← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"SHEKARUN BAYA"
"A cen shekarun baya da suka shuÉ—e mana, shekaru ne na musamman acikin rayuwarmu dama ahali biyu zuwa uku, ba kowane waÉ—annan ahalinba face ahankali sarki maleek ibn suffyan da ahalin sarki ABDULPHATA OMAR tare da ahalin mahaifan MARYAM ABDULJALAAL"
"Tun ina ɗan ƙaramina nasan girman alaqar dake tsakanin waɗannan ahali sarki ABDULPHATA OMAR wanda yake ɗan uwaa a wurin kakana Sarki MALEEK ibn suffyan sun taso cikin s0n junansu,domin su giyar mulkin bata sa sun guji junansu ba kamar yadda wasu mutanen suke yi a tsakanin su!.. wannan abune yasa alaƙa mai tsanin ƙarfin gaske kulluwa tsakanin mahaifiyata da kuma Amaryar sarki ABDULPHATA OMAR wato MARYAM ABDULJALAAL, aloƙacin da aka kawo ta 9j mahaifiyata ce ta zame mata babbar ƙawa aminyi ƴar uwaa domin bata da kowa anan ɗin, loƙacin da sarki abdulphata ya auro maryam abduljalaal inada shekara goma a duniya ina kuma tsananin wayo wanda ko mahaifana basu san inada wannan wayon da basira haɗi da baiwar da Ubangiji na yamin ba, aloƙacin da na fara ganin AUNTY MARYAM sunan dana bata kenan, na maƙale mata kawai naji ina kaunar ta sosae inajinta tamkar mahaifiyata ne, kai hakan yasa idan sun ziyarci junansu nakan maƙalewa aunty maryam nayi ta kuka ince Ni saina bita a gurinta zan zauna, fatan dukka baku manta hakan ba?.
Ya faɗi maganar yana kallon ammeyn sa da kuma FRIEND,...kai suka shiga ɗaga masa tamkar wasu ƙadan garu kana shi kuma yaci gaba da faɗin.
Haka zanyi ta musu kuka har mahaifina yace ya bawa AUNTY MARYAM niiii! Naje na mata hutun aloƙacin ina primary 5 badan mommah taso ba dan aloƙacin ina wurinta da zama baki ɗaya tun daga yayena da tayi;....haka cikin murna Ni kuwa na shiga haɗa kayana abbiena ya kaini har garin Adamawa da kansa al0ƙacin ne na hango wata iriyar s0yayyar da bantaɓa ganinta agun kowa ba face mahaifiyata wato ammeyna kenan!, sai kuma naji tamkar kada nayi tafiyar saboda wannan tsabtatacciyar soyayyar dana hango acikin idanuwan mahaifiyata akaina, amma kuma yarinta tasa nayi tafiyata Adamawa wurin Aunty maryam, danakejin tamkar akwai raina da rayuwata tare da ita! Naga gata mai sunan gata awurin Aunty maryam domin soyayyar duniya ta ɗauka ta ɗora min duk kuwa da cewar aloƙacin tana ɗauke da nata cikin, Amma hakan baisa ta sauya daga soyayyar da take nunamin ba, haka na fara huta na cikin kwanciyar hankali komi na nema ina samu, idan aka bani abu Tofa saina raba biyu na bawa FRIEND rabin nace mata wannan na MATATACE ko ABOKINA domin ban manta alƙawarin dake tsakanin mahaifan nawa ba;.
Aloƙacin da cikin dake jikin friend yakai wata takwas aloƙacin ne kuma mahaifina yazo ɗaukana mu tafi wai hutuna yazo ƙare su, akuma loƙacin nima na dire nace babu inda zani"
"Domin naji na kuma gani da idanuna irin makircin da auntyn nawa take a ciki haka naƙi yarda sammm nabi mahaifina Abuja!, Akwana atashi babu wuya wata Ranar juma'a wacce takasance babbar rana kuma baƙar rana agaremu Aunty maryam ta tashi da nakuda hankali na idan yayi dubu toya tashi haka inaji ina gani aka tafi da Aunty maryam ɗakin haihuwan:.Tasha matuƙar wuya kafin ta haihu aloƙacin dukkan likitocin dake kula da ita suka fita sallar azzuhur"

