← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 45

Sashe 6

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin motocine guda uku na sojoji kuma yasa kasu tsayawa cirko-cirko.
Kowa zuciyarsa yanajin babu daÉ—i da ganin waÉ—annan motocin,
Joy ne ya fito daga cikin motar yana buɗe gidan baya, *JADDAH* ce ta fito daga cikin motar tana tsurawa mahaifan nata ido, da kuma tilon ƙawar tata basma.
Babu wata-wata basma ta taho, A guje tana rungume jaddah haɗi da sakin wani irin sheshsheƙar kuka, ita ma jaddan ƙara rungume wa basman tayi tana sakin nata kukan itama.

A matuƙar ruɗe take faɗin.
"What happened to you? I like Mickey, Who took you from us?"

Duka cikin kuka take tambayar jadderhn.

Maganar joy ce ta dawo dasu hayyacin su, yanawa su malam bayanin komi kamar yadda ogan nasu ya buƙata, ga iyayen *trouble maker* ɗin nashi. sunan daya laƙa mata kenan a cikin zuciyarsa dukk kuwa da cewa bai gama sanin asalin wacece ita ɗin ba. amma har yasama ikon manna mata wannnan suna haka.

Godiya sosai Malam Abdullahi yawa su joy, tare da qara gode musu kan dawo musu da jadderhn su da sukayi, cikin amincin Ubangiji.

Cikin gidan na Malam Abdullahi rano suka shiga bayan gama jawaban joy É—in

Sukuma suka ƙarama motocin su Mai A *360* suka bar anguwar

Maleek kafin dogarawan gidan su ankare dashi yayi saurin buɗe murfin motar nashi, ya fito da wani mugun sauri irin nasu na *SOLDIER'S* yayi wuf ya ɓacewa ganin su.
Domin shi A duniya ya tsani wannan masifar kururuwar tasu cennnn ta wata aba SARAUTA.
Amma fa acewar maleek aha.

Ɓangaren Hajiya Rabi'atou *Fulani* yayi, wato mahaifiyar ammeyn sa kenan.
Baiwar Allah tana kishin giɗe, gabanta kuwa ƙaton basket ne dammm ta kayan breakfast haɗi da kayan lambu iri iri,

Sallamar da yayine yasata saurin kallon bakin ƙofar shigowar, ganin dai da gaske na hannun daman nata ne yasata sakin wani tattasan murmushi tana faɗin

"MIJIN ƙaraso mana"

Hannuwansa zube cikin aljihun zilekar jikin sa, ya kutso kansa cikin wargajejen forlourn nata, ƙarewa komai dake jikin parlourn kallon yayi, cikin qanqanin loƙaci ya gama sanin duk abinda yake a cikin parlourn. kakar tashi aƙallah idan dai har ba mantawa yayi ba yau kusan kimanin shekaru biyu rabon shi da kakar tashi.

"MIJIN"
ta sake faɗa tana daidaita zamanta ƙarasowa yayi yana zubewa cikin garun ɗakin nata.
Amin tacciyar hadimar ta Asiya ta kwalawa ƙira, gabanta ta zube tana faɗin gani uwar ɗakina uwar marayu,

"samo wasu fulatan ki shiryama maleek abun karin ku mallo"

Abubuwan bukata na karin kuwa ta haÉ—a masa, tana kaiwa gaban sa haÉ—i da gaida shi,
ko arzikin kallo bata samu bare tasa ran zai amsa gaisuwar nata, hakan yasa É—iyam ta fice tabar musu parlourn.

suna gaisawa domin saida ya ɗiba loƙuta kafin itama grenny ɗin nashi ya gaidatan, ita kuwa dama indai halin maleek ne tariga da gama haddarsu tsabbbb.
Wani loƙacin takanji wannan da ace shine ɗan sarkin ma ba uwar sa wallahi da ba'asan abinda zaiyi ba!
Domin kuwa tariga ta sani jini *SARAUTAR* dake jikin mahaifiyar sane yake yawo A cikin jinin jikin maleek É—in.

Bai kuma bi ta kanta ba haka, ya shiga lodama cikin sa abinci. Don dama rabonsa da abincin tun jiya da yamma.

Bayan ya kammala breakfast nashi, ya miqe A doguwar kujerar parlourn, Nan kuwa kyakkyawan barci yayi awon gaba dashi.

