← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 45

Sashe 10

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali take masa jawabin abinda yafarun kafin zuwan nasa har kwanciyar asbitin da tayi da yanda aka tattauna akan maganar baki ɗaya s0 dan haka ya kwantar da hankalinsa loƙaci kawai suke jirah
In Sha Allah

Ya fashimta ya Kuma gamsu da dukkan wani bayani da ƙaramar momin nashi tayi mai kuma shima zai ci gaba da roƙon Allah ya sassauta musu ya warware musu komi cikin aminchinsa

Daga nan ya fita ' a ɗakin nata, hakan yayi daidai da fitowar mahaifiyar sa hajiya laura, itama daga nata ɓangaren
wata bahaguwar hararar da ta watsa mishi ne yasa shi saurin sauƙe kansa ƙass

Itafa tagaji da wannan likimo ɗin da takeyi akan matar da dukk duniya tanajin babu wanda tafi tsana sama da ita, matar da indai har zata ganta saitaji ƙirjinta ya buga da wani irin tsalle

to me yasa hakan?

Kawai tana ga zata fito mata'a asalinta na zahiri bawai wanda ta ara ta azawa kanta baaaaaa tagaji shekaru É—aÉ—É—ai har shekaru ashirin da tara amma kullum cikin sakin fuska da hada hada suke mata

Dan haka tagaji da haɗa mata tuggu ta ƙasa kawai zata fara fitoma mata a baiyane neee ta faɗi hakan tana sauƙe ajiyar zuciya kafin ta gallama ƙofar ɗakin nata harara, ta wuce zuwa cikin harabar wajen masarautar tanajin zuciyar ta tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito

Cikin yanayi na razana, ƙiɗima, tashin hankali, take tafiyar a dokar dajin Allah subhanahu wata'ala cikin tafiya ta rashin tsoro take tunkarar dajin haiƙan
Abaya ce baka wulik a jikinta ƙafarta, hannayenta, duk ta rufe su da safa

Saman fuskar ta kuwa liƙab ne gaba ɗaya babu inda kake gani a cikin jikinta

Gaban wata ƙatuwar bishiyar kuka taja ta tsaya tana wasu surkulle masu kama da, dalassumai

Cikin wani irin ihuuu da ƙara ji wani ƙaton boka ya baiyana gabanta yana kururuwa iya ƙarfinsa da wata irin murya tasa mara daɗin ji, ya fara magana

Kamar haka

"Tabbas wannan karon zaiyi AUREN"

kuma harda rabo a tsakanin su

Sannan idan har kikayi ƙoƙarin dakatar da hakan to kuwa tabbas zaki mutu LUBNA

kuma tabbas sannan inada da tabbacin babu wani gurin boka ko malamin da zai iya miki wannan aiki akansu tunda nakasa

Nasan kina tafe neeee akan zancen Auren MALEEK

Cikin wani yanayi marar daÉ—i jin mai kama da tsafi yanayin lubnan yasau ya tana zubar da hawayen jini

Tace Kasani ba yau ba, ba jiya, ba shekaran jiya ba nake musu aiki akansu shida tsinanniyar uwar tasa

Amma wannan karon tashi É—aya kace aikina bazaici
Boka TUNKAS kasan wannan aikin daidai yake da cikar maradina boka dan haka zandakar da hakan !!
Kota halin yayane kamar yadda nasaba

*FITAR 'AZABA TAMKAR FITAR CIWO HAKA YAKE*

*DAN HAKA DOLE WAJEN GUSHE WARSA*

*DOLE SAI DA WATA AZABAR BOKA!!!*

Kafin ya ankare tuni harda ɓacewa ganinsa ɓatttt

Wata iriyar dariya ya kuma kecewa da ita yana mata kallon tsirara domin kuwa ai shine ginshiƙin
Ita kuma tsiro

Shima ɓattt ya bace a wurin yana barin wani baƙin hayaƙi a gurin

******** Kwanci tashi hasarar mai rai zancen auren nan sai ƙara bazuwa yake yi....loƙacin da Hajiya talatu nera taji wannan zancen kuwa saitaji kamar an soka mata kibiya ne a ƙirjinta

Ta cennnn ƙasa kuwa wasu irin shirye shirye ne sarki maleek ibn suffyan yake wanda babu wanda, ya isa yace ga asalin abinda yake ma shirin!.....yanaji kamar ya mats0 da wannan auren domin cikar maradinsa

