya. Ta yi sallama ta shiga fuskarta d’auke da alamar damuwa. Duk wanda yake d’akin kuma ya ji k’amshin turaren Murad a jikinta. Gaba d’aya suka kusan ha’da baki wajen furta “Lafiya Najwa?” Ganin yanayin jikinta da k’amshin da suke ji a tare da ita… Ta yi k’asa da kanta tana furta “Ba ni da lafiya..” Suka waro ido suna kallonta Tauraruwa ta mik’e ta isa kusa da ita tana dafata ta furta “Fa’da min me ya sameki?” Lumshe ido ta yi tana tuna wannan feeling na d’azu da ta ji mai mugun da’di cikin wata irin murya ta ce “Wani ruwa ne mai yauk’i ke zuba a private part d’ina kuma ba period ba ne…….
JIKAR NASHE🥳
08033748387.
[5/12, 8:57 PM] Bahaushiya👍: Da k’arfe 10:00 na safiya ya gama duk wani shirinsa ya zauna a parlourn Baffa yana jiranta tuni an turo masa flight ticket d’in su da zai kai su Abuja. Suna zaune Baffa yana sake masa nasiha a hankali yana fahimtar da shi yarda zai yi zamantakewar aure da matarsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta yi masa biyayya kuma ba tare da nuna gazawa ba ko ka’dan. “Murad mace tana son ka bata lokacinta, ka kuma zuzuta aiyukan alherinta da kyawunta ko da bata kai a zuzuta ta ba. Zata ji da’di kuma zata kambama kanta ta zata tafi duk matan duniya. Mace tana son a yaba mata ka kula da kyau a duk lokacin da kaga matarka ta d’au zafi kai ka yi k’ok’arin zama ruwan sanyi don samun daidaiton ra’ayi a tsakaninku a lokacin da ta d’au zafi idan kai kace zaka d’au naka zafin abin ba zai yi kyau ba, sai kaga an zo abu ya kai da saki. Mace tana son a gatanta a shagwab’ata koda shekarunta sun kai 70 Ka mayar da ita yarinya a kan ka, sai ka ji bakinta lumui tana kuma kurarin mijinta yafi na kowa. Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan abin k’i. Ka lura da kyau kada ka zama sakarai a wajen matarka, har ya zama bata jin maganar ka ka zama tsayayyen namiji wajen tarbiyyarta kamar Uba mahaifi ka gane?” Murad ya d’aga a ransa yana sake jinjina girma da kimar Baffan hak’ik’a Baffa nagartaccen Uba ne na nunawa a kerewa a sa’a. “Bari na turo maka ita.” Ya mik’e kansa tsaye ya shiga cikin gidan b’angaren Umma inda Najee take can tana zaune hannaye a kumatu ta zuba uban tagumi. Haka kawai take cikin tsananin fargaba fargabar da ta kasa b’uya a saman fuskarta. Baffa ya d’an zuba mata ido kafin ya saka hannu ya d’auki mayafin da ta ajiye a gefe. Bata son da shigowar Baffan ba balle har ta lura da mayafin da yake shirin yafa mata. Ji ta yi kawai ya dafa kafa’darta yana yafa mata mayafin. Murya a hankali ya ce “Tashi Najwa ki je Allah ya miki albarka duk wani alheri yana gidan aure martaba da mutuncin mace shine zama gidan Mijinta. Aljannarki kuma tana k’ark’ashin sa idan kina son samun mafi k’ololuwar daraja a cikin Aljannatan Ubangiji ki dage da yi masa biyayya ki guji sab’a masa ki guji aikata duk wani abu da zai sosai masa zuciya yanzun nan sai kiga kin zama Tauraruwa a cikin Taurari. Allah ya miki albarka…” Cikin rawar murya ta amsa ameen d’in hawaye na malala a k’uncinta kamar wadda a yanzu ne zata tafi gidan aure a karo na farko. Baffa ya bubbuga kafa’darta a hankali yana furta “Khairan In sha Allah.” Ya furta yana dank’a mata wani littafin addu’oi da Alkur’ani mai kyan gaske da carbi. “Wad’annan sune makamin yak’ar mak’iyi da mahassadi a rayuwa idan kika rik’e su a gidan aurenki zaki sha mamakin alherin Ubangiji da zai dinga bibiyar ki. A yi rik’o da nafila mafi girmansu sallahr walaha da ta tsakiyar dare..” Najwa ta d’aga kai a hankali tana mik’ewa Baffan ya saka hannu ya damk’i nata hannun suka fita waje. Har d’akin Mahmeey bai Bari ta shiga ba balle ta bawa Umma labarin Mijinta ne ya tafi da ita. Suka fita harabar gidan inda Murad da drivern gidan suke jiran su don ya dawo da motar Baffan da Murad yake hawa tunda ya zo garin.