*Bayan kwana uku*

Maleek ya koma gida ABUJA, sabo da ci gaba da bibiyar cese É—in nan nashi na kashim baba

Zaune yake gaban wani mutum da yake ɗaɗɗaure da manyan igiyoyi, kai da ganin mutumin kasan A jigace yake gashi kuma babban mutum, dan Aƙalla zai iya kaiwa shekaru sittin da ɗori, jikin sa duk yawani cakuye fatar ta yamushe sosae.
Yau kimanin sati kai biyu kenan da kawo shi nan gurin, kullum sau biyu ake bashi abinc,
A rana safe yamma
Yunwa duk tabi ta cinye mashi Æ´a Æ´an hanji,
Gashi waɗannan shegun yaran masu kama da kafuran farko, ya siyesu da makudan ƙudade ma sunƙi sakinsa,Sunce sakin sa tamkar mutuwar suce agaresu su kuma
Gashi ogan nasu yaƙi zuwa.

Cikin takun nan nasa yake tunkarar É—akin.
Yana zuwa ya daki qofar shiga É—akin.
Wata kujera ya fara zuwa gaban mutumin.
P-carp sun glasses ɗin daya ɓoye baiyanuwar ainihin fuskar sa kai tsaye ne ya cire glas ɗin.haɗi da zare p-carp ɗin ma
wani irin kwalalo idanuwa da Kashim baba yayine yasa shi sakin wani irin cool smile, yana É—aga mishi gira É—aya alamar yadai ka tsorata ne??

Cikin zallar tsagwaron mamaki Kashim baba ya shiga.
Nunashi da hannuwansa yana faÉ—in.
"maleek! Maleek!! Maleek!!!, kai ne, kai ne kasa akayi kiddnapping ɗina tsayon wannan loƙacin?, Ai kuwa ka tabbatar sunan ka GAWA da zarar na fita A gurin nan.
Sannan ka tabbata baka ƙara taɓa min ahalina ba ko ɗaya?"

Duk Kashim baba ne mai wannan maganar batare daya bari ya shaqi koda numfashi bane.

*************

Cikin zallar nuna isa, da nuna ya idan yace.

"dan kuma na taɓa ma ahalin naka ya zakayi dani?, ko yanxun ma zaka sa.
A kasheni kamar yadda kuka saba kamar wancen loqacin! kaida magoya bayan ka akan zalumci"
maleek ya faÉ—a yana nunashi da bindiga

Cikin wani irin tsananin tsoro, tashin hankali Kashim baba yake duban maleek, cikin zallar nuna bai girgiza ba ne yasa shi faÉ—in.
"Wannan karon ni da hannuwana zan sheƙe ka maleek!, wallahi nayi wannan alƙawarin saina kasheka da hannuwana maleek toufiq"
Cewar Kashim baba da yake jin tamkar ya shaqo wuyan maleek É—in.

Wata iriyar dariya dashi kansa maleek ɗin baisan zata zo masa ba ya sheƙe da ita.
Yana tafa hannuwansa yace

"Wow zanso ganin wannn rana kuwa Kashim baba ,Kamar dai wancen karon da kuka tura akasheni ba.To zanso ganin wannan gemes É—in ma tabbas "

Da wani irin tuƙuƙin baƙin ciki, Kashim baba yake kallon maleek..
Ji yake kamar ya shaƙosa harse ya mace tukunna ya wullar da gawar sa.

Kenan dama yaron nan yasan sune suka sa su tuje suje su kashe shi, amma yamusu kwantan ɓauna, sai yayi kamar baisan su bane saima kama wani taƙadarin mutum da yayi ne ya baiyana duniya cewar shine Maison ganin bayan sa.

Ashe ɗan shegiyar yaron nan yasan sune😱 . Suka tura a kashe shin kai wannan ɗa anyi tsinannan yaro.
Su ana su haukan har suna murna baiganosu ba,
Domin saida yafara binciken kamar dai zai kamasu, sai kuma dare É—aya sukaga ya baiyana duniya cewar dagus shine mai bibiyar rayuwar sa.
Nan suka shiga murna shida sauran abo kanan sa, Wallahi harda party sukayi tsabar murna,
Ashe kenan shigo shigo ba zurfi ya musu

Uban naushi dayaji an sauƙar masa saman fuskar sane, ya dawo dashi hayyacin sa da dawowa duniyar mutane ba ta tunani ba.

