← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 45

Sashe 34

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

JUMA'AT
Babbar rana tunda jaddah ta tashi takejin maranta na mata wani irin ciwo, amma ta daure gudun kada ta tadawa su ammeyn hankali kuma taje ba haihuwar bane, tunda ta jima tana jin irin hakan a tattare da ita shi yasa take daurewa.
*******
Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yammacin ranan tana zaune, tana tsincewa ammey Ayar da zata mata kunun Ayar da tacema Ammeyn shi kawai takes0****
Duba da yana yin nata bayan ta gama tsince Ayar tass ta miƙa zata kaima ammey ayarne kuma, taji zuuuuuuu wani abu mai kama da ruwa nabin ƙafarta, hakan yasa tayi saurin komawa birnin ta zaune, tare da kwalla ƙiran ammeyn.
Kasancewar tasan halin yanayin ta yau ɗin ta tashi, acine yasa ta rugowa a guje, ashe duk ɓoye ɓoyen da take ammeyn tana sane da ita, ganin bata nuna mata bane yasa itama ta tafi ahakan, tasan dai dole idan me gaba ɗayar tazo tofa dole ta nemeta.
Tana zuwa gurinta tace "AYUSHA ko haihuwar ce" cikin qarfin hali da girgiza mata kai haɗi da faɗin "a ahhhhh ammey kawai dai marana ce naji tana sukana, ina miƙewa kuma naji wani abu nabin ƙafafuna".
"Haihuwar ce mu tafi asibiti kawaiiiiii" mu bari ajima koda zuwa dare ne Ammey"
Ganin kuma ba wani abu bane yasa ammeyn dakatawa kaɗan, ganin kuma ta ware harma tayi sallar magrib lafiya ne yasa ammeyn sakin ranta, wajajen isha'i tace ma da ammeyn tana s0n balangu amma na siyasar wa, haka ammey ta bada aka siyo mata balangun aka kawo mata shi a baƙar leda.
Soma cin balangun nata kenan, wani irin azababben ciwon mara ya turnineƙa a furgice ta soma ambaton sunayen Allah, nan danan kuwa ammey ta ida rikicewa. Ana haka sai ga maleek ya dawo a wurin aiki, tamkar kuma wacce dama shigowar nasa ake jira Nan take ta soma wani irin murɗaɗawa tare da kukan azaba,tun tana ambaton sunayen Allah harta koma sai kuka kawai take.
A 36 maleek ya saɓeta a kafaɗarsa yayi cikin mota da ita, ammey ce tayi saurin biyo bayansu itama ta shige cikin motar.
Cikin ƙanƙanin loƙaci maleek ya isa asibiti mafi kusa privete me kyau da tsada inda dama Anan ne jaddan take xuwa awon ta.
Nurse INDO ADO Mai UNGUWA ce ta amshi haihuwarta emagerncy room tayi da ita, ganin wanda ke tare da ita sananne ne a kasar ma baki ɗaya, hakan yasa ita da sauran nurse suka amsheta jiki har mazari yaje, cikin gaggawa suka sóma bata dukkan wani taimakon da suka san zasu iya mata.
Haka aka dinga fama su MALEEK sun kasa tsaye sun kasa zaune, gashi ance musu haihuwar da saura.
Hakan yasa maleek yake ganin kamar ko basu iya aikinsu da ƙyau bane, daƙar ammey ta lallashehi ya barta cikin asibitin, haka jaddah taci gaba da kanta wani irin tukuƙin bala'i ne idan ya faro daga tafin qafarta saiyazo daidai mararta zai cakeee Anan, aikuwa idan ta soma wani irin murɗaɗɗawa da surutan da itama kanta batasan mene take faɗa ba, idan kuma ya lafa mata CENN xuwa jimawa wannan turnuƙun zai kuma dawo mata, gashi ana ta fama amma har wajajen sha biyun dare shiru babu haihuwa babu dalilin ta, hakan yasa jaddah sarewa******
