← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 45

Sashe 14

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan karon kamm bazata iya jurewa yanda Amon muryarsa ke fita ba, gashi kuma duk ta ƙosa ya tafi ya barta.... Hakan ne yasa ta furta masa "UMMIENAH" cikin kasalalliyar murya! Tana ƙarasa faɗawa saman jikinsa¡!¡

Sauƙar lallausar fatar jikinta akan nasa jikinne yayi sanadiyar miƙewar tsikar jikinsa take yaji ƙofofin sadarwa tunanin sa sun tsaya, yayinda taushi da kuma laushin jikinta suka birkita masa tunani da lissafin sa loƙaci ɗaya suka kuma sauƙar masa da nannauyar kasala, idanunsa da suka ɗan soma marairaicewa ya zubawa ƙyaƙyƙywar fuskarta wacce tayi smooth take kuma shining ɗin kyau , ahankali ya kuma sauƙe ganin sa bisa tsayayyun albarkatun haɗaɗdun ƙirjinta, saurin kawar da kansa da tunanin sa yake ƙoƙarin yi amma hakan naiman fin karfinsa yake yi..

Cikin kasalalliyar muryar daya kusa zauta tunanin JADDAH ya raÉ—a mata "kuma shine duk wannan abin dan kinason birkitani da kuma tunani JADDERH"

Sakinta yayi ganin zuciyarsa na ƙoƙarin ingiza shi akan wani abu na daban wanda bai shirya wa hakan ba kuma, da sauri ya hawe saman sa cikin wani irin yanayin dashi kansa ya rasa na mainene,

Yana zuwa ya zube kan makeken gadonshi yanaji tamkar zuciyarsa zata tarwatse kan wani dalili nata na daban wanda shi kammm sammm baiyarda da abin da zuciyar nasa ke ƙoƙarin tursasashi akai baaaa, ahaka wani wahalallan barci yayi awon gaba da shi ko takalman ƙafarsa bai samu damar cirewa baaaa

Ita kuwa JADDAH saida tayi kukanta mai isarta, wanda kuma tarasa takamaimai da kuma dalilin na menene shi kafin itama barcin yayi awon gaba da ita anan kan sopa É—in palon

Hajiya lubna Mommah ce keta faman kaiwa da komowa a makeken palon nata duk abin duniya yadameta, ganin ɗan ƙaramin abu na neman gafarar ta taje aƙalla gun malamai ƴan tsubbu wanda suke cin dunduniyar musulunci suke amsa sunan malamai a baiyane, amma duk inda taje maganar ɗaya ce ba sanja zani shine ta rabu da wannan Auren domin kuwa akwai rabo mai tsananin gaske, tsakanin MALEEK da JADDAH , idan kuwa harta dage akan sai an raba wannan Auren to kuwa itace zata *MUTU*; idan ta tuna wannan maganar tanajin tamkar ta janyo zuciyarta ta jefar akasss
Cikin zafin zuciya ta kaima iska naushi haɗi da furzar da wani irin turirin baƙin ciki mai ɗacin gaske

"Nice ajalin ahlinki Aysha" domin daidai da rana ɗaya bantaɓa jin koda kwatankwacin ƙaunarki keda yaranki ba shima MALEEK saboda wani dalili nawa nake tsananin ƙaunarsa! Amma a yanzun nayi watsi da wannan banzan dalilin nawa bayanku kawai nakeson gani kota halin ƙaa ƙaa nee kuwa Aysha galadima, ta faɗa cikin ƙara ji tamkar wata ƴar daba ko wacce ta shawuuuu

Ammey kuwa bayan fitar Hajiya talatu nera daga palon nata kai tsaye palon JADDAH ta nufo domin ja mata kunne, akan duk wani harka na gidan ta fita a sabbar kowa sai kawai wanda yace zai yi da ita to itama tayi dashi sai kuma tana zuwa bakin palon ta tura ƙofar kenan taga JADDAHN ajikin MALEEK, shine dalilin da yasa ta komawa baya ba shiri

Yau zaɓe saura kwanaki biyar kenan cibbb wanda iya tashin hankali su Alhaji Atiku sun shiga, na rashin baiyanuwar Kashim baba har wannan loƙacin,
A kuma wannan karon sun shirya tsabbbb ko babu domin ganin sun fuskanci maleek gaba da gaba sunyi fito na fito dashi, domin sunga ma yarda maleek ne kaÉ—ai zai iya musu wannan É—anyen aikin;.... Saidai kuma wani tarin al'ajabi daya ziyarar ci ko wannen su bayan gama taron nasu washe gari da safe baiyanuwar Kashim baban ta tarwatsa kwanwarsu dama tunanin su

Domin kuwa a washe garin da suka gabatar da wannan zaman Kashim baban ya baiyana, anan suka haÉ—a wani sabon meeting na gaggawa sukayi zama mai sunan zama, dan kuwa sun tattauna sosae akan al'amura da dama da kuma buruka mabanbanta;.....

