← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 45

Sashe 37

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bani da loƙacin ɓata laƙacina zanyi biyayya wa shugabana, kawai wajen miƙaka hannunsa ba tare dana sheƙe kuba ku duka, amma da zarar naga abinda raina bai gama kwantamin da wasu abubuwan ba dole saina sheƙeku da hannuwanaaaaaa!" Ya faɗi hakan ne yana wani irin mutsutstsuke hannuwan nashi.

Murya ƙasa ƙasa Ibrahim nera yace " hattara dai yaro bari kaga ƙarɓin shugaban cina"
Hannun yasa ya ciro wayarsa tare da laluba wata NO wacce aka mata sifelin da VP, ya doka ƙiran numbern.
Yana jin an É—aga numbern cikin zallar iya mugun makirci, ya shiga faÉ—in " Inason ashiryomin privete jet na musamman tare da masu tsaro, ina tsohon campany na dake sule ja 24 house"
Daga çen ɓangaren kuma mai girma Chief of army ne ya amshe zancen da cewa " Allah mr. President, za kuwa mu shirya hakan kamar yadda ka buƙata ɗin mr. President" ya ƙarasa faɗar hakan yana yanke wayar baki ɗaya.
Cikin woni irin tashin hankalin da ba'a sa masa rana, su kashim baba suke ja da baya. Domin duk abinda aka faÉ—a É—in akan kunne su, hakan yasa 380 suka ranta ana kare, ganin kamar mushe zai juye da miji ya.
Nan take maleek ya take musu baya ganin suna ƙoƙarin tserewa ne yasa shi zaro guns ɗinsa , dake maƙale a aljihun wandonsa, Kashim baba ya fara harbi a gwiwa. Hakan yashi sakin wota irin azabar ƙara, nan ya shiga harbinsu gaba ɗaya saida maleek ya tabbatar yaga raunatasu.
Kana yawa sauran rundunar su ta sojojin dasu tattare masu raunin cikin su.
Wata baƙar mota ce Hilux tayi parking daidai wannan tsohon campanyn, wata dojuwar matace ta fito a cikin ta. Inda tun daga kan ƙafafunta har zuwa samanta, babu abinda ake gani gaba ɗaya kayan jikinta baƙaƙe ne, ga liƙaf data ɗora a saman fuskartan, hakan yasa kai tsaye ba zakace ga yanayin ta ba in ka ɗauke tsayi kawai da matar take da. Cikin taka tsantsan take tafiya wani abu saɓe a kafaɗart, wanda yayi kama da riƙon ɗaukar jariri, saida ta tabbatar babu komai kana ta sanwo kanta cikin tsohon campanyn taci gaba da tunkarar cikin gidan
Maleek dake tsugunne daga jikin wata baƙar mota ne ya saki wani irin murmushi, duk kuwa da halin da zuciyar take a ciki, hakan bai hana shi sakin murmushin ba,
Tazo daidai tsakiyar harabar wajen kawai babu zato babu tsammani, taga MALEEK TAUFIQ tsaye a gabanta yana tafa hannayensa tare da nuna ta da guns yana faÉ—in.

"YOUR UNDER ARREST my Mommah"

Hakan yasa ta sakin abinda yake riƙe a kafaɗartan, cikin wani irin salo maleek ya taro abin tare da rungumesa tsammm a ƙirjinsa.
Ita kuwa gaba É—aya jikinta ne ya shiga mazari, tare da wani irin tsoro mai tsanani.
Cikin fusata maleek ya É—ago ya zubama matar idanunsa, wanda suka kaÉ—a sukayi jawur dasu, ya fara magana cikin azabar sukar zuciya abinda yake shirin faruwa koma yace ya farun.
"Ahar kullum ina takaicin lalacewar ƙasata! Yaushe zata gyaru? Yaushe sanji zai zo mana? Kowa ya juya bayansa kansa kawai ya sani! Yana tafiya a kife Ohhhh Allah!. Nayi baƙin ciki da takaicin yau ga ɗaya daga cikin ahali na da laifi dumu² andaɗe ana ruwa ƙasa tana tsotsewa, amma duk da haka baki ankara ba LUBNA!, Waima mene kike nema?".

