← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 45

Sashe 4

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motar suka buɗe masa yafito jikin shi yana tsuma domin kuwa sungama taɓo maza. guns nashi dake ɗaure daga bayan wandon jikin sa ya zaro, yana harba ta sama fareti suka farayi suna kaiwa suna komawa sunfi ƙarfin muntuna talatin.
sunayi kafin kuma su tsaya cakkk! Ganin ogan nasu yanufi *CHIEF OF ARMY STAFF* (COAS).
Yana tafe cikin tafiyar nan ta mazajen fama mazajen gaske wanda ruwa,iska,tsanani, bayasa su gudu 'a filin yaƙi.

A jiyar zuciya chief of army ya sauƙe bayan yagama ganin komai ta glasses ɗin, ɗakin wanda aka seta da ctvv Camera na ɗakin, kan kujerar sa yakoma yana kuma sauƙe wata ijiyar zuciyar again.

****
Da sallama yashigo cikin babban Ofishin na chief of army.
cikin tsananin kulawa da jin yaron cannn ƙasan zuciyarsa yake amsa sallamar tashi, haɗi da nuna mashi wurin zama saida ya sara mishi kafin ya zauna, yana fuskantar ogan nashi wanda daga shi sai shi 'a matakin matsayi.
Hannu yamiko mar kamar kullum musabaha sukayi kamar yadda suka saba.

Fuskantar sa yayi da kyau kana yana numfasawa, tare da faÉ—in.

"lieutenant maleek taufiq kana ganin wannan karon bazaka bar wannan aikin, A hannu naba kuwa domin ta ko ina rayuwarka kewaye take da magautanka!! kana ganin wannan karon bazaka fito musu A mutum ba, domin ganar dasu kuskuren da suke son jefa kansu?"

Hannayensa ya miqar tare da lankwasa su, cikin girmama ogan sa kuma tamkar mahaifi yake, a wurin shi yace.

"Kabar komi 'a hannuna sir. Kamar dai kullum ɗin, kada ka manta niɗin horon kane dan me kakejin kamar zan gaza wannan karon,Fito musu A mutum kuma bawai shine mafita ba domin hakan bazata taɓa sanja rawa ba, Idan zaka kama tsuntsu mai wayo, tofa ta wuya zaka kama shi sir."

Ya faÉ—i maganar yana kallon wani gefe daban,ba kamarda da yake kallon chief of army ba.

Kurrrr chief of army yabi *MALEEK* da kallo, tamkar bai taɓa ganin saba sai yau ɗin yake more wa ganin sa.
Lalle sai yanzun yaƙara yarda ɗari bisa ɗari wannan shine renon shi. Ba kamar sauran ba, kai yashiga gyaɗawa yana tafa hanna yensa yana faɗin.

"weldone yarona haka akeson mazan gaske tamkar dai kai É—in nan"

Sajen fuskar shi yashiga shafawa haÉ—i ta faÉ—in

" wannan É—in *horonka ne* sir."

Chief of army kuwa wani alfahari yaji yana kama shi, na kasan cewar maleek A matsayin babban yaronsa wanda shine mafi kwazo a cikin sauran.

"Ka tabbata ka ɓoye mana *kashim baba* guri mai tsaro kuwa??"

murmushin da bai shirya zuwan shi bane ya subce wa maleek ,
yana jijjiga kai yace

" kadama kasa wannan damuwar A ran ka sir! Yana nan A wuri mafi killacewa da tarin tsarona, bana kowaba"

Cike da zallar alfahari da maleek É—in chief of army ya shiga faÉ—in.

"Da kyau yarona tashi kaje abunka, lallai naji dadin wannan maganar Allah ya dafama yaci gaba da shiga cikin lamuranka"
da amin ya amsa yana ƙara jin ƙaunar dattijon har ƙasa ranshi.

Fita yayi bayan ya tabbata babu wani sauran annuri dake saman ƙyaƙyƙyawar fuskarsa...

***
Darmanawa tudun fulani suka nufa, yana son anguwar saboda shiru-shirunta shiyasa yazaɓa zam, Acen a bakin get ɗin suka tsaida motocinsu , soldier ɗayane yafito da gudu ya buɗe musu ƙofar get ɗin. saida yabari motocin sun gama shiga kana yabi bayansu yana ƙara rufe Kofar get ɗin.

Basu shiga cikin gidan ba kasan cewar ana ta ƙiraye kirayen sallar la'asar, alwala
Suka shiga yi kana suka nufi masallacin anguwar.

Basune suka dawo ba sai bayan sallar isha'i domin sun ɗan leƙa gari.