Tamkar abin wasa haka gidan su malam Abdullahi rano, suma suka fara shirin bikin aurar da Æ´ar tasu..... Jaddah kuwa hankalin ta idan yayi dubu toya rida, daya tashi domin ganin tabbas da gaske shirin bikin tane ake

Ummeyn ta tashiga gyaran Æ´ar tata tako ta inaaaaaa

____ Su alhaji atiku kuwa sun riga sun seta wata ƙayataccir diner da tashin hankali a zuciyar maleek taufiq
Wanda yayi daidai da ranan É—aurin auren saaaa

Cikin yanayi na cikon wani cikar muradi tashi addu'a babu dare babu rana

*Kuyi haƙuri yau TYPING kaɗan ne ba yawa*

Nerth PAGE in Sha Allah

*By Ammey laylah 🫶🏻💔**🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*

FREE BOOK
Page 1️⃣4️⃣

081-04-49-32-15

*RAYUWA TAƘAITACCIYA CE, KARKA CIKATA DA DAMUWA.*

*HAƘURI DA JURIYA SUNE SILAR CIKAR KOWANE BURI*

______- Cikin yanayi na cikon wani cikar muradi nata, ta shiga ambaton sunayen Allah babu dare babu rana.

Haka ma na hannun damar nata wato Sufyan Abdulphata ba'a barshi a baya ba wajen taya Little momman nashi adda'o'i,wajen sauƙaƙa musu wannan lamari

****Cikin jimami da fargaba da take ciki take tafiya cikin sanyin jiki haka kawai takejin kar ba kalau ba kamar wani abu gagaru na shirin faruwa da rayuwanta, saidai tana ƙoƙari wajen danne hakan, dalilin kada mahaifan nata susan halin da take ciki,
A hankali take taka ƙasa kamar wacce take tausayinta ko kuma irin anyi mata dolen nan?

Cikin sanyi murya tayi sallama a cikin gidan nasu wanda yafara tara Æ´an uwansu na rano, da suka fara zuwa domin gudanar da biki

Ko wannensu ɗauke da tarin farin ciki maɗaukaki suke amsa sallamar nata,har wasu daga cikin su na tsokanarta amayar baƙya laifi koda kuwa kin kashe ɗan masu gida,gaidasu tashiga cikin ladabi hadi da tarin nutsuwarta

___Gidan su MALEEK TAUFIQ kuwa cike da tarin farin ciki marar ɓoyuwa ammeyn nashi take saukar bakin nata, wanda take ganin kamar ' a mafarki wai yau waɗannan jama'ar sun tarune domin bikin gudan jinin MALEEK

Ɓangaren hajiya Lubna kuwa idan hankalin ta yayi dubu toya gama tashin kanta,domin ganin abin take kamar madubin mafarkinta MALEEK maleek daiiii maleek ɗin ta shine yau harya samu zarrar fitar da matar aure, to shin ina asirin da tayi mai?
na tsanar mata gaba É—ayansu kai ita da s0ma tayi tarabashi shida munafukar uwarsa saidai hakan ya gagara
Badan tas0 ba ta ƙyalesu a haka suke mu'amulatar junansu a duniya idan da matar dafi tsana to kuwa yabi bayan aysha galadima ta auna kasheta ita da yaran nata saidai hakan ya gagara, kuma yasan hakan baya rasa nasaba da wancan shegen uban nata wato sarki maleek ibn suffyan domin tsaye yake akan duk wani abinda, ya danganci ahalinsa.da tarin adda'o'in kariya daga sharrin masharranta

Cikin tsananin azabar dake tsikarin tsakiyar ƙirjinta tafi to daga bayin ɗakin nata bayan ya dauraye idanunta

Sumayya, yusrah ihsan,jamila Sune ta tarar a tsakar parlon nata sai autarta nabeelah wacce take jingine da jikin Aunty Sumayya tana buga game 'a wayanta fuskarta ta ƙara saki tana duban yaran nata cikin tsananin ƙaunar ƴaƴan nata.....gaisheta suka shiga yi cikin girmamawa amsasu tayi har tana tambar yaransu domin dukkanin su ko wacce yana ɗakin mijinta iya autar ta ce nabeelah a gabanta...

Ita kuwa hajiya talatu nera barin ma ƙasar tayi gaba ɗaya tace baza'yi wannan abin baƙin ciki da itabaaaa.....