"Kuɗi?, Mulki?, Duniya? Nasan dole acikin hakan kina da buƙatar ɗaya daga cikin su, koma dukka kike da buƙata ohooo! Matar mahaifin JARUMI SADAUKI MALEEK TAUFIQ tsamo tsamo acikin manyan gawurtattun masu lefukan Nan da aka kama, tana ɗaya daga cikin su!. Shine burinki? Shine alfaharinki ba?".

Gaba ɗaya jikin ta tamkar babu wani abu mai rai daya saura haka take jin kanta, yaushe? Yaushe?, Yaushe MALEEK yasan tana cikin ƙungiyar su Ibrahim nera? Taya kuma akayi yasan itace ta shigo wurin kai tsaye? Bayan kuma gaba ɗaya jikin ta a rufe yake, koda yatsarta ba'a iya gani.
Amma kai tsaye yace mata.

YOUR UNDER ARREST my Mommah. Shine kalmar daya girgiza DUNIYAR ta.
Hannayensa ya rataye a qirjisa tare da zuba mata runannun idanunsa, sannan yace

"Wannan haka yake amma kisa Ni domin sauƙaƙama wasu! Dole sai an takura ma wosunsu,sai kuma an sadaukar da wani abin ake samun wani, kamar dai haka!"

Ya faɗi hakan yana zaro onka ya kama hannayenta, ya zira mata onkar. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin "uhummmm to da kyau JARUMI, amma ka sani kare da da yaga rawar kura cewa yayi da kyau. Ba lallai kasan koni wace ba!, Lalubene kawai acikin duhu kakeyi maleek! Baka da hujjar da zaka sa kotu tayi aiki a kaina.
Cikin wani irin salo maleek ya karyar da wuyansa gefe, tare da faɗin atafin hannayena kike komai Mommah, domin tundaga ranar dana gama sanin ke ko wacece, hakan yasa naci alwasai akanki Mommah, tun ranar da kika ɗauke min RAYUWA ta tun daga ranar nasan asalin ki! Sannan nasan wacece keeeee. Zanso ki hasaso ranar Mommah keda aminiyar haɗin ki Laura!. Dama! damammaki!! Rana! Ranaku!! Loƙaci da loƙuta duk a lissafe suke kuma tafiya suke cikin tsarin ubangiji sammai. Abu mafi haɗarin kuma nine jagoran tafiyar!, Wannan shi ake ƙira da ƙarangiya, kin haƙa ramin da zai rufta dake! Gurnanin zaki kaɗai yakan sa sauran namun su girgiza, ya hana su samun kwanciyar hankali. Hausawa sunyi gaskiya tabbas na yarda KAREN BANA shike maganin ZOMON BANA Mommah. Ya faɗi maganar daidai lokacin da su Jawad suka ƙara SO da sauran masu laifin.
A kuma daidai loƙacinne shel kwafta na sojojin 9j ya dira a tsakiyar babban filin campanyn, nan aka yi gaba dasu Ibrahim nera tare da sauran miyagun yaransu.
*****

ACEN GIDAN MALEEK kuwa.

Idan hankalinsu yayi dubu toya tashi, ummie dake tare da AYMAN suna kwance akan 3ster acikin parlour. Barci ya fara É—aukar ta sama sama, ita kuwa jadderh tana cikin bedroom É—in ta tana barci itama.
Ƙawai sai farkawa sukayi sukaga babu ayman babu dalilin sa, da ummie tasha tana barcinne yayi kuka bata ji ba, shine uwarsa ta fito ta ɗaukesa, sai kuma da taga shiru shiru ko motsin jadderh batajine yasa jikinta bata kamar ba ƙalauba.
Hakan yasa ta nufi bedroom É—in jadderhn, amma me zata ga sai taga wayam babu alamar jariri a tare da jadderhn, hakan yasa ta shiga tashinta koda ta tashin take kuma tambayar ina kuwa AYMAN. Tace mata ai yana wurinta Nan fa hankalisu idan yayi dubu toya tashin jin baya gurin kowanne acikin su, ai kuwa jadderhnku ta taqarqare ta zunduma uban ihun daya É—au hankalin uban jami'an da maleek ya zuba. A 370 suka shigo cikin parlourn gidan ganin matar ogansu ta dage sai uban kuka take hakan suma ya tashi hankalin su kwarai da gaske. Jin anshigo har cikin gidan an kuma É—auke AYMAN wanda su kansu haidane yaron shine DUNIYAR ogansu maleek, ai kuwa Nan kowa ya shiga tashin hankali marar iyaka a cikin su, wasunsu harda masu fara hawayen tausayin kansu da kansu.
Cikin tashin hankali marar qarewa ummie ta qira ammey take faɗa mata wannan tashin hankali da suke ciki, ai kuwa itama idan hankalinta yayi million dollars toya tashi, cikin qanqanin loƙaci sai gata a gidan maleek ɗin.

