← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 45

Sashe 40

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

God is always the thing to be thankful for, and to you we extend our issues.
Allah ka iya mana badan iyawarmu ba🤲🏻🙏🏻

********************************
Washe garin wannan rana, haka gaba É—aya labarin nan ya karaÉ—e social media, duk inda ka wuce zancen ne kawai ke faman tashi agarin na Abuja.
Kafin kace me kuma gaba É—aya duniyar yanar gizo taci gaba da haskaka fuskar, TAUFIQ MAI NASARA mahaifi ga maleek wanda yake a matsayin Chief of army.
Kana kuma wanda akafi sani, da shahararren É—an kasuwar nan na sarrafa motoci.
Wanda wani dalili nashi yasa bai taɓa baiyanarma duniya matsayin saba, yace ba suna ko matsayin yake da buqata ba, sabo da girman Allah yake komansa, wannan dalili yasa kowa yake ma Chief of army staff GENERAL ABDULLAHI BELLO makama.
Kallon shugaban sojojin Nigerian, wanda dukkan wani tsarin abubuwan dake gudana kuwa Alhaji taufiq mai Nasara shine ja gaba,kuma ragamar wannan tarin nasarorin da suka samu.

***********
Shi kansa Alhaji taufiq ya girgiza loqacin da ya gama kammala kallon gidajen talabijin É—in da suka wannan bin nannen tsohon sirrin nasu.
Shi kuwa mai girma Abdullahi Bello makama yayi hakan ne dan nuna halaccin sa ga shugaban sa. Wato taufiq mai Nasara uba ga yaro mafi qazo acikin tafiyar rundunar sojojin Nigeria baki É—aya.
Cikin zallar abinda yake yake zuciyar sa na alkhairinsa ga mamallakin, wannan jigo kuma jagora yaci gaba da bayyana ma duniya waye Alhaji TAUFIQ MAI NASARA.
Adalin shugaba

Gammmm ya rumtse idanunsa daidai wurin da GENERAL ABDULLAHI BELLO makama yake faÉ—in.

"Tabbas irin ka DUNIYARMU take da buqata generally TOUFIQ MAI NASARA! Kaida yaronka irinku duniyarmu muke da buqata Aiki domin sadaukar wa al'umma Rayuwa!"
"AIKI domin sanya ma zukatan bayin Allah nutsuwa!! Aiki da ayyuka domin sadaukar da tasu Rayuwar wa rayuwar al'umma!!!, Shin mene za kuce game da waÉ—annan bayin Allahn?, Ku dai duba rayuwarsu! kudai duba irin sadaukar warsu gareku bayin Allah, MATARSA UWAR gidansa uwar Æ´aÆ´an sa tsare a kotu, tare da..

Cikin wani irin zallar abinda ɓacin ran da ya daɗi bai shimfiɗama fuskar nasa ba, ya miƙe tsaye tare da fincike gaba ɗaya wayarin na plasma ɗin parlourn nashi, inda ammey take zaune ta kasa koda kwakkwaran motsine, cikin fusata ya fice a parlourn baki ɗaya yana barin gida baki ɗaya, kai tsaye tashar da yasan suna kan haska bayanan da GENERAL ABDULLAHI BELLO makama ya nufi.
***********
Da qarfi ya janye general abdu makama daga gaban abin haskawar, ya fara magana cikin ihu da qaraji.
"Kana tunanin abinda kayi shine zai sanya tarin alkhairinka juyewa zuwa gareni MAKAMA?, To tabbas indai ta haka ne ba zai taɓa karɓuwa ba! Ka taɓa ganin alkhairin wani ya juye zuwa wani? Ka taɓa ganin inda mai duka yake ma madaki sannu? Kamar haka ne" ya faɗi hakan yana haɗe hannayensa biyu, wata kwallar zallar tsagwaron Imanin daya kuma wanzuwa a zuciyarsa abdu makama ya share, tare da bin bayan generally TOUFIQ MAI NASARA daya kama hannunsa dan barin wurin baki ɗaya.
**********************
Gaba ɗaya mutane kuma sai jikkunansu sukayi sanyi qalau, vp ɗin take zaune a office nashi kuwa wani irin hawayene masu zafin gaske sauƙo masa, bayan hannunsa yasan ya share hawayen tare da faɗin "Alkhairin Allah ya tabbata agareka tare da Ni'imominka da tsarewar ya Allah! Allah kaci gaba da shiga cikin dukkan al'amurran wannan bawa naka"
A inda yake yaci gaba da zama dan yama rasa mene zaiyi taka maimai, shi yasan waye wannan bawan Allah, kana shi yasan irin tarin ayyukan alkhairinsa ga al'ummar Musulmi.
Tabbas shima yana son yayi koda kwatankwacin irin abinda wannan bawan Allah yake aikatawa na lada.

