← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 45

Sashe 18

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Garkuwa kuwa daya gama jin komae domin a loƙacin suna cikin magana da itane, tama manta da cewar magana suke yi da garkuwan inda yake tabbatar mata,idan harta kwantar da hankalinta to kuwa ƴarta zata baiyana gareta Nan bada jimawa, sammmm ta manta dashi....
Cikin wani irin matsanancin tausayinta daya daɗe yanajine yaji zuciyarsa da kuma ƙaryewa, saidai kuma kasancewar soldier ne yasa shi ƙasa baiyana rauninsa akan fuskarshi.....
"Insha Allahu zanci gaba da zamewa AYUSH ABDULPHATA OMAR garkuwa harya zuwa ƙarshen numfashina na ƙarshe a duniya"
"INAS0NKI AYUSH"

"I CAN'T LIVE WITHOUT YOU AYUSH"

YafaÉ—i hakan cikin wata iriyar sassanya murya

Tofa waikam
Menake shirin gani kutayani dube ƴan terms MALEEK da kuma terms na JADDAH😊😊🥰

Dankari wannan shi ake ƙira da uhummmmm

Shin wanene GARKUWA?

Shin wacece AYUSH?

Shin acikin yaran MALEEK wane yabasu kashim baba goyon baya?

Shin wane irin mataki ne kukega su Kashim baba zasu É—auka dangane da MALEEK

Nima kuma gashi dare yayi dan haka

Duk kubiyo *Ammey laylerh* danjin yadda zata kaya

More comment more typing esheeeeee😌

*INDO ADO {MAI UNGUWA} ki nuna Khadijah Sulaiman ƙaimi yaudai kammmm sunanta ya tabbata a cikin littafin KAREN BANA

Khadijah Sulaiman ƙaimi jinjinar ban girma tare dake da ahalinki baki ɗaya Allah yaci gaba da haskaka rayuwanki cikin aminci farin da tarin nutsuwa😌😌
*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH
*Ammey laylerh*

Page 2️⃣5️⃣

08104493215

_________"I CAN'T LIVE WITHOUT YOU AYUSH"
"I am myself I don't know What kind of s0 do I do AYUSH"
"I just know that I love you with all my heart and soul AYUSH"
"God willing, I will continue to take care of you , as a mother cares for her child,This is my promise"I became a SHIELD" haka dai MALEEK yayi ta sambatunsa tamkar wani zararre, kafin ya kuma ya zare p-charp da kuma facemark ɗin take lulluɓa da ƙyaƙƙyawar fuskarsa,....MALEEK taufiq kenan wanda yayi alƙawarin zamowa AYUSH ABDULPHATA OMAR garkuwa na har gaban abadan,

JADDAH

Cikin magagin barci take buɗe kyawawan idanunta wanda suka ɗan sirka hasalin blue ɗin da suke daaa, ganin kamar garin yaɗanyi duhun magribne yasa ta ƙara wara manyan idanun nata tana dirowa daga kan lallausan gadon nata,
slippers ta zura ta shiga toilet ta É—aurayo bakinta, tana nufar cikin falonsu direct kuma kitchen ta nufa cikin sauri sauri tashiga haÉ—a musu lafiyayyan girkinta.
bayan ta kammala kimtsa komai loƙacin anata ƙiraye ƙirayen sallah, ɗakinta ta koma tashiga wanka tare da ɗauro alwula doguwr rigar material ta saka baƙi wanda suka amshi ƙyaƙƙyawan surar jikinta, sallah tayi saida ta bari akayi sallar isha'i kana ta miƙe tafito falon nasu..... tamkar tare suke atare suka sanwo ƙafafunsu cikin makeken falon, kallon kallo aka shiga tsakanin JADDAH da MALEEK, ji yayi tamkar wani abu na ɗibansa zuwa gareta, sai kuma yayi saurin ɗauke kansa daga gareta yana ƙarasa shigowa cikin falon,...