Cikin tsananin azabar ciwon dake sukar zuciyarsa yake buɗe idanunsa wanda suka sauya launinsu daga farare zuwa jajaye ƙiran sallar la'asarin da ake ta faman yi, shine ya tashe shi a nannauyan barcin da yayi awon gaba dashi
daƙyar ya iya kai kansa cikin toilet ɗin sa yana zuwa baiyi wata wata ba ya sakarma kansa shower, yafi ƙarfin sama da 15 minutes ruwan na sauƙa saman lafiyayyar fatar jikin sa, amma ko gezau baiyi ba kuma baida niyar barin toilet ɗin,
Sallar dayaji an tada ne yasa shi saurin kashe shower É—in tare da É—aura towel ya fito yana tsane gashin kansa da wani mini towel É—in dake hannun sa cikin hanzari irin nasu na kartin sojoji yayi maza maza ya shirya kansa cikin doguwar riga ta maza kamfanin kimono a gurguje ya fice a É—akin nasa,

Tana kwance inda ya barta har yayi kamar zai wuce sai kawai ya fesa mata saurin ruwan alwulan dake bakinsa saman ƙyakykyawar fuskar ta firgigit kuwa ta farka, tana mutsurtsuke idanuwanta ganin shine yasa ta saurin sadda kanta ƙasa, alamu ya mata da tatashi tayi sallah kai kawai ta ɗaga masa tana miƙewa tsaye ta nufi cikin ɗakinta, shi kuma yayi waje

____________________

Bayan 2 week's anyi zaɓe angama cikin aminci da kwanciyar hankali inda duk masu mugun nufi suka ajje gefe sabo da samun nasarar su, inda kuma suɗin neee suka ƙara lashe zaɓen , a sannu kuma zasu fara fitowa MALEEK ta inda baiyi zato ba , sunbarwa kansu sani iyakar kansu

Yayin da zaman JADDAH da MALEEK yafara sauya wa daga yanayi na kai da kai zaman nasu yafara sauya wa anata samun ci gaba da saka makon shigar sabgar juna dasu ka fara.......

A gefe guda kuma maleek shi kaÉ—ai yasan irin abun da ya shirya wa su Kashim baba sai shi sai zuciyarsa

Kamar kullum yauma zaune suka bayan sallar isha'i suna kallo a arewa 24, wani series suke kalla na indian hausa gyangyaɗi ta fara daga zaunen da take, kibbbb ta faɗa kan maleek dake zaune ya miƙe ƙafafunsa, hakan nema yasa ta faɗa saman cinyarsa ba tare da tasan tayi hakan baaaa....... Shi kuwa sai wajajen sha biyu da rabi ya saɓeta a kafaɗarsa yayi ɗakinsa da itaaaaaa

Sai anjima

*By ammeyn LAYLERH*

*🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥* karen bana *KAREN BANA*

Kada ayi babu keeeeeeeeee

Shering and comments fisabilillah👌🏻👏🏻🙏*🔥❤️KAREN BANA❤️🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH
*Ammey laylerh*

FREE BOOK
page 2️⃣0️⃣

081-04-49-32-15

*Dedicated to ya sapwan*

*Special tnx to my people masoya masu ƙaunata Ako da yaushe🤝💅*

_____________-Akan ƙayataccen gadon shi ya shimfiɗeta tare da gyara mata konciyarta, kai tsaye toilet ya wuce tare da watso ruwa ajikinsa, koda ya fito saman sopa yayi kwanciyar sa bayan ya tofesu da addu'ar bacci..
Ahaka har bacci yayi awon gaba dashi ƙiran sallan farko ya farka, toilet ya wuce yasakarma kansa shower tare da ɗauro alwala, darduma ya shimfiɗa tare da ɗaukar Alqur'ani nafila yayi raka'a biyu, Kur'ani ya ɗauka yasoma karatunsa cikin ƙira'arsa mai kyau mai daɗin sauraro, jin ana ƙoƙarin shiga sallar ne yasa shi tashi tare da ƙarasawa gaban gadon,