Har take ga kamar itace ba zata iya haihuwar da kanta ba, hakan yasa cikin kuka ta shiga roƙar nurse INDO ADO ɗin dake tsaye akan, akan kawai su taimaka su mata tiyata, nan suka shiga bata baki suma suna qara kwantar mata da hankali, suna faɗin ta kusa saura qiris...
wajajen qarfe ɗaya da rabi loqacin duka nurse basa wurinta sai iya INDO ADO ceeee itama barci ɓarawo ya soma kwasarta hakan yasa jaddah kuwa tayi wuff ta diro a gadon nan, ta saɗaɗo ga azabar ciwon mara da ciki amma haka ya fito wurin da ammey ke zaune, tana zuwa ta zube tana kuka tana faɗin "ammey nasan baxan iya haihuwar nan da kaina ba pls acenzan asibiti muje Amin CS kawai na huta, ana haka nurse INDO ADO ta ƙaraso wajen, bayan ta farka bata ganta bane, hakan yasata fitowa wajensu a guje, ta kuma meda jaddah.
shi kuwa maleek bama ya wurin yana a cikin motarsa ya ɗauka tasbaha yana faman yima Annabi salati, kan Allah ya saukaƙama wannan baiwar Allah tashi.
Wajen ƙarfe uku da mintuna arba'in, naƙuda gadan gadan ta kuma tasar ma jaddah, haka suka shiga fafatawa a filin yaƙin mata, cen tace ma nurse INDO ADO ɗin zatayi kashi, inda dama akwai wani qaton foo na musamman domin irin haka nan akace ta sauƙo tazo tahau, haka ta ƙaraci nishinta amma ko ƙyamass ta gaza yin kashin Nan.
Tana komawa gadon kuwa nurse INDO ADO mai unguwa zira hannu, sai kawai ta ji kai ya taho, hakan yasa tace ta ware ƙafafunta ga kai nan tahowa, Nan tasa ta fara nishi, tun tanayi da qarfinta har qarfin nata ya kusan qarewa, qiran sallar farko tare da dirowar santaleken baby boy ɗin nan ya faɗo duniya, Nan kuwa baby ya zankata ma su ammey qiran salla na biyu, nan ta yanke cibiya tare da gyara babyn da uwar babyn, badai raki ba Dan wurin yasar jini ma ansha daru, inda wata nurse INDO ADO ta fara mata, tayi sau uku tace ya isa.
Nan kuwa wata gabjejiyar nurse É—in tace ta bari ta qara mata koda so biyu ne, ai kuwa jaddah tana kyalla id0 ta hango hannuwan wannan nurse yayi biyun na nurse INDO ADO...
nan kuwa tace bal bata san zance ba,. Haka nurse INDO ADO da ƙyar ta qarisa mata yasar jinin.
Tsabar farin ciki kuwa ammey harda hawayenta, shi kuwa oga maleek sujjada yawa subhanahu wata'ala, wanda ya bashi wannan farin cikin da yasan duk duniya in za'a hadesu babu mai iya bashi, aikuwa ana kammala kimtsa masu jego yayi wuff, ya shige ɗakin yana xuwa baibi takan mutanen cikin ɗakin ba ya haɗe babyn da maman babyn ya rungume su tsammm acikin ƙirjinsa, ya kuma ƙi cikasu ganin rashin kunyar na neman yawane yasa ammey korar shi daga cikin ɗakin.
Nan yashiga É—aukar babynsa zafafan pics a wayarsa qirar samfurin samsum galaxxy 8 4100.
Kafin kace me har wannan haihuwa ta gama zagaye dangi da ma social media, Inda har mutanen Adamawa Kano sun gama bayyanuwa suma acikin asibitin.
Kasan cewar a jirgine suka zooo su duka inda harda su Malam Abdullahi da ummey.
Nan jaddah aka sami abinda akeso ta maƙalƙale ummey ta hanata koda ganin ɗan be wanda ubansa harya riga ya masa huɗu ba, saidai babu wanda yasan sunan wayene ya masa huɗu bar dashi.

