← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 45

Sashe 32

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Kwanci tashi hasarar mai rai yau kimanin watanni huÉ—u ciff kenan da komawar su MALEEK sabon gidanshi na asokoro, inda lissafin yayi daidai da watanni bakwai da aurensu kenan...zaune take É—are É—are a cinyar maleek,inda take zuba mishi shogwa akan ita fa bazata kuma shan woni maganinsun cennn ba, kawai ya barta ko ance musu dole shan maganinsun shine zai sa cikin jikinta ya RAYU.
Shi kuma gaba ɗaya ya gama susucewa akanta sai faman lallaɓar abarsa yake faman yi kamar kullum wannan dramer a zaune take, indai akan zancen shan maganin nuwanta ne.
"Haba Babe ki daure kisha mana' nasan ba hakan bane nima kawai dai sabo da q
Kirinqa jin daÉ—in jikin kinne kawai, badan wani abu ba AYUSHHH"
"Pls kisha yauma zan fita dake wurin aikin" jin ya ambaci wurin aiki ne kuma yasa ta qara gimtse fuska, "Oyo sai kawai kace min kayi missing abar s0nka abar ƙaunan IHSAN FANDALLAH!, Ba saika haɗa da kinaya ba MALEEK"
*************
Hannunta dake cikin nashi hannun ya matse da qarfin da saida ta fidda sautin azaba, "bance ki daina sak0min zancenta acikin dukka lamurana, kuma idan da ace ina s0nta ke kin isa kima kai labarine? Ehhhhhhhh kodan kinga kawai ina biye miki duk abinda ranki yakes0ne yasa kikes0n rainani?" Pls Don't talk to me about the nonsense inside my house AYSHA, if you don't want to give me a problem"
Ya faɗi hakanne kuma yana dureta ajikinsa In a crying voice ta shiga faɗin naji dan Allah kayi haƙuri kazo ka bani maganin zansha, zansha wllh ta faɗi hakan tana qoqarin riqoshi hakan yasa afusace yace mata "DON'T TOUCH ME kada ki kuskura" sai kuma kawai ya shige cikin bedroom nashi yana rufo qofar da qarfin bala'i.
Hakan yasa jaddah durƙushewa a wurin tana sakin kukan azabar sukar da zuciyarta ke mata, aduk loƙacin da zata tuna akwai wata mace guda wacce keson wasa da rayuwarsu ita da mijinta hakan yakansa taji tamkar ta zare zuciyarta tabar numfashi a doron qasar baki ɗaya.
Haka ta shiga sambatu ita kaÉ—ai "to idan kace baka s0nta! Ita zuciya ai bata da qashi wurin aikin kufa É—aya, da ita kuma ta ya ya kakes0n zuciyana ta sami salama? Idan har nace banajin kishin IHSAN É—in to wallahi nayi qarya, bayan nasan wajen aikinku É—aya da ita.
Matar da ta dubi tsabar id0na tace tanas0n MIJINA kuma saita aureka kota halin qaqa, idan kuma bata aureka ba ta rantse saita É—anÉ—ani zumarka"
"Innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un, innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un, innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un" sune kalmomin data tunga ambata loqacin da kalaman IHSAN FANDALLAH suka shiga dawo mata tsakar KANTA.
Hakan yasa batasan loƙacin data buga kan nata da jikin qarfen dining table ɗin parlourn ba, buguwar data ji kanta yayine tasa ta fasa wata uwar qarar data kusan sanya maleek haukacewa****
Dan yayi tunanin wani abune ya sameta ko yasamu cikin jikinta, hakan yasa baisan loƙacin daya taho da gudun balaki xuwa gareta ba, a kwance ya tadda da tana faman kukan ta wanda gaba ɗaya kishine yasata hakan,samm bugewar da tayi ba wata mai yawa bace kawai tsabar rakine irin nata.
Cikin tamke fuska dan karma taga damarsa ya qaraso gareta, cirota yayi daga kwancen da take kan nata ya ɗora saman cinyarsa, sai kuma yashiga share mata hawayen dake fita daga cikin idaniyarta, "me ya sa!' me yasa samm samm baki duba irin condition ɗin da kike ciki AYUSHHH" me yasa kikes0n wasa da hankali na aduk loƙacin da kike cikin daru da rigimarki Ni kuma kike jefani cikin tashin hankali? Uyummmm kodan kawai kinga na damu dake sosae har haka?" Dan Allah ki daina ki daina hakan pls na roqeqi AYSHA".
Ya haÉ—e hannayensa biyu alamun roqo.
"Baxan sakeba baxan kuma tada ma da hankalin naka ba ya MALEEKkkk kayi haƙuri na daina, amma sai inhar kace min bazaka na kulata ba" ta faɗi hakan cikin sakalci da shogoɓar daya qara zame mata jiki.
Tunda shine yake qara daure mata gindin hakan, tunda kuma tasami wannan cikin rigimar taci uban tada.
"Nayi! Nayi alqawarin AYUSH, bana qarawa kuma bana qara kulatan dama cen, ba kulatan nake ba ai! Kene baki da wayo shi yasa take amfani da rashin wayon naki take s0n kawo mana nakasu cikin rayuwan aurenmu!" Na gane na fashimta hakan YAA YAA NAA"
CIKIN tsantsar zallar soyayyar da yake mata ya miƙe da ita tsaye tare da soma tafiya da ita, xuwa bedroom nashi Cikin toilet ɗin sa ya wuce da ita****
Wanka yayo mata mai rai da lafiya, kana ya shiryata cikin riga da wando pallazo inda É—an tudun cikin nata ya bayyana kaÉ—an, daga nan kuma kitchen suka nufa. haÉ—aÉ—É—an sandwich suka haÉ—a, da lafiyayyan kunun gyaÉ—ar daya zamewa maleek tamkar rai da mutuwa, dan so goma duk shigowa saiyasha abunsa.