***************

Zaune suke a babban parlourn ammey suna tattauna maganganun da suka gama kewaye duniyar yanar gizo, inda anan sukaji tabbacin banda 2 week's za'a yankema su Mommah hukunci, inda yaune jadderh ta cika kwana arba'in ciff da haihuwa, a yau din ne kuma zata koma adamawa, inda ammey ta naimawa jadderhn alfarmar maleek ya barta ganin gida.
Dake shima yana tsaka da ayyukan sane yasa shi barin ta suje cenñnn adamawar, ƴaƴan Hajiya lubna kuwa hankalin su idan yayi dubu miliyan toya tashi, jin mahaifiyarsu nada hannun acikin wannan manyan masu aikata laifukan, da aka garƙame.
Inda ba Anan abin yake Bama saida Alhaji taufiq ya kunna Cameran da maleek ya mannawa kowa acikin É—akinta tsakanin ta da Hajiya talatu nera, aikam sun qara shiga tashin hankalin ganin, iriyar rayuwar da mahaifiyarsu ta gudanar, inda Hajiya talatu nera ta shiga cikin taitayinta, lallai sai yau maganganun jadderh suka kuma dawo mata sabi fil a tsakar kanta.
"Indai har ahaka kika shimfiÉ—a rayuwar aurenki , to tabbas anci da rabon ki Hajiya, anyi amfani da damar ki an dama abubuwan da Allah ne kaÉ—ai yasan iyakar abinda aka dama É—in, kana ina baki shawarin idan zaki faÉ—i magana kika sanin yadda saqon zaigewa mai amshe ta, kika sanin zancen da zaki dinga faÉ—a wa jama'a"
Wannan maganganu sune ta dinga maimaituwa acikin RAI da RUHINTA, ai kuwa taɗau darasi na har abada, dan ita tunda take bata taɓa nufar kowa da mugun nufi ba, kawai dai bata da danne ɓacin ranta ne da kuma cutar hassada hassada dake damunta, da kuma qarincin ilimin addinin Islama data ke da.