Wanka yayi kana yaÉ—anyi wasu ayyuka nashi,
a laptop nashi sai wajen sha biyun dare ya kwanta bayan yayi sallar nafila haÉ—i da karatun Alqur'ani mai girma...asba ta gari lieutenant maleek taufiq.

Washe garin ranar.
Wajajen yamma suka ƙara fita, bayan sun dawo sunyi wanka wajen cin abinci suka nufa. restaurant kowa yabuƙaci abinda yake so, aka kakkawo musu, ogan kuwa babu komi A gabansa banda robar faro guda ɗaya, kanshi duƙe akan waya nashi yana ɗan ne danne.

Kamar ance cira kanka yakuwa cira ido huɗu sukayi..... Ai kuwa da wani irin mugun sauri yafito yana ƙara jan p-carp ɗin dake kansa, yana bin bayan mutumin da yabiyo abaya, Cikin motarsa yafaɗa mutumin hannunsa sarƙe da hannun wata budurwa, wacce da gani ba sai anbaɗa makaba kasan karuwarsa ce feenah, shima motar tashi yafaɗa yana mata key, aguje yaja motar nashi .
Shima maleek mara masa baya yayi
shima a gujen yabi bayan shi....

Gudu suke tamkar wanda suke gudun barin duniyar.. kiiiiiiiiiii motar maleek yaja wani uban birkin da baiyi niyar ciba.
Maleek ya taka ganin kamar mutum ne ya bige.

Muje zuwa yanxun aka fara duk wanda yabar wannan daddaÉ—an labari shi yayiwa kansa
Domin babu ruwan
*MARYAMA ƳAR NASEER*

*Haƙiƙa bana da bakin gode muku masoya littafin 🔥 KAREN BANA 🔥*

*Dubun gaisuwa ta ga*

*Asmeetar Headar*
(MAYAUDARI)
*Oum Shaheed oummuna* {INDA RAI}
*Mom sani Mommah Naaaaa 💃* (RIƘON SAKAINAR KASHI)
*Maman Inayah Aunty Naaaaa*
{ IZINAH}
*Gimbiya ayshu* (MATSALAR GIDAN MIJI)
*Teemah cool*
{A SANADIN WAYA}

*Fateema special writer* (Haƙkin mu)
*Aunty Sajida Niger* (Æ´ar mahaukaciya)
Da sauran marubutanmu ubangiji yaƙara bamu ƙwarin gwiwa a koda yaushe...

*My Real fan's*

*MLS Jamilat*
*INDO ADO 💖* {Mai unguwa}
*Zeey Abba*
*Auntu bilkisu*
*Aunty fareeda* (maman ZEEY)
*Aunty Hafsat* {maman Hafsat ikram}
*Aunty Hajiyalle* (maman Dee)
*Sister Lubna* nagode da ƙaunarki gareni
*Hajjo*
*Oum Nihal*
*Aunty fateema*
*Maryuda usman* (maman Najwa)

*Kune duniyar MIRRAH ✨ YAYYENA*

*Yaa Yaa Nura* (al'idgham)
*Yaa yaa Habeeb* {Captain HABEEB tiktokers}
*Uncle bash Gusau*
*Yaa yaa Al-ameen Naaa* (yaya ameern Naaa) *ehhhhhhhhh shine mai bani ciwon kai 😔*

*Sadaukar mebi takace ƙanina Rabi'u bapper* *Real tiktokers*

Shering and comments fisabilillah👏🏻

Yawan comments naku yawan typing ehammmm

Takuce
*AMMEYN LAYLAH 🫶🏻**🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*

Na MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah🫶🏻*

FREE BOOK
Page 6️⃣

081-04-49-32-15

*DUK TSANANI KADA KAZAMTO MUTUM MAI S0N KANKA 'A RAYUWA👌🏻*

*ITA NASIHA BAWAI, FAƊA BANE , IDAN ALLAHU YABAKA MAIYIMA NASIHAR, TO KA GODEWA ALLAH SANNAN KA GODEWA SHI WANNAN MUTUMIN DOMIN KUWA MUTUM NESHI GUDA 'A CIKIN RAYUWAR KA*👏❤️

*MARYAM NASEER GARKUWAR MUSULUNCI*💪🏻

********
Fitowa yayi domin ganin miye ya bige haka?. matashiyar budurwace kwance a ƙasa ta riƙe gefen cikinta da hannun ta, sanye take cikin kayan islamiyya ruwan toka, Can kuma gefe ɗaya jakar islamiyyar natace daga gefe.

