← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 45

Sashe 7

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"MALEEK TOUFIQ kenan lallai kammmm yaro yarone, kuma yaro baisan wuta ba saiya taka.
lalle idan kace zaka shigo hurumin da ba naka ba kayi kuskure maleek!, kaje cennn bakin iya kar ƙasa kayaƙi miyagun mutane masu safarar mata da masu shigo da miyagun ƙwayoyi, bawai mu na cikin gariba kuma sannan gida. domin kuwa tsabbb Allura zata tono garma, dan haka katafi kayi aikin ka yaro! Muɗin dai mune ƙasar
Kuma sannan ina tausaya maka domin farashim wannan abin da kayi min, Ni kuwa zan siyeshi da farashi mafi daraja, mutumci, kima kana abu mafi soyuwa, acikin duniyar kaaaa MALEEK! hhhhhhhhhhh"

Ya shiga sheƙe wata uwar dariya ta de da cira masa hannunsa, manuniya alaman ya jinjina mashi.

Ido kawai maleek ya zubawa kashim baba, cike da baƙin ciki takaici yake kallon shi, yanaji shi kuwa, wai shin idan ma ya kashe wannan mutumin ma halak yakashe ne ko haram! Domin kuwa irin waɗan nan mutanen mahaliccin mune kawai maganin su,amma duk da haka bara yayi ɗan wani wasa ya gani.

Hakan ya sa A fusace ya miƙe tsaye ya take ƙafar kashim baba, kana kuma ya ya murza wuyan shi kanshi ya dawo bayan sa, bayan kuma ya dawo gaban sa ya shiga mutsirtsike ƙafafuwan shi, Wani irin ihun da bai shirya zuwan shi bane yake tsalawa domin kuwa a iya tsawon tarihin rayuwan sa kamo ƙuruciya kamo yanzun ba'a taɓa mai iziya irin ta yau ɗin nan ba wallahi.
Tun yana ihun iya qarfin sa har qarɓin ya qare yana kururuwar har yagaji dan kansa ya daina, Kafin kuma a haka ya sumeeé
Sakin sa maleek yayi yana huci yanajin kamar ya kashe shi ma kowa ya huta.

A fusace yafito daga cikin ɗakin da kashim baban yake, yana ƙara jadda dawa kada yaron daya yarda yau yabama kashim baba abinci yau, koda kuwa ɗigon ruwa neeeeeee....

****
Iyalan kashim baba kuwa ganin yau har kimanin sati kai biyu babu wani abinda ya biyo bayane, yasa su fawwala Allah al'amuransa.ita kuwa hussanna amarya ta haihu ta haifi kyakkyawan yaron ta domin yaron sak ita ya biyo yau satin suna...

Zaune suke a babban É—akin taron nasu kamar dai koda yaushe
Isah hasarara, alhaji atiku, isa tanbuwal, Ibrahim nera,
gaba É—aya sungama hallara, suna tattaunawa

"Nifa na gama yarda wallahi Allah É—an iskan yaron nan, shine ya É—auke kashim,
domin kuwa naga zahiri tun daga gudun tseran tsiran da muka. fafatawa dashi a Kano Allah ne kawai ya kwaceni da wannan la'ananen yaron.
Nifa tunda yashigo rayuwarmu komi yake neman ƙarasa kwaɓe mana, kullum baci gaba saici baya wai duk meye hakan neeeee?"

Da kallo suka bishi kowa yana sauraran shi, domin kuwa tabbas yayi gaskiya, tunda Allah yagama baiyana musu Maleek , suka shiga halin tsoro mara dalili mara tushe, marar iyaka koyaushe cikin tsaron kansu da kansu suke,
Alhaji Atiku daya fi kowa zuciya cikinsu ne.
yamike tsaye yanufi hanya aguje yana faÉ—in.
"Ina nikam nagaji da gafara sa banga ƙaho ba, dan haka yau koni koshi saidai ayi wacce za'ai gaba ɗayaaaaaaaaa"
Ya qarisa maganar yana harba pistol É—in dake hannunsa
garba ne yake mar magana ammah inaaaa yarigada yafice ko juyowa baiyi, ba bare yasa ran zai tsaya É—in

Cikin tsoron abinda
Ka iya faruwa yasa shi faÉ—in.

"Kasani ana dab da zaɓe Atiku! idan har kaje wurin Wannan yaro kana ganin jama'a kuwa zasu zaɓeka 'a matsayin babban Ministern su?
kenan bayan ka baiyana ma jama'ar kai ɗin babban ɗan *DABA NE* eyeeeeee?, Idan hankali ya ɓata hankalin yake naimoshi atiku"

Cakkkk kuwa ya taka birki,daga ƙarasa ficewa daga gaba ɗaya harabar gidan nasu na sirri, yana dafe da goshinsa kana kuma wannan bindigar ta hannunsa ya shiga harba ta sama, saida ya ƙarar da gaba ɗaya bullet ɗin cikin bindigar nan.