Maleek ƙafar sa ya sanya ya take jikin kujerar, da Kashim baba yake tare da cewa.

"Dame dame kuke shiryawa akan al'ummah nason ganin bayansu, ku kenan babban. Burinki a rayuwa kunsami Duniya A hannun ku, bayan kashe kashen rayuwakan da kuka sa akeyi ta ƙarƙashin ƙasa! A baiyane kuma kune masu bada tallafi wa al'umma!?, Shin ku ko kunya bakwajine bakwa tunanin idan kun mutu kuma, mezakuce da mahaliccinmu "

******
Gidan su jadda kuwa suna shigewa ciki ummey ta kama hannun jadda ta zaunar tana tambar abinda yafaru
Tiryan-tiryan tashiga zayyano musu iya abinda ta sani
Malam ne ya ɗauko wata ƴar ƙaramar leda da joy ya bashi yace ta magungu nan jaddan ne yayi,
Buɗe wa ledar yayi yashiga futowa da magungunan cikin ledar, yana ƙare musu gani
Dan da gani masu shegen tsadane .
KUƊI kuma suka faɗa ata re dukkansu dan ganin wasu uban maƙudan kuɗaɗen da suka zubo, daga cikin wata farar ambulos,

Against kuma Wata ƴar ƙaramar farar takarda ce ta faɗo, malam ne yayi gaggawar ɗaukowa takardar
Yana walwale wa, rubutu ne a jiki kamar haka.

*Assalamu alaiku iyayen wannan yarinya*
*Naɗan samu accident da ita dan Allah kuƴi haƙuri ku ga farceni abisa tsautsayi abin ya faru*
*Domin aloƙacin bana hayyacina sosae*
*A garin kama abin farauta ta kuma abin harina haka, tafaru*
*Amma kuyi haƙuri da rashin ganina da bakuyi ba*
*Allah zai bata lafiya sannan kuyafemin itama kunaima min gafararta domin na guji zuwa gurin mahalicci na da nauyin wani 'a kaina*
*Sannan kuyi haƙuri bawai dan nasan kunada da kuɗi ko bakwa dashi bani dan ALLAH Aci gaba dayi mata magani badan niba dan ALLAH mai kowa mai komai*
Bslm daga MT

Atare zuke sakin ajiyar zuciya,
Wallahi har cikin rai da zuciyarsu sukejin sun yafema wannan bawan Allah duniya da lahira.

Muje zuwa

Yanxun aka fara

*Shafin nakune masoya littafin 🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥 ngd*

Taku ce akoda yaushe
*Ammeyn laylah 🫶🏻*

*Good 9yt masoya*
*Natafi bacci*

*Shering & comments naku muke da bukata a koda yaushe shine ƙwarin gwiwan mu**🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻*

FREE BOOK
Page 9️⃣

081-04-49-32*15

*Wannan fejin dukka na sadaukar dashi ga masoya littafin 🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*
_______________________________

***********
wallahi har cikin zuciyarsu sukejin sun yafema wannan bawan Allah duniya da lahira.

Daga nan ummey takai mata ruwan É—umi bayi, taje tayo wankan ta, kafin ta fito har an haÉ—a mata abin karin safe.
basma kuma ta fito mata da wata jallabiya ta mata ruwan sky blue, bayan duk ta gama shiryawa cikin jallabiyan tafito tsakar gidan nasu, Masha Allah rigan ta ƙarɓe ta iya ƙarɓa makura, sai dai muce Masha Allah.
A gindin bishiyar mango É—in gidansu suke zaune
gaba ki ɗayan su, sai suka zubo mata idanu iya jiya amma wallahi sai suke ganin kamar ba ita ba taƙara fresh abinta,
Kanta a ƙasa ta ƙaraso wurin nasu tana zama. jingina da jikin ummeyn nata tayi, abincin da aka riga da aka haɗa mata tashiga ci domin kuwa intace batajin yunwa tayi ƙarya.
Tassss ta tashi da abincin kuwa tasha ruwa mai sanyi kana tayi kwanciyarta jikin ummeyn nata tana shafa mata kai.
Ahaka har wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

Kashim baba ne ya sheƙe da wata irin dariya kana kuma ya gimtse fuskar sa duk loƙaci ɗaya yayi wannan abin. sannan yashiga faɗin.
Chapter 6 · 0% Book details