← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 45

Sashe 13

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsakiyar compound É—in gidansu yayi parking motar, wanda Ya É—auki sama da 8 minute bai fito daga cikin motar ba.

Sanin yaga daidaita parking motar ne yasa shi ɗauke hannun sa akan steering motar, ɗan jingina bayan sa da jikin kujerar motar yayi, tare da fesar da iska me zafi ta bakinsa, yana lulawa duniyar tunani, tabbas dole ne yanxun ya ƙarayin taka tsantsan wajen fuskantar sauyin yanayin sabuwar rayuwar daya tsinci kansa cikinta,

Ahaka ya fito a motar nashi! yana nufar ɓangaren mahaifiyarsa Hajiya Aysha galadima... A zaune ya tadda ta da littafin rabba na arba'in a hannun ta tana dubawa, da sallama yashi ga yana zama kusa da ita.
Tare da zubawa mahaifiyar tashi! idanu kamar mai shirin gano wani abu a jikin nata...

*"BABANA"* ammeyn taƙi rayi sunan shi bayan ta kammala adda'o'in nata,
Cikin tarin nutsuwar data zame masa jiki, yashi ga gaida ammeyn nashi' abubuwa masu tarin yawa da kuma muhimmanci suka tattauna da mahaifiyar tashi, kafin kuma yayi mata saida safe...

Ba tare daya sake cewa komai ba yanufi babban ginin benen dake tsakiyar compound ɗin gidansu, wanda Nan ne kuma zai sada sa da nasa ɓangaren, kai tsaye yanufi ɓangaren nashi cikin tafiyar zaratan mazan da idan suna yinta sai ƙasa ta amsa,

A hankali ya murɗa handle ɗin kofar falon ya shiga, zuwa loƙacin babu kowa a falon: sai dinner daya gani a jere akan dining table, wanda dama yasan yana ɗaya daga cikin aikin baby doll ɗin nashi cikin tafiyar sassarfa ya ƙarasa gaban ɗakinsa yana tura ƙofar babban falon nashi..

daddaɗan kamshin da kuma sanyin easyn daya bigeshi ne ya kuma cakuɗa masa tunanin sa nan take cikin wani irin yanayin daya tashi dashi ya sa shi zubewa kan ƙafafun sa yana sakin wata iriyar ajiyar zuciya!

Yafi ƙarfin mintuna goma a wurin kafin kuma yasa ma damar jan ƙafafun sa yanufi toilet, A daddafe yayo wanka ya zira jallabiya falon yanufa, kai tsaye wurin abincin yanufa kaɗan yaɗanci sabo da marar sa dake wani irin azababben ciwo ko ƙofar ɗakin jadda bai kalla ba ya shige ɗakin sa haɗi da jan ƙofar yana rufe wa

__________________

A hankali yake ware idanunsa wanda suka yi jajur dasu, hannu yasa yana dafe kansa, dake Sara masa kaɗan kaɗan , hakanan gaba ɗaya duk bayajin ƙarfi a jikinsa, wanda hakan kuma baya rasa nasaba da ƙarfin maganin daya sha daren jiya , wanda ko sallar asuba ma daƙar yatashi yayi.....cije jajayen laɓɓan yayi cikin ɗan kuzarin daya saura ajikinsa ya sauƙo daga saman gadon nashi..

***Kai tsaye yanufi toilet, tundaga bakin toilet ɗin yasoma rage kayan dake jikinsa, kafin ya faɗa bayin nasa, yana sakarwa kansa shower lumshe luhu luhu eye nashi yayi yana sakin ƙyaƙyƙyawar ajiyar zuciya, wanda hakan ne yasa shi ɗan jin relief.

A haka ya kwashi sama da 15 minutes yana tsaye ruwa na dukan jikinsa, ahaka dai yayi wankan koda ya fito daga toilet É—in towel ne É—aure a waist É—in sa, gaba É—aya jikinsa É—auke yake da damshim ruwa, yayinda itama lafiyayyar sumar kansa tayi lub, itama hankali take É—an digar da ruwa.