"Akuma loƙacinne na samu damar kutsa kaina cikin ɗakin haihuwar ina zuwa na tarda ta haihu ta haifi ƴarta mace, na rasa yadda zanyi gashi bata cikin hayyacinta ita domin ma bata san ta haihunba ba kuma tasan maine ta haifa ba! Ganin almakashi dadai sauran kayan haihuwane yasa na ɗauki almakashin nan na yanke cibiyar domin ina ganin yadda ake acikin game na wayar wasan da Aunty maryam ta saimin, kuma dama dukkan wani FATANA da BURINA shine inzama LIKITA! Haka bayan na yanke cibiyar na ɗaukar kyakkyawar babyn auntyna wanda dukkan jikin nata jinine amman banji ƙama ba haka na rungume babyn a ƙirjina a kuma daidai wannan loƙacinne ta fara wani irin kuka, kukan ashe da ashe kukan rabuwa da mahaifiyane Ni bansaniba, kamar wacce aka sauken wahayin da nayi mata huɗu ba hakan yasa na raɗa mata AYSHA!"
"Sunan ammeyna kenan ina gama mata huÉ—u bar nan likitocin suna dawowa hakan yasa suka koreni nayi cikin gidan ina kuka, anan aka bayyana cewar amaryar mai martaba sarki ABDULPHATA OMAR ta haihu ta haifi Æ´arta mace.
Anan kuma naga mommah Naaaaa Hajiya LUBNA kenan wai dama ɗaukana tazo haka ina kuka ina komai ta kama hannuna zuwa ɓangaren hajiya LAURAH wai zasu gaisa, zaunar dani tayi a daya daga cikin kujerun falon tace na zauna tana zuwa karna yarda na biyota, sammm naji ban gamsu da Wannan dokar nata ba hakan yasaaaaaa

Tofa muje zuwa

Donji mene ya faru a gaba
🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
More comments more typing😌😌😌

Shin mene maleek ya jiyo ?

Menene dalilin sa na kin tafiya yabi mahaifinsa?
Ya akai aka sace jinjirar da ko mahaifiyarta bata samu ganinta?😭😭😭😭🙃🙃🌚

Amsar kunsan tana ina

*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*
👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻🤠👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻

Muje zuwa by
✨ *Ammeyn laylerh🫶🏻*

*Allah yaci gaba da haskaka al'amuranmu cikin farin ciki da kwanciyar hankali🤲🏻*

*Allah Ubangiji kaci gaba da shiga cikin Al'amuranmu Allah kaci gaba da shige mana gaba akan komi namu🤲🏻*
*Ina miƙa sauƙin ta'aziyyyata gareki MUB'ASHA IBRAHIM na rashin dan uwaa da kikayi fans kuma members acikin group na KAREN BANA FAN'S group Allah yakai haske ƙabarinsa Ubangiji yasa mutuwa hutuce gareshi🤲🏻🤲🏻😭😌*

Ohh my God
*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨

*Ammey laylerh*

Page 3️⃣1️⃣

08104493215

Yau fejin nakune masoya littafin KAREN BANA 💔

*Haƙika Ina jin daɗin comments naku sosea masoyansa*

INDO ADO
Fatima lawan60
Fatima Aliyu
A'isha Yusuf
qanwan ta'eeba naman ta'eeba
Aunty apple Naaaa
MLS jamilat
Mub'as Ibraheem

Dama wanda alƙalummana bazasuyi amfani wajen rubuta tarin alkairanku gareni baaa,saidai nace ilahu yabar ƙauna har gaban abadan🫶🏻🫶🏻🫶🏻

*❤️‍🔥It's just that you are close to Ammey Laylerh, she is very kind to you🫶🏻*
________________________Â¥

_____Kawai naji sammm ban gamsu da wannan dokar nata ba hakan yasa na miƙe nabi bayansu!,na laɓe abayan labulen dakin, inas0n ki kashe ta idan kin tafi bana ƙaunar ganin jinin MARYAM acikin duniyar Nan lubna.
"Wannan kalmace da takusan tarwatsa tunanina, amma ina cikin wannan tashin hankalin maganar ne kuma...kunnuwana suka ƙara jiyo abinda ya kusan tafiya da rai da numfashi na, daga matar da naɗauka mahaifiyata a wancen loƙacin wato Lubna!"