Cikin sassanyar muryanta ta furta

"Barka da zuwa Ya MALEEK"

Kansa kawai ya kaÉ—a mata yana shigewa cikin bedroom É—in sa

Cikin hanzari ta shiga jere musu ƙayatattun fulasanta wanda ta ƙayata da lafiyayyun girkinta mai ɗan karan daɗi akan dining table, tana shirin barin falon taji sauƙar muryarsa a tsakar kanta

"Ina zakije"
"Bakiyi sarving É—ina ba kuma"

Cikin gadara da nuna zallar isa ya faÉ—i hakan yana É—auke kansa daga kallon ta

"Dama zantafi É—akine barci nakeji"

"To dawo kizauna "
"Ba yanzu ba"

Simi simi ta dawo da baya cikin falon ta shiga sarving nashi, "zauna" ya faÉ—a yana nuna mata kusa da inda yake zaune

Ahankali ta zaune tane kame kanta da tattara nutsuwarta guri guda, plat ɗin abincin data zuba mishi ya turo mata, kanta ta ɗago ta kalle shi ganin shima kallon nata yake yine yasata sunkwi da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, shi kuma ganin bata kalli ko inda flat ɗin abincin yake bane yasa shi ɗago da haɓarta,...yana zubawa fuskanta idanunsa masu kama da madara wani irin murmushi ya saki ganin muguwar kamar dayagani tattare da matar ɗazun da kuma AYUSH ɗin nashi,sakin fuskar nata yayi spoon ya ɗauka yana tsakura abincin kai tsaye bakinta ya nufa dashi, jadda sororo tayi tana ganin ikon Allah yau kuma dame yazo abinci a baki bakinta kuma, kawar da fuskarta tayi tana kallon wani gefe na daban......
"BuÉ—e idan kinganta kallon nawa"
Shima yafaɗi hakan yana kawar da kansa wani gefen daban,........ganin babu yadda zatayine yasata buɗe ɗan ƙaramin bakinta ya fara bata abincin a bakinta, shi kuwa cennnn ƙasa ransa faɗi yake keɗin ƴar amanatace keɗin amanatace AYUSH ABDULPHATA OMAR har gaban abada abadan abada zanci gaba da kulawa dake tare da haskaka rayuwanki nine zanzamo haske agareki AYESHA!...you are everything to me, I am your everything AYUSH, baisan ya ɓata loƙaci harhaka yana zance da zuciyarsa ba saida yaji tayi gyaran murya sannan tace "Ya MALEEK na ƙoshi, kaina kasamu kaci ko kaɗanne" kai ya gyaɗa mata sannan ya zuba wani abincin ya fara lodama cikinsa lafiyayyan kunun gyaɗar tada saba masa dashi kamar kullum ya tsiyanyo daga cikin ɗan ƙaramin plask, kamar koda yaushe ƙamshin lafiyayyan kunun ne keta faman tashi haka yashiga sipping kunun shi yana sha har wani irin lumshe ƙawawan idanunsa yake, tabbas yayi mamakin iya girkinta shiga idan aka ɗauke girkin ammeynsa to kuwa wannan shine nabiyu acikin jerin abinciccikan ɗaya taɓa mishi daɗi har haka "I love you AYUSH no matter what I'm different" hakadai yaci gaba da shan Kunun sa har saida ya kusan shanye cikin plask ɗin nan, sannan ya miƙe tsaye yana taku ɗaɗɗai saman sa yanufa kai tsaye ransa fessss...

JADDAH

Ganin yabar falonne yasata miƙewa itama tana faɗin "ya MALEEK kenan Everything about you is different, MALEEK You are unique"
Sai kuma ta saki wani ƙayataccen murmushi tuna moment ɗin su na daren jiya...
Kwanikan da suka ɓata ta debe takai kitchen tawanke abinta direct ɗakinta tawuce daga ganin tsananin zafin da akeyine yasata watsoma jikinta ruwa, wasu Mayun kayan barci masu kaishi da tushi tasanya wanda suka kwanta luff ajikinta kana suka bayyana ƙyaƙƙyawar halittar jikinta, turaruka masu daɗin ƙamshi tashiga kullawa jikinta gashin kanta ta haɗe wuri guda ta fakeshi da wani mitsitsin jan riboms dan danan ɗakin nata yaɗauki wani irin sinadarin ƙamshi na musamman, saman gadonta ta faɗa tayi kwanciyar ta hankali kwance...

MALEEK

Yana ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin sa toilet ya shige yana sakarma kansa shower kafin kuma yayi full wa kansa ya fito ƙugunsa ɗauke da towel ɗayan hannunsa kuma wani mini towelne yana tsane gashin kansa dashi wanda yayi luff luff sai sheƙin ƙyau yake fitarwa gaban wadrobe nashi ya nufa ɓangaren ƙananan ƙayansa yayi, wasu pygmas masu ƙyau da ɗaukar ido ya ɗebo kalan ruwan sararin samaniya saida yagama feshe jikinsa da turaruka masu azabar ƙamari da wani irin daɗi mai sanya nutsuwa acikin zukata kayan yasanya ' a jikinsa yana barin bedroom ɗin nasa baki ɗaya......