Wani mini towel ya É—auka wanda dashi ya goge kai da kuma jikinsa

Wani tsadadden kuma fitinannen body lotion me ƙamshim gaske ya shiga shafa wa lallausar fatar jikin sa, gaban drawer ɗin sa ya ƙarasa wanda ke jere da kayansa makil; ɓangaren ƙana nan kayansa ya buɗe ya ciro riga da wandon track suit masu masifar ƙyau da tsada, koda yasanya kayan a jikin sa ba ƙaramin ƙyau suka masa ba haɗuwarsa da kwarjinin sa sun sake baiyana , gashin kansa kuwa sai shining yake domin yasha mayuka masu ƙyau da tsada... Wasu white shoes yasanya a ƙafafun sa sannan ya debi wayoyinsa da kuma wata black bag yafice a ɗakin,

A zaune ya tadda ta tana breakfast da wani irin azababben kallo yabita mai kama da zaki sani É—in nan

"Good Morning sir." Ta faÉ—a cikin siririyar Muryar ta ko inda take bai kuma kalla ba a gurguje ya zauna, yayi break É—in ma kafin cikin azama ya fice a falon baki É—aya, kai tsaye compound É—in gidan yanufa,....

Soldiers ɗin sa dake zazzaune ne suka mimmike suna ƙamewa ogan nasu ,

joy ne cikin hanzari ya buɗe wa maleek ɗin murfin motar dazai shiga cikin isa da kuma taƙama ya shiga cikin motar yana lallatsa wayar dake hannun sa ƙirar iPhone 12 promax

Cikin 40 minutes suka ƙarisa babbar headquarters Abuja , cikin yanayin na sanin takan aikinsa yanufi ofishin sa kai tsaye, kan ɗaya daga cikin kujerun ofishin nasa ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya ƙan ɗaya, anan yaci gaba da gudanar da sauran ayyukan sa cikin kwanciyar hankali,

__________________

A ɗaya ɓangaren kuwa anata shirye shiryen zaɓe sabo da yana gab da gaba towa, yayinda wasu daga cikin su ɗauki manya manyan alwasuka na ganin bayan *LIEUTENANT GENERAL MALEEK TAUFIQ*

Saidai kashhhh

Wannan maganar da ƴan azanci sukance kowa ya *ƘONA RUNBUNSA* yasan inda *TOKA TAKE TSADA* to kamar haka abin yake ga LIEUTENANT GENERAL MALEEK taufiq, Shima a wannan karon ashirye yake tsabb domin fuskantar su gaba da gaba, a gwabza *YAƘI*

Can kuma idan muka koma cikin gidansu maleek taufiq hajiya lubna itama ta shirya tsabb domin tarwatsa rayuwar Hajiya Aysha galadima gaba É—aya.

Ɓangaren Hajiya talatu nera kuwa itama akwai wasu kudirorin dake ƙasan ranta

*** Cikin tafiyar ta mai kama da yanga take tunkarar ɓangaren surukuwar nata, gabbb taji an wani irin mangajeta, saida tayi taga taga kamar zata kai ƙasa sai kuma cikin zafin nama tayi wani irin juyi tana kuwa juyowa ta ɗauke husna da wani azababben marin daya kusan zauta duniya da tunanin husna na wucin gadi

Cikin tsabar fitsara da rashin kunya ta dubi *JADDAH* tana Binta da kallon ƙasa da sama, wani wawan kallo da jaddah ta wurgawa husna ne yasata sakin trolling dake hannun ta babu shiri, tana fashewa da kuka kafin kuma ta ruga a guje zuwa ɓangaren mahaifiyar ta hajiya talatu nera tana risga kuka

Ita kuma jaddah da tayi niyar zuwa wajen ammey yasa ta koma nata ɓangaren tana jin wata irin tafasar zuciya da kuna

Hajiya talatu tana zaune gaban makekiyar plasma ɗin ta tana kallon tashar arewa 24 ce tayi saurin miƙewa tsaye, tana nufar ƴar lelen nata wacce gama wayar su kenan bayan sauƙar ta, a jirgi ta dawo daga wurin karatun ta daga ƙasar America!¡!

Cikin kiɗima Hajiya talatu nera ta kamo hannun ƴar lelen nata tana zaunar da ita kusa da inda take zaune, tana faɗin wanda shegen ne kuma ya taɓamin ke daga shigowar ki ƙasar cikin sheshsheƙar kuka take faɗin momi bansan ko wa ce ce ba momi amma sainake ga kamar matar bro wacce kika tura min pisc ɗin ta ta Whatsapp fa momi;