A private jet ɗin maleek aka kai su ummie Adamawa, inda aka haɗa mata sha tara ta arziƙi.
Suna zuwa labarin yasha banban dan kuwa sun tadda woni sabon rikicin ne da tashin hankalin haukacewar Hajiya Laura, mahaifiyar Sufyan friend, inda sai tone tone da banƙato irin asiran data ɗin ga zabgawa abokiyar zamanta MARYAM ABDULJALAAL take.
Inda tace itace ta hana mahaifiyarta waiwarta itace itace kai komai ma itace sanadi, tsabar kunya da nadamar rayuwa friend qasar ma ya bari baki ɗaya, dan yace baima san da wanne idone zai kuma kallon Little momien nashi ba, inda mai martaba sarki abdulphata Omar yasa aka killace a ɓangaren guda dan ta girbi abinda ya shuka, dama ya jima da sauwaqe mata
Inda da magiya da naci da komai mai martaba ya yarda bisa jajircewar MARYAM ABDULJALAAL malam Abdullahi yake ma Hajiya Laura adda'oi, cikin hakuncin Ubangiji take samun sauqi, saidai abinda suka lura dashi shine bata iya magana ba kuma ta iya motsa ko ina na jikinta, loqacin da jadderh taje ganinta kuwa idan da abinda yafi kuka to tabbas tayi.
Gashi dai dukkannin waɗannan abubuwan data aikata a banza abinda take gudun kuma ya riga ya gama faruwa, yau gaya amma tamkar babu ita, yau gata amma gidan da dukiyar data kema duk yazam saidai gani daga nesa hanqoro NOOOOOh kuma, yau ga ƴar jaririyar daga wullar taso kashewa tun cikin mahaifiyarta, yau gata da nata jaririn itama cikin gata so ƙauna.
Tana son tayi magana amma babu bakin maganar, sai yawu yalala da yake zuba daga cikin bakinta mai azabar yauqi da warin masifa, adda'oi sosae jadderh ta mata haÉ—i da naima mata afwa wurin mahaliccin ta.
Don rama cuta ga macucu ba shine Nasara, ka barshi da Allah ma kaÉ—ai babbar musifa ce acikin rayuwarsa,dan idan mutum ya zalumceka kayi gaggawar ramuwa to kamar kayi kutsene acikin al'amurran Ubangiji, shi yasa kabar mutum ma da fitowar rana da faÉ—uwar tama kaÉ—ai isharace.

******
Two weeks later

Zaune suke a babban parlourn Alhaji taufiq.
Inda Cikin zallar hikima da tarin baiwar da ALLAH ya masa yace

"Nigeria wata qasace mai tarin tseko mai labarai cike da! , damfara da rashawa, inda mai qaramin qarfi yake wahala!, A hannun talauci da kuma yunwa.
To amma dai koma meye! namu ba tsokaci da qorafi bane, abinda muka sani kawai mu bada rayuwarmu domin TUTARMU taci gaba da kaÉ—awa, da kuma kawo qarshen zalumci wa qasata Nigeria baki É—aya, dama Duniya. Tabbas kaine tauraro mai haskaka wannan tafiyar MAKAMA! Dan haka"
" Prepare to answer your position forever and ever MAKAMA, God continues to be our privilege."
Cikin wani tsananin qaunar Alhaji taufiq É—in ya zube a gabansa, cikin zubar da hawaye yace..
"Ba irina qasa take da buqata ba! Ƙasar mu dole mazaje take nema irinsu MALEEK TAUFIQ!, Tsayayyen namiji mai aiki da rai da rayuwarsa mai burin zamewa 9j uba, uban data riga da ta rasa.
Tabbas maleek shine ya cancanci zama
International military bawai niba!, Duba Nan ka gani" ya qara faÉ—in maganar yana É—an kama Abbie wasu tarin takardu masu kama da files, cikin sanyin daya rasa daga inda ya sameshi ya amsa files É—in Yina dubawa.
Kansa kawai ya kuma yin qasa dashi,idan yace zuciyarsa bata motsa ba yayi qarya, yana ina? Yana ina hakan ta faru? Gaba É—aya wannan takardun na shaidar qarin girman maleek É—in ne. Inda suke É—auke da shaidar sa hannun sauran shugabanni da kuma sarakun musulunci, na sun amince MALEK The head of the Nigerian army.
Yana daga inda yake ya gaza koda kwakkwaran motsine sukaji gaba É—aya gidan ya É—auka Parade na zarratan mazajen fama, soja mar mari daga nesa soja birginar hankaka,
Gaba É—aya suna cikin gidan an gama shirya komai da tsara komi na qarama maleek girma da kuma girmamawa, inda gaba É—aya makama ne yayi wannan shige da ficen ayyukan, tabbas da sunso barinsa a matsayin da yake da, amma cikin kamala da tattako irin nashi, ya nuna sammm baya da buqatar hakan ga maza a gabansu.
Chapter 40 · 0% Book details