********

Gaba ɗaya shirye shiryen sauƙar al'qur'ani mai girma sukeyi, kasan cewar yau saura kwana uku takk saukar tasu. wanda ƙasa da ƙasa ne suka shirya ma wannan babbar sauƙa nasu, daga nan kuma idan anware mafiya ƙwazo a cikin su saisu tafi ƙasa mai tsarki wato Madinah.
domin ƙara ƙarfafa musulunci ƙasar *MADINA* suka shirya musu, wannan babban taro wanda za'a gwada tsakanin ƴan ƙasar mu *NIGERIAN* da kuma *MADINAH* da sauran ƙasashen duniya.

Duk wani abu mai muhimmanci daya danganci wannan sauƙa tasu ta gama killace kayanta, malam Abdullahi rano da ummeyn ta sunata samata al'barka da taya ta adda'o'in samun nasara.

Kwanci tashi babu wuya agun mai rai, yaune babban wurin taron al'QUR'AN mai girma yagama cika ya tambatsa, kowa da kowa na wajen manyan ciyamomi sarakunan gargajiya sarakunan fulani manyan ƴan siyasa manyan masu kuɗi, ƙara fanin su sune a wannan wuri.

Bayan buɗe taro da adda'a ne da wasu nasihohi masu ratsa jiki su biyo baya, ne aka fara gudanar da sauƙar tasu cikin aminci da kwanciyar hankali. haziƙan mahaddata QUR'ANIN suka fara rairo karatunansu cikin ƙyaƙyƙyawar ƙira'arsu mai ƙyau, sukaci gaba da gudanar da sauƙar tasu. sai wajajen magrib taron nasu ya tashi, sai daga baya kuma sakamakon wanɗanda suka yi na ɗaɗɗan anemesu kana'a tantance waɗanda za'ayi tafiyar dasu.

Haka taron nasu ya tashi inda kowa, yake yaba ma MARYAM ABDULLAHI RANO, don tayi karatu mai ratsa zukata da wasu littattafai na daga cikin, addinin Islama. Hakan yasa ta shiga zukatan bayin Allah sosai.

Kwanci tashi
Alhamdulillah sakamakon yafito, kuma *MARYAM ABDULLAHI RANO* tana cikin waɗanda za'ayi tafiyar da su. Su malam Abdullahi da ummey ƙwarai sunyi farin ciki matuƙa da wannan Sa'ar da ƴar su ta samu.

Bayan kwanaki biyar suka lula cennnn ƙasa mai tsarki, saida suka ƙwana suka huta sannan washe gari suka fara gudanar da taron nasu komai cikin larabci sukeyinsa wata balerabiya Anum dawood aka fara ƙira tafito cikin shiga ta alfarma ta kamilallun bayin Allah tafara raira karatun ta. Cikin zazzaƙar muryarta, Ana datso mata tambayi Cikin tsaƙiyar, al'QUR'AN mai girma tana kuwa cafewa tana bayar da amsar su daidai,lalle wannan baiwar Allah da baiwa take.

Alhamdulillah muhaÉ—u'a fejin gaba
Wllh ina ɗan wani uzirine ammafa kuyi haƙuri fejin gaba in Sha Allah zaku samu mai tsayi

By ammeyn laylah 🫶🏻*🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻*

FREE BOOK
Page 🔟

081-04-49-32-15

*Alhamdulillah forever and always*

*IDAN KASAMI DUNIYA'A HANNUNKA TOKA BITA'ASANNU DOMIN ITAÆŠIN BA MATABBATA BACE*
*RAYUWA CE WATA RANA SAI LABARI*

*SHINE RAYUWATA KUMA DUNIYA TA❤️👌🏻🫂*

*MARYAM NASEER MIRRAH ✨ GARKUWAR MUSULUNCI💪🏻*

_________Haka akaci gaba da ƙiran bayin Allah ɗaya bayan ɗaya har akazo kan *MARYAM ABDULLAHI RANO* sanye take cikin Baƙar abaya kimuno da dogon hijjabin ta har ƙasa ruwan sararin samaniya, a hankali tafara takowa cikin abinda aka tanada domin masu karatun!
cikin nutsuwa take takawa tamkar wacce batason taka ƙasar wata irin ginshira ce kwance saman kamilalliyar kyakkyawar fuskar nata.......gaba ɗaya idanuwan jama'ar gurin ne yayi mata caaaa aka ji takeyi kamar ta nutse kawai ta huta;