Dan haka maaa tabar ƙasar baki ɗayanta ta lula ƙasar masu jajayen kunne ita da yaranta sai kasar swinzlan

Yau takamaa 21 ga watan 5 Na june wanda yayi daidai da ranar daurin auren MALEEK TAUFIQ da amaryarsa MARYAM ABDULLAHI RANO

A babban filin harabar masarautar wanda matakan tsaro na manyan sojoji sukawa Masarautar ƙawanya da tarin tsaro mai tsanani

Sha biyu daidai aka É—aura auren *MALEEK TAUFIQ*
DA
Amaryarsa
*MARYAM ABDULLAHI RANO*
Akan sadaki dubu É—ari biyar lakadan ba ajaran ba wanda mangan shugabanni Æ´an siyasa tattawa masu tattako suka shaida....

Saidai wani abin mamaki sama ƙasa anrasa ango anrasa dalilin sa murmushi kawai sarki maleek ibn suffyan yayi domin shi yasan abinda yasa ya gudarma ɗaurin auren nasa a loƙacin da jama'a suka rigada sukawa Masarautar ƙawanya a loƙacin ne shi kuma MALEEK TAUFIQ yasa daman shiga cikin asalin fadar sarki maleek ibn suffyan kakan nashi, wanda yarufe fuskarsa da glas da p-carp , wannan dalili yasa babu wanda yagane asalin wanene sai idan yaje gurin masu tsaron ƙofa ne yake dage p-carp ɗin sa

A zaune ya tadda Sarki maleek ibn suffyan wanda ya kishingiɗe a saman ƙayatacciyar kujerar SARAUTAR SA!..... Shima kujerar yaja yazauna yana fuskantar kakan nasa

haɗi da haɗe ƙyaƙyƙhawar fuskarsa.
sammm babu wani annuri dayai saura ' a saman fuskar nashi cikin magana mai kamada bada umarni yafarawa kakan nashi magana

"Yaka mata kayi gaggawar baza wannan dandazon tarin jama'ar daka tara"

"Tunda na fashimci kai kawai takurawa mutum ka iya kuma shine aikin"

"Dan haka tun wuri kasan yadda zakayi da tarin jama'ar ka"

"Ko kasan yadda zakayi da ita yarinyar domin bani zaka É—aurama baaaaa"

Yana gama faÉ—ar maganar dake ransa ya fice a fusace fuuuuuuuuu saikace wata kububuwa
Yana fitowa ya faÉ—a matar shi yajata da mugun gudu na masifa

Wani murmushin sarki maleek ibn suffyan yayi yana shafa saman fuskarsa, da sammm bata da maraba data É—iyarsa little daughtern shi aysha

Alhaji TAUFIQ ne ya ƙara s0 gurin mai martaba sarki maleek yana bashi hannu musaba sukayi yana ƙara masa godiya bisa hidima da ɗauwanir jikin nasa maraji...

Shi kuwa maleek gudu yake kamar zai tashi sama

Kamar a mafarki kamar almara yaga wata ƙatuwar mota tazo tasha gaban sa!, Kuma cikin S0n halaka abinda yake cikin motar dama motar kanta; wannan ƙatuwar mota ta iyo kanshi gadan gadan

Cikin wani irin sauri da jajircewa ta ƙwararrun sojoji ya wani sha kwana ta kan motar nashi!! yana zaro bindigar sa, dake maƙale jikin wando jikin sa

Dai-dai tayar motar ya É—a na harbi ji kake tushh, tayar motar ya fashe

Su kuwa mutanen cikin motar ganin an harbi tayar sune yasasu fito da nasu muggan makaman nan suka, fara musayar wuta, a tsakanin su

*******

Ganin hakan bazai kaisu bane yasasu fitowa suka tunkaro motar maleek É—in duk kuwa da uban harbin da yake zubawa

Tifffff sukaji harbin ya kuma tsaya kamar sauƙar ruwa da ɗaukewarsa haka abin yafaru' maleek kuwa ganin babu bullet nashi ya zubar dukka

Yasa shi dirowa daga cikin motar nashi, shima ya shiga tunkararsu.....nan aka fara kabta uban faÉ—a tsakanin Æ´an ta adda da maleek cikin baiwar da Allah ya bashi nan da nan yagama da mutanan, nan ya kamesu yashigar dasu cikin motar sa yajaaaa yayi gaba dasu!!!!!
Chapter 10 · 0% Book details