Cikin wani irin wutar bala'i take cin Hajiya talatu nera tace

bantan ubancan

ita É—in Æ´ar uban waye

ubanta waye a Nigeria da har tasama *ZARRAR DUKAN KI*

Tana gaba faÉ—ar haka fuuuuuuuuu ta fice a falon baki É—aya

Tana mai nufarrrrrr

To be continued in Sha Allah

Xuwa safe

Kuhuta da wannan
Masoya yanxune asalin wasan zai fara a shafi na gaba

🙃🙃🙃 Akwai Tarin cukurku ɗaɗɗiyar Cakwakiya a gaba

*Ƙaddara ƙaddara wata abacee dake dan ƙare a jini da ƙuma ɓargon ko wanne bawa*

*Kuma kowa akwai irin tashi ƙaddara domin rubutaccen al'ƙalamine tundaga rabbil izzati*

*Ko wanne bawa ta nashi kalan ƙaddarar manne a ƙirjinsa*

*Idan har kaga ƙaddarar wani ƙada kayi ma tashi ƙaddsarar dariya domin kai ɗin baka san ya taka zata kasance ba🤗*

*Dan haka ƙaddarar MALEEK da kuma JADDAH a manne take a jinin jikin ko wannen su kuma akwai wani tarin kalubalen da zasu fuskanta nan gaba*

*Rai da rashin su a manne yake a cikin ƙirjin ko wannensu tare da wata iriyar ZAZZAFAR S0YAYYA💔❤‍🔥 da ban al'ajabi da kuma burgewa, mai tafe da tausayawa juna sadaukarwa CAPTAIN IHSAN itama da nata kudirin duk Acikin SOYAYYAR MALEEK da JADDAH**🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*

{👉MAGANIN ZOMON BANA👈}

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*

FREE BOOK
Page 1️⃣8️⃣&1️⃣9️⃣

081-04-49-32-15

_____ Tana mai nufar palon ammey kai tsaye, tana zaune baiwar Allah ta ɗaura kan ummita asaman cinyarta tana shaluma tsakiyar kanta zuwa keyarta, ahakan barci yayi awon gaba da ita,....sai kawai ji tayi an wani irin turo ƙofar palon nata da ƙarfin gaske ,ummita dake barcice tayi saurin tashi zaune tana mirtsike idanunta..

Ko sallama batayi ba, tafara zubawa ammey ruwan bala'in dake famar sukar zuciyarta, ci kanki ammeyn batake mata ba...saida tayi mai isarta kana ta fuce daga palon nata bayan ta barwã ammeyn manyan kashedu game da surukuwar tata!¡!

Ita kuwa JADDAH tana zuwa palon nata ta zube kan É—aya daga kujerun palon tana sakin ajiyar zuciya, idanunta da sukayi raurau suka ciko da hawaye ta lumshe, ji tayi gaba É—aya zuciyarta ta karye, da wannan al'amari na sabuwar rayuwar data tsinci kanta a ciki, harse zuwa yaushe zata fara farin ciki nekammm
Ita? Gaba ɗaya rayuwa neman juyin waina takeyi ƙoƙarin yi da ita!

Tunda ta shigo wannan gidan gaba É—aya al'amura suke naiman juye mata, a wurin ammey ne kaÉ—ai take samun duk wani farin cikin rayuwa tun farkon shigowar ta gidan sai kuwa abbie,

A yanxun bata buƙatar komai domin brain ɗin ta gab take da juyewa, wanda hakane kuma yayi sanadiyar hautsinewar tunanin ta....

Bataji duk uban sallamar da MALEEK ɗin ke faman yiba, kansa ya sawo cikin tsakiyar palon, ganinta kwance tayi irin kwanciyar Nan ta rub da cikine yasa shi tunanin koba ƙalau ba dammm yaji zuciyarsa ta wani irin buga da ƙarfin gaske,
A sukwane ya ƙaraso gare ta haɗi da birkitota ta faɗa saman jikinsa, cikin kiɗima haɗi da zallar MURADI da kuma FATAN abinda zuciya ke tsananin ƙauna amma taurin kai haɗi da kuma ƙaryata zuciya yaƙi aminta da hakan;

Yake faman jijjaga ta haÉ—i da É—ago saman fuskarta, ganin hawaye kwance saman fuskar nata yasa shi faÉ—in "MENENE meya sameki haka ?"

Cikin Muryar kukan datake yi ne ta furta

"please ka barni"

Cikin wata zallar kiɗimar daya sama kansa a cikin ta ya ƙara birkitota jikinsa, yana ɗaura kanta saman cinyarsa ya ƙara furta "please keda waye?"
"Minene yake damu ki?"
Chapter 13 · 0% Book details