"Kai yasin kunun markaɗaɗɗiyar gyaɗa duniya ne, wanda baisan shiba ko baisha hhhhhhhh daɗi ya barshi ya kuma barrrr🫰🏻🫰🏻uyummmm ba magana dai kammm kawai"

Haka suka fito ɗauke da kayan kwalaminsu a tsakar parlourn suka bajeee haja dan basa da buƙatar hawa dining table, haka dai suka shashanta wannan yinin nasu cikin sakalcin da shi kuma yake biye mata.
Daga qarshe ma zuwa yamma cannn ya É—auke ta sukayi wajensu ammeynsa, ko acikin motarma hakance ta faru tace ya tsaya yasai mata wancan yasai mata wannan, ahaka dai suka samu suka qarasa, ammey tana cikin kitchen tana abincin dare suka ranbaÉ—a mata sallama, cikin tarin farin ciki take amsasu l0qacin da suka qarasa shigowa cikin parlourn fitowa tayi daga cikin kitchen É—in.
Atare shi da ita suka shiga gaidata****
Cikin annashuwar ganinsu cikin farin ciki da kwanciyar hankali take tambayar yaya jikin nata, maleek ne yayi charab ya amshe zancen daba nashi ba, "Ai wllh Ammey samm bata s0n shan magani kinganta Nan, É—axuma saida muka gama rigima sanan tasha, kuma bataji sosae don Allah kimata faÉ—a ammey!"
Tunda ya fara zuba uban wannan jawaban ammeyn da jaddah suka bishi da idanu, kafin daga bisani ita ta sadda kanta qasa tana wasa da yatsun qafarta,
"To sannu sarkin sara! FaÉ—i ba'a tambayeka ba kuma, yawasa dakai ko kaine mai jikin?"
Bakinsa ya turo mata gaba tare da ɓallama jaddan harara ganin tana masa gwalo, gwalon ta kuma yi masa hakan yasa shi ɗauki wa fil0n kujerar ammeyn ya jefa mata, tare da mata waning da idanunta, hakan yasa ta ɗan harareshi kaɗan.
Ammey da komai ke faruwa akan id0n tane kuma batare da sunsan tana ankare da su bane yasata, miqewa tsaye tare da bar musu parlourn, ta komawarta kitchen tare da ci gaba da aikinta, qiran sallar magrib ne yasa shi miqewa ita kuma tace da ammeyn tana zuwa bara taje su gaisa da mutan gidan.
Da to ammey ta amsa mata tana daga cikin kitchen, kai tsaye ɓangaren hajiya talatu nera ta fara yi, a zaune ta tadda ita ƙafar Nan ɗaya kan ɗaya sallamar ma da qar aka amsa mata, "Barka da dare momie"
"Wani sabon kilibibin kuma aka qara kwasowa? Wai momie, toni ba momienki bace kin gani kalli cann Ni momien waÉ—ancan ne" ta nuna yaranta dake zaune.
