← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 45

Sashe 44

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunyi baƙin ciki matuqa loqacin da suka san waye mahaifinsu. Kana amayar Kashim baba wacce da taimakon ta maleek yake samun dukkan wani ishu akansu da motsin su. Haka sukayi kuka suka share ashe itama amaryar faɗe ya mata shine kuma ya aure ta bata da uba mahaifiyar ta rashin qarfi da rashin mataimaki yasa ta bashi auren ƴarta badan.ranta yaso ba, saka makon cikin daya ɓullo bayan yi mata faɗen da yayi.

*JINIOR AHLAM*

Na farkon littafin mu wanda suka faÉ—a da jadderh harya mareta. Ashe tun daga wannan tafiyar ba'a kuma ganin sa, saka makon maleek dake dabaibaye da rayuwar jadderh, tun wancen loqacin ya ka mashi ya garqame sai bayan wani loqaci ya sake shi bayan yasha kwakkwaran kashe di na Bara zanar da yayi wa rayuwar jadderhn.
Inda wannan abu da maleek ya masa shine dalilin shiryarsa, dama É—an wani me kuÉ—ine dake Kanon ai kuwa maleek yasha adda'a wurin iyayen AHLAM.
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylerh*

Lass page 4️⃣9️⃣&5️⃣0️⃣

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
==========================

*~💐 It's just that you are close to AMMEY LAYLERH, she is very kind to you🫶🏻~*

*DEDICATED TO UMMIE MUHD NASEER {Maman Humieratou, Mrs Yusuf babbah Aujara.}*

Wannan page na sadaukar da shi, wa RAYUWATA baki É—aya My teemah ta fateemah Ibrahim malam Aujara

******
___________________
Shekarar ayman É—aya A duniya jadderh ta kuma samun wani cikin, aikuwa jadderh tasha kuka danma loqacin ayman yana yawonsa ko ina.
Kuma dama irin yaran Nan ne da shan mama bai dame suba, haka ne ma yasa Ammey É—auke Ayman ganin dama ba wani damuwa yayi da tsotson ba. Shi kuwa dama dake ya saba da ammey yayi zaman sa, saima kamar qara masa lafiya da aka yi ma.
Ita kuma taci gaba da rainon cikin ta, wanda yazo mata da azabar laulayi kamar me.
Wurin aikin maleek kuwa saidai muce hamdallah , dan kuwa nasara da buÉ—in Ubangiji haka ya ringa samun su, shine tukuici abun Alkhairin.

Do good for others it will come back to you on unexpected time👌🏻
Ma'ana.

Yi wa wasu alheri zai dawo gare ku a lokacin da ba ku tsammani ba😌

Tsabbb kuwa hakan ne ya faru da GENERAL MALEEK TOUFIQ MAI NASARA, dan kuwa wani abu ma ya manta da yayi a cikin rayuwa, haka tarin Alkhairinsa keta dawo wa gareshi, hakan yasa ya qara ƙaimi da himma wurin aikinsa, dan ganin wa cire ɓata gari daga cikin al'umma. Inda sunan GENERAL MALEEK TOUFIQ ya karaɗe ilahirin faɗin DUNIYA, babban burin kowa ace yau Alkhairinsa ya zo gareshi, inda wata haiba da daraja suka sake hawansa.

§Bayan shekaru goma sha biyar👯🏻‍♀️§
*************
Abubuwa da dama sun pharu, a kimanin waÉ—annan shekarun marasa daÉ—i da masu daÉ—i.

Ciki marasa daÉ—in kuwa ya haÉ—a da mutuwar Hajiya Laura, inda ta rasu bayan doguwar jinyar data sha. Bayan dogon loqacin data É—auka.

Hajiya lubna ta fito daga gidan yari, inda gaba É—aya ta zama wata so silent, dade da magana ma bata dame ta ba.
Inda Hajiya AYSHA galadima ammey ta É—auki nauyin É—awainiya da ita.
**********
Mu koma bangaren su GENERAL MALEEK TOUFIQ MAI NASARA.

Ya zama cikakken magidanci inda girma ya fara hawansa, wani matashin saurayi ne zaune a gabansa É—an kimanin shekaru goma sha sha bakwai, gefe guda kuma wata mata shiyar budurwa ce. Itama Æ´ar kimanin shekaru goma sha shida.