Abinda zaifi baka dariya da tausayi kuwa gaba ɗaya jami'an tsaron gidan maleek ɗin, sunyi knel down suna wata waƙa dagaji irin ta sun shiga tsaka mai wuyar nan ce.
Abu mafi tausayi kuma kowa a parlourn hawaye yake ɗauke wa daga saman kuncinsa, ammey kuma faɗi take "dama nasan da wata a ƙasa ba kuma banza tunda yaron nan ya zuma mana uban jami'an tsaro acikin gidayan! Hankali na yaƙi kwanciya da hakan, ashe ashe kuwa da abinda yake shirin faruwa damu! Shi yasa sammm bana qaunar wannan aiki NASHI, amma idan nayi woni tunanin kuma sannan nayi duba da hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama! Sai na fawwalama Allah al'amurran sa, amma dama na daɗe jin wannan aikin nashi sammm babu alkhairi acikin sa!"

"Ya Allah! ya malikul zuljalalu wal Ikram ya Ubangijin talikai ya Ubangijin sammai da ƙassai ya Ubangijin Al'arshi! Ka karemin yarana da yarona a duk inda suke, ya Allah🤲🏻".

Ɓangaren su maleek kuwa kai tsaye babban barikin sojojin Nigeria dake Abuja suka nufa dasu Kashim baba, suna shiga harabar barikin sojojin gaba ɗaya sojawan wurin suka hau wani irin iface ifacensu da masu hankalin cikinsu da marasa hankalin, Nan da aka garƙame su Ibrahim nera bayan anyi uwarka ubanka tsakanin sa da vp ɗinsa isa gwal aikuwa saida ya kuma jama kansa domin Anan ma saida maleek ya ladaftar dashi sosai. Ganin AYMAN yana kuka ne yasa Chief of army staff cewa yaje wa iyalansa ko safi samun kwanciyar hankali da nutsuwa tattare dasu. Baiyi musu ba kuwa domin shima yana da buƙatar hakan. Hakan yasa aka shirya masa motocin rakiya har guda shida, tashi a tsakiyar su itace ta bakwai ɗin. Haka suka rankaya sai gidan maleek ɗin.
A loƙacin wajen qarfe biyar da mintuna, suna shiga cikin harabar anguwar suka fara sakin jiniyar sojoji, hakan yasa gaba ɗaya mutanen parlourn fara rige rigen fitowa. Har xuwa wannan loƙacin kuwa abinda yaga cikin su Ammey, kowa ya gaza iya cin komai koda kuwa ruwane.
Haka suka jeru tamkar wasu sojawa, haka suka ƙame a tsayen da suka.
Har sanda maleek ya fito daɓe da AYMAN a qafaɗarsa, gaba ɗayansu har rige rigen qarɓan AYMAN suke.
Ita kuma jadderh a guje ta É—iba, tana zuwa ta haÉ—e da maleek É—in da AYMAN ta rungumesu duka, tana sakin kuka mai tsananin azabar gaske.

Not editing🙃

Kuyi joining group ɗin kana kuyi shering pls👏🏻
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✍️
*Ammey laylerh*

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟

Page 4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣

08104493215
Chapter 37 · 0% Book details