Ɗan bubbuga gefen gadon yayi tare da ƙiran sunanta in slow voice, ɗan juyawa tayi tare da wani irin juyi kamar zata faɗo cikin azama irin ta matan gaske yayi saurin tarota, tare da zaunar da ita

"*JADDERH*" yaƙira sunanta cikin wata irin sillent voice ɗinsa kitashi kiyi sallah

Ahankali tashi ga ware idanunta harta sauƙe ganinta tsabb, a cikin ƙayataccen ɗakin maleek ɗin saurin ƙara ware idanunta tayi,ɗan ganin ɗakin da take da sauri kuma kamar wacce aka tsikara ta miƙe cikin al'ajabin mene kuma ya haɗata da ɗakin maleek, ahankali kuma komai daya faru ya fara dawowa cikin braind ɗin ta tasan dai kallo kawai sukeyi, saita farajin barci daga nan kuma bata sake sanin maiya faru ba,

Ahanzarce ta miƙe miƙe tsaye tare da nufar bakin ƙofa handle ɗin ɗakin ta tura tana ziri ƙyawawan ƙafafunta xuwa cikin tanƙamemen falon nashi, kai tsaye ɗakinta tanufa toilet kawai ta shige alwula ta ɗauka tare da tura dogon shimar ɗin ta na sallah...

Bayan idar da sallar nata Qur'aninta ta É—auka kamar yadda ya zame mata sabo tashi ga rera karatunsa cikin muryanta daÉ—i

Ganin garin yayi haske sosae hakan yaÉ—ata aje Alqur'anin ta nufi kitchen domin sama musu abinda zasu yi kari

Agurguje ta haɗa musu abu mafi sauƙi ganin kamar tana naiman makara

kan dining table tajere masa nashi ita kuma ta nufi ɗakinta da plat na abincin nata , tura handle ɗin ƙofar nata tayi tare da mirza ma ƙofar key tana barin key ɗin ajiki, ahankali tashi ga cin abincin ta cikin kwanciyar hankali
Bayan ta kammala kuma taje toilet tayi brush, saman lafiyayyan gadon ta tafaÉ—a tayi konciyarta...

*MALEEK*

koda yadawo bai ganta aÉ—akin ba shoulder É—insa yaÉ—aga alamun baida meshi ba,jallabiyan jikinsa ya zare dare da komawa saman gadon yayi konciyarta

11 dot yatashi toilet ya shige aƙalla yaɗauka sama da 30 minute bai fito ba, kana ya fito yashirya kansa cikin kakansa sky blue denim jacket ya ɗaura saman kakin nasa, kai tsaye wajen shoesrug ɗinsa dake cike da takalma kala kala ya nufa wani haɗaɗɗan white sneakers shoe ya ciro haɗe da sanyawa aƙafarsa, cikin falon yanufa kai tsaye dining table yanufa ganin an shirya abincin kamar koda yaushe,......Zama yayi yafara ɗiban gara kamar yadda ya saba har wani kumshe blue eyes ɗin da yakeyi tsabar abinda yake i nayi mishi daɗi......Still haka yaci gaba da cin abincin sa aƙalla yakusa ɗaukan 15 yana ƙaryawa!¡!

*Kashim baba*

After like 30 minutes haka suka shirya meeting ɗin gaggawa cikin wani haɗaɗɗan building mai haɗe da wani ƙaton hall acikinsa , coutions ne acikin sa na alfarma wanda hall ɗin yaji kayan more rayuwa, ko ina stainding A/C ne manner a wurin sai sanyayyar ƙamari da kuma fitar numfarfashin jama'ar da wurin ya tara ne ke tashi

meeting sukayi me sunan meeting Dan har wajajen sha É—aya rana sunanta daman kulli da warwara, ahaka har suka sami mafita kana kowa ya kama gabansa.

Relaxing Hajiya kubba tayi akan bed tana juya maganganun da sukayi da ita da aminiyarta

Yazama dole awannan karon nufi to a ainihin mu lubna domin naga wankin hula na naiman kaimu dare, konace yana naiman kaimu domin Ni tun tuni nadaÉ—e da gamawa da abu É—aya saura É—aya
Chapter 14 · 0% Book details