Wani irin murmushin da ita kaÉ—ai tasan ma'anar abinta tayi kana tace mata "kina bani mamaki dan hakan da tun farkon zuwa na ganewa idanuna abubuwa da yawa!, Tabbas idan har ahaka kika shimfiÉ—a rayuwar auren acikin wannan gida to tabbas, hasashena da tunani na basu bani qarya ba, tabbas anci da rabonki HAJIYA, an kuma kutsa cikin rashin wayon ki! Da rashin iya adana wayonki agunda yadace, tabbas anyi miki tura yaro rami anyi amfani da damarki an dama abubuwan da Allah ne kaÉ—ai yasan iyakar abunda aka dama É—in MOMIE;"
"Na barki lafiya 🙏amma tabbas daga yau kika iya tauna halshenki da sanin kalaman dake fita daga cikin bakin ki,
Da kuma sanin abinda zaki ka furtawa jama'a bye nayi wajen uwarr" sai kuma ta kanne mata id0 É—aya tana barin parlourn baki É—aya.
Baki sake ta fita bar Hajiya talatu nera, dan zata iya rantse wa tunda uwarta ta sunkuya ta haifeta, ba'a taɓa jifanta da kalamai munana irin waɗannan ba, kai koda kwatankwacin hakan ba'a taɓa ba, amma sai gashi yau ƴar cikinta ta faɗa mata maganar data gadama.
Kai tsaye ɓangaren hajiya LUBNA tayi, tana zaune tana latsa wayar dake hannunta qirar iPhone 7, cikin zallar bariki da iya taku ta faɗaɗa fara'ar dake kwance saman fuskarta, "A ahhhh yau kuma amaryarmu ce agidan barka da xuwa ƴata! Ƙaraso ki zauna tana nuna mata kusa da inda take zaune, cikin tafita sanin mai duniyar take a ciki itama tazo ta zauna ta hakimce akan kujerar data mata nunin.
Tashi tayi tana faÉ—in " bara na kawo miki abin kwalam danku wani sa'in masu cikin Nan kwaÉ—ayi gareku"
Ta ƙasan ido ta shiga binta da kallon baki da hankali LUBNA " Atafin hannuna kike tarrr nake ganinki"
Ahaka ayadda take ta dawo ta tadda ita****"yauwa gashi lemun kwakwane da sanyinsa É—axun nan nahaÉ—ama abbanku dake yana gari yau"
Amsa tayi tana faɗin yawwa mommah Naaaaa shiyasa nake ƙaunarki bani amsa tayi ta ajje a gefe, Nan suka shiga fira, kafin tace mata ita salla zatayi.
Dadduma ta shimfiÉ—a mata ita kuma tayi bayin dake cikin parlourn dan É—auro alwula, fitowa tayi tahau kan daddumar tare da tada fara sallar, tana idarwa maleek na shigowa parlourn, cikin murmushin Nan nata kamar koda yaushe ta shiga faÉ—in "id0n ka kenan my S0N yanxun ganinka sai an ciki form"
Murmushi kawai yayi tare da shafa sumar kansa yana faÉ—in "wallahi Mommah abubuwan ne sai ahankali**
"Ga ayyukan da suka tiso miki Ni agaba!"

"Ayya sannu my S0N komai zai wuce wata rana sai labari"
Chapter 32 · 0% Book details