Gida nigeria kuwa duk wani wanda yake da alaƙa da waɗannan bayin Allah masu sauƙar hakimce suke bakin tv suna kallo, masu sauraran radio nayi

*MASARAUTAR ADAMA*
*****************

Gaba É—aya
jama'ar masarautar kowanne ɓangare suna hakimce gaban maka makan plazma ɗinsu

Dalilin *SARKI ABDULPHATA OMAR*
bai samu halartar Wannan taron sauƙar AL'QUR'ANI ba bisa wani dalilin daya riƙe shi........ *HAJIYA MARYAM*Da mai martaba sarki *ABDULPHATA OMAR* ne zaune gabansu sun zubawa plazma ɗin ɗakin nasu idanu tun farkon fara sauƙar suke gaban tv suna kallon komai har akazo kan wannan baiwar Allah.....Anum dawood cike da burgewa suke kallonta

A daidai loƙacin da aka ƙira sunan baiwar Allah *MARYAM ABDULLAHI RANO* atare zuciyoyin na mutum biyu suka buga' Alaƙaci ɗaya..

Cikin tarin nutsuwar ta taci gaba da takawa har zuwa kan ƙawataccen gurin karatun nasu!
cikin girmamawa ta amshi abin karatun haɗi da ɗage likaf ɗin nata!.... ƙyaƙyƙyawar fuskarta wanda wani irin annuri, da haiba, yake kwance saman cute face nata ya baiyana' jama'ar wajen da yawansu kasa haɗa ido suka yi da ita sakamon wani kwarjini dayayi ma fuskar nata ƙawanya ga ɗan wani irin ruwa-ruwa da ƙwayar id0n nata suka fara tarawa sanyi takeji sosae 'A jinin jikin ta
Ahaka ta gabatar da sallama!
ta gaida mutanen duk cikin harshen larabci,
fara rairo karatunta tayi cikin zazzaƙar muryarta da kuma ƙyaƙyƙyawar ƙira'arta cikin *SURATUL KHAFIH* saida taje wajajen tsakiyar kana aka gimtse ta....

Aka shiga kutso bata tambayoyi cikin juya ƙwaƙwalwar mutum da tunanin sa!!!

Amma Allah cikin ikon sa da buwarsa ta ringa bada amsoshin duk da aka ringa mata hadisai ne, sira ne, fiqhu ne, bulugul maram ne, tauhid ne, balaga ne, da dai sauran littattafan mu na addinin Islama haka aka ci gaba ta zakulo mata tambayoyi tana lashe su

Su ummey da malam Abdullahi! Dake gaban ƴar ƙaramar tv ster nasu suna kallon komai jikinsu duk yafara sanyi ganin irin tambayoyin da ake watsowa shalelen ƴar tasu

Anan cikin Masarauta kuwa 'A daidai loƙacin da aka bukaci fitar MARYAM ABDULLAHI RANO da loƙacin da ta , fito tafara tafiya suka ƙurewa tafiyar nata kallo da kuma loƙacin da ta cire likabin fuskar ta da maganar da,
tafara cikin ginshira da tarin nutsuwar nan nata mutane biyun nan suke kallon ta kurrrr
Kafin daga bisani Hajiya Maryam ta zube sumammiya ko motsi bata ƙara yiba shi kuwa mai martaba sarki Abdulphata omar duk yanayin jikin shi yaji yana sauyawa ka kuma ana cikin hakan amarya tashi ta zube 'A jikinsa summammiya

Saida kowacce ƙasa suka gabatar ta saukar tasu ne bayan sallar la'asar dab da magrib taron nasu ya tashi!...... Kana bayan sunyi sallar magrib aka kuma buƙatar ganin su!
Susu hudu

Anum dawood madinah

MARYAM ABDULLAHI RANO kano

Khadija habeeb niger

Zainab qasim Jigawa

Liyafa ta musamman aka shirya musu cikin babban masallacin birnin madinatul munaiwara

"Khadeeja Habeeb itace tazo ta hudu"

"Zainab qasim Jigawa ta uku

Anum dawood ta biyu

*MARYAM ABDULLAHI RANO*, Kano

Itace wacce ta lashe wannan gasar domin su, sauran dukka ,ana musu gyara ko waccensu anci gyaranta!!!

Da wani irin maÉ—aukakin mamaki farin ciki gaba É—aya duk wani ahlin É—an Nigeria murna sukeyi gani suke kamar ba gaskeba; malam isyaku el-yakub kuwa ji yake tamkar ya goya *JADDAH*, A gadan bayansa yayi ta juyi da ita tsabar farin cikin daya gama kewashi,
Chapter 7 · 0% Book details