Gaba ɗaya faɗin irin farin cikin da wannan ahali suke ciki faɗa loƙacine, inda kowa ƙoƙarin ganin ya faran tama jaddah rai yake, nan aka basu sallama suka ɗun guma gidan Maleek kai tsaye suka nufa, inda suka yanke shawaran ummey ne zata zauna da ita zaman wanka har arba'in.
Ai kuwa ummey taji daÉ—in wannan abu da suka mata, domin sun nuna mata har yanxun matsayin ta yana Nan a wurin jaddah na uwa, malam Abdullahi ma yayi murna da hakan.
*********
Mutane MADINAH ma sun qira video call, inda suka ga santalelen babyn nasu mai kama da maleek sakk babu abinda ya bari nashi, saima kusan kereshi da yayi wajen hasken fata da kuma ƙyau, duba da cewar uwarsa ba cikakkar Hausa bace half cast ce ruwa biyuce, hakan yasa babyn ya zarta mahaifinsa a komai da komai.....

Kwana biyu a tsakani mutanen MADINAH suka dira tare da uban kayan barka saukace hauka, aikuwa zokaga yadda ake ruwan kayan barka, ga uban shimilin kayan akwatunan da maleek ya musu ita da babyn, banda wanÉ—anda suka dinga saya suna ajjewa.
Kai wannan baby yazo duniya a sa'a.
A kuma babbar rana sarki ABDULPHATA OMAR, sarki MALEEK IBN SUFFYAN ma haka suka kawo nasu kayan barkar, inda abinda sarki ABDULPHATA OMAR ya kawo gurgiza zukata da yawa domin jirgin sama guda yaba jikan nasa yace shine jika na farko kuma mafi soyuwa daga ɓangaren matarsa Hajiya maryam abduljalaal yeko,shi sarki maleek ibn suffyan shima ƙyautar da yawa babyn ta girgiza zukata, inda maleek ne da kansa ya garga ɗeni da kada na gayawa FAN'S abinda ya bashi.
Mai girma maleek kuwa ya bawa NURSE INDO ADO MAI UNGUWA kujerar maka tare da wasu maƙudan kuɗaɗen dani kaina AMMEY LAYLERH bansa nawa bane.
___________

Mom sani ita ce mace ta farko acikin FAN'S na KAREN BANA ta tazo wa jaddah barka, tana zama saiga bloody AYSHANTY tazo kamar anjefota, tana muzurai wai danme mom SANI ta gudo ta barta.
Shi kuwa maleek yana daga gefe sai faman murmushi yake musu domin yasan akan meyene suke hakan.
Cen kuma ƙofa ta fara buɗe wa inda OUM SHAHEED, tare da maman Inaya suka diro suma cen saiga masoyiya ✨ Asmitar hydar tare da Aunty Reema suma sun zo barka, a ahhh saiga su teemah shalelen Abba sun bayyana suma.
Ai kuwa nan FAN'S of KAREN BANA suma ƙofa ta buɗe musu💃
Gaba ɗaya KAREN BANA FAN'S groups ne suka zo atare, inda SAPWAN AHMED ya raɓe a bakin ƙofa yana jiran umarni daga MALEEK akan ya masa is0, aikuwa saiga maleek ya taho tare da rungume SAPWAN AHMED, dan shifa maleek baya da tsayayyen abokin daya wuce JAWAD., Gashi JAWAD baya ma qasar hakan yasa yakes0n su raba farin cikin tare da SAPWAN AHMED🥰.
Aikuwa zokaga murna wajen SAPWAN ganin loƙaci ɗaya ya samu shiga a wurin maleek ɗinnnnn...

Hajiya LUBNA

Idan tace zata yi kuka to kuwa tayi qarya domin ta gwada yin kukan, yafi cikin carbi amma ya gaza zuwar mata, hakan yasa cennnnn ƙasan zuciyarta ya kuma kaikasgewa da bushewa.
Inda ta kuma É—ana uban Target É—in dayafi nada tsanani,

HAJIYA LAURA
Loƙacin dataji cewar jaddah ta haihu, ji tayi kamar ta mutu dan baƙin ciki, Ashe bataji komai bama lokacin dataji cewar Sarki ABDULPHATA OMAR jirgin sama guda ya mallakawa ɗan gidan kishiyarta shi kuma ƴarsa ɗan kuma jikansa, jika na farko a wurin sa ai saida takaita ga faduwa ƙasa warwass...

Ahalin malam Abdullahi Rano ma sunyi masa kara wajen zuwa barkar samun qaruwar da sukayi.
*🔥♥️KAREN BANA ♥️🔥*

Na Maryam Naseer mirrah
*Ammey laylerh*

Page 38&39

08104493215
Chapter 34 · 0% Book details