Wani irin dafe kai yayi ganin kamar abin harin nasa yana S0n ɓacewa ganin sa.
yi yayi kamar ya koma cikin motar nashi sai kuma yaga kamar ta motsa ƙafarta.
saurin juyowa yayi yana ƙara ƙurewa kallonta, dake mutum ne shi da samm, baya taɓa barin nauyin wani akansa,
duk da dai kasan cewar baya ne ta bashi sammm baya ganin fuskar ta.. Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin babu motar da yakebi babu alamunta,
Wata iska ya furzar mai zafin gaske haÉ—i da kaiwa iska naushi.

Saurin zubewa yayi akan ƙafafuwan shi yakai ɗurƙushe gabanta.

"Mena miki baiwar Allah? da kika zaɓi shigowa rayuwata a irin wannan loƙacin! na farautar abin hari na.

Inaaaa ita kuwa baiwar Allah bata masan abinda yake faruwa ba

Ciilak ya É—auke ta, yana danna remote É—in dake hannunsa
wangale wa but É—in yayi, shi kuma ya cillata ciki tare da jakar islamiyyar Tata.
Zagayawa yayi gaban motar nashi yana shiga da sauri, key yawa motorn kana ya sauya akalar tafiyar nashi daga bin maharin nasa, ya zuwa wata kwanar ta daban.. Privete hospital mafi kusa yanufa da, ita
A gaggauce likitoci suka amsheta sunayin emagency room da ita, safa da marwa kawai yake famanyi shi kaɗai, Bai taɓa dana sanin rashin yaransa kusa ba irin yau ganin duk wannan abin bazai kaishi bane, yasa shi nufar famfunan harabar ƙatuwar asibitin, don yin alwular magrib dayaji anata kira.
gaba ɗaya sai yanxun ya lura da irin kallon da gaba ɗaya jama'ar asbitin suke binsa dashi. saurin kallon kansa yayi yaga wandon kakin sane Ajikinsa sai kuma baƙar t-shert kansa ya laluba yaji ba p-carp ɗin akan shi, saurin tunowa yayi ai yariga da yabarta a cikin mota...

"kallon na miye haka kuma?"
yafaɗa ƙasa ƙasa.

Su kuwa jama'ar wajen kallo kawai suke morewa gani.. ganin dai tabbas
lieutenant maleek taufiq general neeee. tsaye agaban su.
Wanda suka saba gani jikin jaridu, television's , wanda kullum basa gajiya da kallon irin jarumtarsa ne, yau tsaye gabansu yasa wasu fara É—aukar sa 'a photo ba tare da ya ankare da hakan ba, saurin dawowa hayyacin sa yayi ganin kamar hasken Camera yake gani akan sa.
Saurin ƙarisawa gurin famfunan yayi yana ɗurƙusawa ya fara alwular bayan ya tattare hannun rigar sa.

Cen gidan malam Abdullahi rano kuwa. ganin shiru shiru har doshin magrib *JADDAH*. Bata dawo gida bane yasa hankalin su. Ya fara tashi ganin loƙacin sallah yayi ne yasa Malam Abdullahi nufar masallaci, gwiwa a sake yanajin kamar wani abu yana shirin faruwa da shi da rayuwar sa.

Ummey ce zaune saman darduma da tasbaha a hannunta tanaja dana adda'ar allah ga baiyana mata yarinyar ta cikin aminci.

Da wani irin gudu basma tashigo gidan,
bayan idar da sallar magrib malam yake shaida cikiyar ɓatan jaddan, shine taji
Wannan daliline yasata shigowa gidan a guje a hargitse kuma, tana zuwa ta zube jikin ummeyn jaddan tana risgar wani irin kuka mai ban tausayi, da karya zuciyar mai sauraro..
"Ummey wallahi shin nee! Shi nee!! Shine ummey"
ta faɗa tana wata iriyar sheshsheƙar kuka.

"Ke basma tsaya! dakata nace waye shi É—in? wanene dan uban waye? Ki nitsu kimin bayani basma"

Cikin azabar kuka ta shiga faÉ—in.

"Ummey saida nace babu ruwan ta dashi!, amma taƙiya dan kawai ya mareta, shine ta rama dama yace saitayi dana sani, kuma saiya wulaƙanta ta yace"
" Innalillahi wa'inna ilaihir, raji'un"
ummey ta shiga mai mai tawa tare da malam dake tsaye tun É—axun amma basu san da zuwan sa ba.

********
"Shin wane wannan mutumin shi kuwa? Mai baiwar Allah kyauta daga Allah ta masa, yanemi cutata mata har haka?"
Cewar ummie dake share hawayen dake ta faman zarya, akan saman kuncinta.

A cen asbiti kuwa bayan idar da salla ya koma gurin likitan, domin jin yadda akayi dame jikin.
Chapter 4 · 0% Book details