___________________________
ADAMAWA
__________________________

Saida tayi kukanta cin ƙarfinta kafin ahankali kuma ta miƙa tana nufar bedroom nata, wayar ta ta ɗauka tana lalubar wata number wacce
Aka rubuta AUNTY NIMRA YAHYA wacce dukkan alamu suka gama bayyana cewar numbern bata Nigeria bace, Calling numbern tashiga ringing wayan tafara Amma ba'ayi feeking call nata ba, tasan dama bazata taɓa ɗaukar ƙira dagareta ba
Saidai ita taƙirata haka suke dahaka suka saba tana wannan tunanin ne kuma taji ring ɗin waya ta tamkar daga sama jikinta na karkara da wani irin mazari takai hannunta tana answering call ɗin tayar nata, tanajin Muryar yayar nata ta wani fashe da wani irin kuka kukan nan mai ƙona zuciyar mai sauraron sa
"Wallahi Aunty NIMRA nagaji, nagaji aunty wannan karon kammm haƙurina yakai ƙarshe kawai zanyi tahowana sauɗiya wllh saidai OUM ANUM ɗin da HUBBIE sukasheni nasan zanmutu cikin salama kuma nasan na mutu a ƙasata ta gado AUNTY NIMRA kimin rai,.....
Sai kuma kawai ta zube sumammiya a wurin

AUNTY NIMRA kuwa jin shirune yasa gabanta faɗuwa domin tasan AUTAR tasu ɗan ƙaramin abu ƙadan saita sune musu haka take tun tana yarinya barinsa ita domin itace tamkar uwaa mahaifiya agareta, shakkar dake tsakaninsu ta musamman ce

"HABIBTIE"

" HABIBTIE"

"HABIBTIE"

Haka tashiga jera ƙiran sunayenta amma shiru
Saurin katse ƙiran tayi tana lalubo numbern Suffyan abdulphata Omar bugu ɗaya kuwa ya ɗaga yana faɗin "Auntynmu barka da dare ykk ya Saudiya nayi kewarka wllh " tun kamin yaji tayi magana yafara zuba mata Suratu

"Kanaji na Suffyan kaje ɓangaren friend naka tamkar akwai matsala muna waya da ita kawai naji shiru alamun ta somee kenan"

"Innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un"
"Innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un"

"Bara naje yanxun Nan Auntynmu!"
kitt ya datse ƙiran arikice yanufi ɓangaren friend ɗin tashi cikin wani irin tashin hankanli kadai ace Maganar ɗazuce tasa ta somee haka innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un...........

More comment more typing

Byyyyyyyyeeeeee masoya

Wallahi idan naga ruwan comments naku nayi muku alqawarin typing da safe insha Allahu

Takuce ammeyn laylerh akoda yaushe🫶🏻

Kutayani da adda'arku ƴan uwaa jinin jikina babu lafiya my LAYLERH😭😭😭😭*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*

NA MARYAM NASEER MIRRAH✨
*Ammey laylerh*

Page2️⃣6️⃣

08104493215

*Yau wannan littafin kaco kammmm sadaukarwa ne ga dukka wani masoyin littafin 🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*

*Haƙiƙa inajin daɗin comments naku😌🫶🏻😌*

~fateema lawan60
Ƙanwan teaba maman taeba
INDO ADO
Fateemah aliyu
~mls jamilat
Aunty apple Naaaaa
Ummah zahra
Saratu m aliyu
Al-ameern ameena
Jidderh
Mrs~😁 fatan kingane
*Aunty Salma {ammey laylerh maman twins insha Allah}*
*Ummie muhd NASEER*
*Hafsat musa maman mujaheet*
Da dai sauran wanda alqalummana bazasu faɗesu ba kungane😌😌🫶🏻 *l want to love you like no other you see me happily by the way God bless you and I am proud of you You are always motivated MIRRAH🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻❤️💕*
*************************

_________________________

Kada dai ace maganar É—azuce tasa ta somee haka, innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un......

Kawai friend ya shiga nanatawa cikin zuciyarsa,haka ya ɗin ga tafiya cikin sassarfa kuma a kiɗimeji yake tamkar ya sheƙe da gudu saidai babu damar hakan domin koda ina bayine rarrabe da kuyangu, babu damar da zai yi gudunne kawai gani tamkar bazai tadda sashen friend ɗin nashi ba....
Loƙacin daya ƙarasa asalin sashen nata kuwa ya shiga kwala mata ƙira

"FRIEND!"
"FRIEND!!"
"FRIEND!!!"
Chapter 18 · 0% Book details