Tunda ta fito ya zuba idanunsa a kanta yana jin duk wani bak’in cikinsa ya yaye, Allah ya gama yi masa dukkan wata ni’ima a rayuwa da ya mallaka masa Najwa a matsayin matarsa. Baya jin a duniya zai sake kallon wata mata da niyyar soyayya idan ya kalla d’in ma ba Zata kai Najwa ba a zuciyarsa. Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana furta “Alhamdulillah Hamdan katheeran bi ni’imatihi tatummussalihat…” Ya yi sauri bu’de mata k’ofar motar. Baffa ya k’araso da ita da kansa ya saka ta a cikin motar yana furta “Fi Amanillah.” Ya juya wajen Murad yana murmushi ya furta “Murad ga Amana!” Murad ya dunk’ule hannunsa yana murmushi ya furta “In sha Allah Baffanmu.” Ya juya wajen Najwa ya ce “Najwa ga Amanar Murad nan na baki..” Lumshe idonta ta yi a hankali ta kasa furta komai sai kunyar Baffan da ta kamata. Baffa ya yi murmushi ya sake furta “In sha Allah kuna cikin amincin Ubangiji sakamakon Aljannah ga duk wanda ya kyautata zamantakewarsa da d’an uwansa a cikin ku.” Ameen suka furta a hankali Najwa tana jin ruwa da iska ba mai hanata yi wa Murad biyayya ko don wannan addu’ar ta Baffa ta amsu a kanta, haka nan Murad yana jin ya zama dole ya kyautatawa Najwa ko don samun tagomashin Aljanna. Baffa yana d’aga musu hannu suka fice daga gate d’in ya saki murmushi da ajiyar zuciya a hankali ya furta Alhamdulilah. Wata siririyar k’walla da ta d’an mak’ale a idonsa ta zubo wacce na tabbata ba k’wallar komai ba ce sai ta zallar farin cikin auren da y’arsa da ya yi.
Kukan da take bata sarara ba tun Murad yana jinta yana lumshe ido alamar kukan yana tab’a ransa har ya faki idon drivern ya zura hannunsa ta bayanta murya k’asa k’asa cike da kasala ya furta “Ki yi shiru muryar kukanki na saka ni a wani condition…” Ya fa’da yana zuba narkakkun idanunsa a kanta. Harara ta b’alla masa hararar da ta saka shi sakin murmushin da bai shirya ba ya yi pointing hannunsa a kan k’irjinsa ya furta “Ni ko?” Lokaci guda ya girgiza kansa yana taune gefen leb’ensa ya furta you will explain it anjima ka’dan..” Sake kukan ta yi da k’arfi Murad ganin ba Zata yi shiru ba kawai sai ya lumshe idonsa ya fara rera mata wak’ar india a hankali wacce ake cewa Boli choriya…. shiru ta yi tana sauraran muryar tasa kamar ba shi ba wak’ar ta zauna akan bakinsa cikin Husky Voice d’insa da take jin ta har tsakiyar kai… Bata sake kukan ba saboda yanayin yarda wak’ar take bin dukkan zuciya da gab’banta sai gata da lumshe ido. Murad ya saki murmushi a hankali ya furta “My Piya…” Isarsu airport suka sallami drivern shi kuma ya ja trollynta k’arama wanda kaya ne kala biyu a cikinsu sai tarkacen underwear’s d’inta don ta kasa sakin jiki ta d’ebi kayan a tsorace take da lamarin Murad..
Tun a jirgi duk wanda ya gansu sai sun burge shi kuma kana ganinsu ka san sabbin aure ne. Murad baya jin kunya yayinda ita kuma Najwa duk abinda ya mata sai ta ji kamar k’asa ta bu’de ta shige ciki. Haka suka isa yana sake bayyana mata sirrin zuciyarsa.