"Papa Ni kawai kace ta fita acikin harkana tunda bata da kunya"
Cewar ayman Keenan matashin saurayin dake ji da gayu, da kuma tashen samar taka.

É—ago dararan idanunta tayi wanda suke kama sakk dana HAJIYA AYSHA ABDULPHATA OMAR {Mamie jadderh}.

"Kaji ko papi! kaji da kunnen ka ko wllh yaron Nan ya rainani, dan kawai ka bani 1 years old. Shine ka ranani har haka.."

Bakin tan ya buge tare da cewa
"shiiii"
"Amma dai ai yayan kine kuma ya fikin" ya faÉ—a cikin zaro mata lumsassun idanunsa da har yau basu sanja kama baaa.
System nashi yaja gefe tare da fuskantar gabas sabo da wani irin azababban ƙamshin da jiyo daga ɓangaren, ƙamshin dake rikita masa tunani da kwakwalwar sa, wanda yake sa shi mance waye shi. Amaryarsa kuma uwar gidan sa kenan HAJIYA AYSHA ABDULPHATA OMAR. Cikin takun ƙasaita ta nufo parlourn, cikin wata kyakkyawar shiga ta alfarma ta kece raini. Wasu matasan yara biyu biye da ita, ɗaYa kuma a rataye a kafaɗarta. Toufiq kenan da kuma little MARYAM, ƴan biyun data haifa, shekararsu tara da haihuwa a duniya toufiq ana ce dashi Ashraff, sai kuma little maryam anace da princess.
Sai kuma auta kilishi wacce taci sunan kaka wa maleek wato Fulani anace da ita kilishi sabo da sunan mai sunan data ci.
Yaranta biyar biyu maza uku mata inda gaba É—aya yaran, suka tashi cikin wata irin tarbiyya da girmama junansu, da kuma mutunta mutane dan sabon da suka tashi dashi kenan.

Tana qariso tsakiyar parlourn ta wani irin jujjuya idanunta, tare da ma maleek yaran su dake zaune a gabansa, suna kallon mahaifinsu shi kuma yana kallon mamansu.
Kafaɗunsa ya ɗaga irin ko a jikin nan nashi, tana xuwa daidai kan little ammey wato AYSHA MALEEK TOUFIQ ta ɗan dungure mata ƙeya, tare da faɗin..

"Har abada kekam a kawo ƙarar yayanki zaki kare kenan NURHAN?, sammm baki biyo sunan mai sunan kiba ko ɗaya, ga shegen tsokanar ziya a wurin ki!"

Ta faÉ—i maganar tana dallara mata wata uwar harara.

Maleek da duk ya kusan susucewa a zaunen da yake ne yasa shi faÉ—in.

"Aike ta biyo komi da komi nata na kine, samm batayi halin Ammey na wllh ko ɗaya, gaba ɗaya kin ɓata min uwa"

Itama harar ta aika masa tare da zaro masa idanunta, kana da farfara masa su hakan yasa yayi saurin🥰😅.

"Kuta shi kuje AYMAN zanyi maganin ta ne"
Abinda ya iyawa furta wa Keenan, tsamm kuwa suka miƙe dan cika umarnin mahaifin nasu, suma Ashraff da kuma princess suka mara musu baya.
Ta hanyar kama hannayensu da yayyensu suka yi.

Suna barin parlourn maleek yayi saurin miƙewa tsaye tare da rungumo, jadderh cikin jikinsa.
"Waikam minene sirrin irin wannan shan kyau haka, kodai akwai ajiyata anan ban sani ba?"
Ya faɗi maganar yana shafa saman cikin da yake a shafe tamkar bata taɓa haihuwa ba.

Cikin wani irin salon jan hankali tace.

"Kaine sirrin jarumina kuma ƙaunana, sai dakai Duniyar jadderh MALEEK take haskawa. Amma meiya sa sammm baka girma ta wannan fanni?"