"Idan kikace kisa ai kinyi ɗan ƙaramin abu LAURAH, zan tafi da jinjirar yarinyar zan yarda ita a cikin kurmin jejukan dake ƙauyen Kano, nasan rayuwar yarinyar zaya tagaiyara tazam abin tausayi bayan ita jinin mulki ce gaba da baya!.
Ko kin manta da cewar da nima wannan tsinan nan yaron MALEEK so nayi na kashe É—an banza, ammah kuma danayi wani tunani nace idan na kashe! shi dole uwarsa ta haifi wani, wannan yasa na sanja tunani ta hanyar raba uwarsa ta mahaifarta baki É—aya, sannan nazamar da yaron tamkar bawa acikin gidana, sannan shi kuma yaron na cusa masa tsantsar tsanar mahaifiyarsa AYSHA GALADIMA, kana kuma nayi amfani da yaron wajen tarwatsa rayuwarsu da kansu shida shegiyar uwarsa!"
"Miye kike ganin zai faru gaba?" Idan har wannan shawara tawa tayi miki hhhhhhhhh suka sheƙe da wata shegiyar dariya ta tsantsar rashin imani da mugunta"

"Wannan zance nasu da naji,shine farkon shafin ƙaddarar ta tazo ta gitta daga cikin rayuwana, shine dalilin sauyin ra'ayina daga zama LIKITA zuwa SOJA, domin kawo ƙarshen zalumci irin nasu LUBNA da LAURAH.
Wannan shine abunda baya taɓa gitta wa daga cikin rai da ruhina, wannan abu yasa nayi alƙawarin zamewa wannan jaririya GARKUWA agareta;"
"Kafin su fito kuwa bayan na tabbata sun gama tattauna komai. nayi saurin komawa saman sopar da mommah ta zaunar dani tamkar babu inda na motsa...saima sautin kukana dayafi na ɗazu yawa da gunji, da banyi niyar bin mommah na ba amma wannan dalili yasa na amince zanbita, zanbita domin kare rayuwar rayuwata AYSHA ABDULPHATA...haka mommah ta jani muka fito ashe Hajiya LAURAH sun haɗa baki da likitocin cikin masarautar ta hanyar siyesu da wasu maƙudan kuɗaɗe, koda muka fito kai tsaye cikin clinic ɗin masarautar muka nufa!" Koda isarmu har sun saka jaririyar acikin kwali, muna shiga aka miƙowa LAURAH kwalin Nan wanda na tabbata jaririyarce acikin wannan kwalin, haka inaji ina gani a gaban id0na! Hajiya LAURAH ta miƙowa mommah wannan kwalin ko sakan ɗaya bamu ƙara acikin masarautar Adamawa ba muka ɗauki hanya, tafiya muke babu ji babu gani haka muka dinga tafiya, munzo daidai wani gari da bansan ko ina bane amma jejin garinne ta faka motar tace na zauna acikin motar tana zuwa ta ɗauki kwalin Nan tayi gaba, tana fita a motar saida na tabbata tayi nisa ni kuma na fito na dinga bin bayanta!....saida muka wuce gonaki uku ta tsaya tana ajiye wannan kwalin Ni kuma ganin ta ajje wannan kwalinne yasa nayi saurin zaro kibiyar da riga na ɗauka tun acikin ɗakin LAURAH, wata jikin ƙatuwar bishiyar gamjin dake kusa da gonar na shiga rubuta cikin sauri domin yazame min shaida wajen gane wannan gurin!" Abinda na rubuta kuwa ba komai bane faceee...

" RAYUWAR AYSHA ABDULPHATA da RAYUWAR MALEEK TAUFIQ WATA RANA ITACE SANADIN KU"
Chapter 25 · 0% Book details