← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 45

Sashe 38

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

=================
Cikin tsananin tausayin yaran nasu ummie da ammey,suka nufi wurin yaran nasu. ammey ce tayi saurin amsan ayman tana haÉ—e shi da qirjinta, jin sai faman shan zuciya yake ne, yasa Ammey nufar wurin jadderh wacce take rungume cikin maleek har yanxun.
Cikin muryarn tausayinta ammey tace mata "amshi Ayman ki bashi abincin sa Ya sha, da dukkan alamu abincinsa yake da buƙata". Hakan ne yasa maleek zare ta daga cikin jikinsa tare da wuce su cikin hanzari dan kada su fuskanci halin da yake a ciki.
Ummie ce ta amshi ayman tare da riƙo kafaɗun jadderhn su kayi cikin parlourn, a kujerar farko ammey ta zauna tana nunama jadderh da ummie wurin zama kusanta. Gaba ɗayansu zaman sukayi jadderh tana zaro mama dan bama ayman abincin sa, tamkar irin wanda ya shekaran nan bai samu abuncinsa ba, haka ya kaima nonon uwarsa cafka, cikin shogoɓar data zame mata jiki, ta callara qara, tare da faɗin
"wash ammey nonona"
gaba ɗayansu kuma sai ta basu dariya da tausayi duk loƙaci guda, tabbas zataji zafi dole. Ace tun safe rabonsa da abincinsa, ay dole taji zafin tsotson.
Suna Nan zaune har maleek ya sauƙo cikin jallabiya, kai tsaye masallaci ya nufa tunda yaji ana qiraye qirayen salla, suma kai tsaye miqewa sukayi tare da cikin ɗakin domin gabatar da Sallah. Bayan idar da Sallah suka dawo palon ammey na shirin tafiya gida kuma tunda anga ayman ɗin. Tana sanya qafarta woje maleek na sanwo tashi ƙafar, Ganin Ammeyn shi na qoqarin fitowa ne yashi dakatawa, tare da ɗan rusunawa "Barka da dare ammey Naaaaaa"
"Barka" kawai tace masa domin tana da buqatar sanin komai daya faru ayau É—in.
Key na hannunta ya amsa tare da wuce wa gaba, ganin hakan yasa tabi bayansa dan sanin taka maiman abinda yake nufi ɗin. Tana shiga cikin motar ya mata key tare dayin reverse yana nufar bakin get ɗin gidan, cikin ƙanƙanin loƙaci ya kaita gidan. Suna faka motarsu motar Abbie na sanyo kai gidan.
Hakan yasa maleek dakatawa da niyar fita da yake a cikin gidan nasu, Abbie kuwa yana fitowa ya kafe maleek da ido yana kallon sa babu ko qafta ido. Ganin irin kallon qurillan da mahaifin nasa yake binsa da shine yasa, yaji gaba É—aya ya sare kuma bai kyautama mahaifin nasa ba, wajen kama matarsa uwar gidansa Hajiya lubna, cikin wani irin tsananin kunyan mahaifinsan yake qoqarin durqushewa Dan gaida mahaifin nashi. Cikin sauri Abbie ya taro shi tare da haÉ—e jikinsa dana maleek É—in, dan bayansa ya shigawa bubbugawa kafin ya É—an janye shi kaÉ—an yana faÉ—in.
"Tabbas kai namijin gaske ne YARONA! Imani da niyar gyara itace manufa yarona, irinku duniya take nema maleek. Ka sani shi marar jin magana sai ammasa hukuncin jaki! Domin kawo gyara acikin al'umma,dole sai wasu sunsha duka dole wasu sai sunsha jijjiga, kafin wasu su rauraya kayi amfani da damar da mahaliccin mu ya baka! Wajen kawo qarshen zalumci da azzalumai".

"Kamar yaya kenan"

Cewar ammey shi kuwa maleek.
Gaba É—aya duk wata jijiya mai rai a jikin maleek babu wacce bata motsa ba jin irin furuncin dake fita daga bakin mahaifinsa, duk kuwa da cewar harda matarsa uwar gidansa acikin manyan masu aikata laifukan.

Cikin haqiqa nin zallar tsagwaron zallar gaskiyar dake danqare acikin qirjin Alhaji taufiq, ya dubi tsabar idan Hajiya Aysha galadima yace mata

"Misali ace kece na kama da laifi, domin kawo gyara dole saikin fuskanci hukunci, daidai da laifinki daga wurina. To yanxun ke a ganin ki mai zaki É—auki hakan?"
"Gyara" ta faɗi hakan tana sauƙe ajiyar zuciya, dan Tasan da wani abu a qasa, tunda suka fara mata wannan kwanakwanar.

Murmushi Abbie yayi tare da faÉ—in "kin tabbata?"
"Tabbas na tabbata Alhaji"
"To kamar dai haka ne! Hajj LUBNA tana daga cikin miyagun qasurguman masu aikata miyagun Laifuka"
Yana kaiwa Nan yayi saurin wucewa cikin coumpaun na gidan nashi.
Tsaye take qam gaban maleek ta kasa koda kwakkwaran motsine, jin wani irin tashin hankalin da maganar ta Abbie ta sanya mata. Hakan yasa ta shiga jijjaga maleek cikin wani irin tsananin tashin hankali, take faÉ—in "mene haka maleek? Menene kayi kenan? Kana nufin matar ubanka ka kama, kakai kotu! To wanne dalalin?, Sabo da me? Duk bana ce a rabu da wancan maganar bane, taje ita da Allahn daya halicce ta ba MALEEK? Ashe ban isa da kai ba dama MALEEK" ta qarisa zancen cikin É—auke maleek É—in da wani irin gigitaccen mari. Wanda da ace badan kasan cewarsa tsayayyen soja ba da babu abinda zai hana shi somewa a wurin. Dan kuwa kyakkyawan marine ya samu daka Ammeyn nashi.
Hannunsa ya zira cikin aljihun jallabar dake jikinsa, tare da kuma sunkuyar da kansa qasa dan jiran ko Ammeyn nashi zata kuma É—aukar woni hukuncin akansa.
Kamar rugujin sauqar aradu sukaji sauqar maganar Abbie ta saman benen dake nashi ɓangaren, komai daya faru akan idon sane. Ganin kamar ammey na shirin qarama maleek woni marin ne yasa shi dako mata tsawar da zata iya rantsewar tunda suke bai taɓa mata koda kotan kwacin taba.
"Kina qara kuskuren taɓa min yaro ranki sai yayi mummunan ɓaci,! Tunda baki san daidai da rashin daidaiɗinba AYSHA, meye laifin MALEEK dan kawai aikinsa ya kawoshi gareta? To kisa aranki koda ce ke ko da kuwa nine to tabbas irin wannan abun da MALEEK TAUFIQ yayi shine daidai, kuma shine hukunci na gaskiya bawai zalumci ba! Kina Nan kamar wayayya amma anbi dare anbi rana ana neman ruguza miki farin cikinki kota halin qaqa"
daidai loƙacin ne kuma ya ida sauƙowa qasa xuwa inda ya bar su ita da MALEEK ɗin da hannu ya nuna ta yana faɗin.
Chapter 38 · 0% Book details