Wani irin shigewa cikin jikinta ya kuma yi tare da qara cusa kansa cikin wuyanta,
"Ai ke ɗince ta musamman da komi naki, sammm baki taɓa sanjawa sai ma qara haɗewa da kike abunki. Yanxun dai muje aji dani dan nakai gaɓar da bazan iya jurewa ba"

AUTA kilishi dake maqale a kafaÉ—ar jadderh, wacce tuni barci yayi awon gaba da ita suka kai É—akin ta tare da kwantar da ita akan gadon ta, tun daga bakin qofa suka fara al'amurra nan naja musu qofa dan gudun yauma kada su bani maganin barci. Yauma na kasa moruwa kamar waccen RANAN.
Haka suka raya wannan dare cikin annashawa, da tarin farin ciki, inda maleek sai sanya ma jadderh albarka yake, dan ta kula dashin sosae kamar yadda ya buqata.
*****
Basma tana yara huÉ—u inda tama jadderh takwara haihuwar farko aiko zokaga murna, da uban kayan data jibgawa little AYSHA, inda suke zaune cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Gaba É—aya sun zama wasu manyan hajiyoyi. domin ko waccensu harkar business tunda kamo harkar kayan lefe cosmetics Women's jewelry kayan siyayyar jarirai.
Maka kuwa sunje yabi a qirga, mazajensu sun biya musu suma kuma sunjajje da kuÉ—in su.

Suna kyauta suna sadaka hakan yasa suka zam, tamkar wasu taurari masu haskaka duniya. Basma ta biyama iyayenta suma sunje hajji sunje Umrah.
Gefe guda sun haÉ—e sun zam abu guda suda ASMA'UN M MAHII SAURAYIN YAYATA.
Suda su Nihal É—in Ayaan, jadderh kam ta zamo Æ´ar gatan dangi gaba da baya dan itace AUTAR AHALI, tamkar yadda suka raÉ—a mata.

AYMAN MALEEK TOUFIQ
Yana karatunsa ne akan likitanci, kasan cewar yasan labarin mahaifinsa na san zamowa likita a wancen loqacin.
Amma ƙaddara tayi aikinta a kansa ta hanyar sauya masa buri da kuma fatansa, hakan yasa Ayman yace saiya cikama mahaifinsa burinsa, ta hanyar zamowa cikakken dactorn da babu kamar shi.

Kwance suka akan haÉ—aÉ—É—en gadon su kanta, akan ruwan cikinsa bayan kammala ibadar Allah ta hanyar faranta ran junansu.

"I love u too my watermelon my heart, Ina tsananin ƙaunarki MATATA uwar ƴaƴana. Ta hanyar da baki bazai iya misalta yadda nake tsananin ƙaunarki, sai dai nace ilahu yabar ƙauna ta har gaban abada, ƴar aljanna!"
"Saidai wani loqacin ita kanta rayuwar duniyar tsoro take bani, matuƙa duk yadda ka kai da iya taka tsantsan da duniya, to tabbas wani baya taɓa ganin hakan. Kinsan wani na samu acikin ɗaya daga cikin fan's nawa na Instagram wani ya gaya min wota maganar da har na koma ga mahaliccin na, bazan daina tuna wannan maganar ba. Saidai Allahu ya Iya mana badan iyawarmu"

Rungume shi tayi tsammm a cikin jikinta bayan ta haÉ—e bakinsu wuri guda ta bashi wani kyakkyawan
kiss.

Cikin zallar hikimar tsara zance da wayon da ubangiji ya bata, ta shiga faÉ—in

"Tsabtatacce tsarkakakke baya damuwa da surutu, da munana zato da munanan kalamai, da miyagun kulle² mutane akansa. Ƙara nutsuwa bawan Allah! Ka kuma kauda kai, ka toshe kunnuwanka domin bazaka kuɓuta daga irin abubuwan, dako Annabawan Allah basu kuɓuta daga suba. Naka shine koyi Annabawan ALLAH! JARUMIN jadderh da kuma Ammey da Abbie"
Rungume ta shima ya kuma yi tsamm tamkar ya mai da ta, ciki haka yake ji.
Shi yasa Ahar kullum yake qara gode ma Allah subhanahu wata'ala da ya bashi jadderh a matsayin Mata kuma uwar Æ´aÆ´an.

"Alhamdulillah, alhamdulillah alhamdulillahi ala kulli halin, Ahar kullum ina qara godewa Allah. Daya bani mata ta gari kamar AYUSHHH, haqiqa samun mata ta gari ma Rahama ce daga cikin Rahamomin Ubangiji, Allah shine abin godiya Allah ya dauwamar da haske marar yankewa daga cikin Rayuwar mu, haqiqa keÉ—in matar Alkhairi ce kana MACEN SIRRI, Allah ya dawwamar da farin ciki acikin rayuwarki na har abada. AYUSHAAA ABDULPHATA OMAR Adamawa".
Chapter 44 · 0% Book details