← Book details Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 45

Sashe 36

Karen Bana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ciki dariyar mugunta da sanin muguntar da suka É—ana masa suka shiga faÉ—in.

"Kada ka manta fa yanxun ba kai É—aya bane, kana ba ki biyu bane baku goma bane kuna da yawa, mafi soyuwa kuma É—an ka ayman, wanda muka seta Ranar mutuwarsa daaaaaa hhhhhhhhhh"
Suka shiga ƙaƙata dariya su duk.
Bai samu zarrar cewa komai ba aka yanke ƙiran kitt daga ɓangaren masu ƙiran.

Hakan yasa maleek komawa jikin rug É—in office É—in, tare da jingina jikinsa da kujerar, yana dafe daidai saitin zuciyarsa daya fara jin ta masa wani irin nauyi.
Cikin jin ya gaji ya kuma ƙosa wannan rana zato ya miƙe tsaye a fusace, tare da saka hannunsa na dama ya doka plasma ɗin cikin office ɗin, ai kuwa ji kake taratsatsa ta tarwatse. Gefin leɓensa ya shiga taunewa da qarfin gaske, ya cuta hannunsa zai kuma tarwatsa system nashi ne, Jawad ya shigo cikin office ɗin ganin a halin da maleek ɗin yake a ciki ne, yasa shi saurin dafe kafaɗarsa haɗi da cewa "haba maleek b a man mana ka nutsu, kana karanta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Ai kuwa nan dana ya shiga nanata kalmomin da Jawad ya shiga faɗa masa, cikin kudira ta Ubangiji kuwa ya soma jin wata irin nutsuwa na sauƙar masa.
Hannunsa Jawad Ya kama ya zaunar dashi, tare da fuskantar sa kana ya shiga faɗin "yanxun haka na riga da na gama dukkan wani shirin da kace na shirya maka! Sannan akwai ƙalu bale sosai tattare da hakan, amma kada ka damu Ni zanji da komai."
Cikin sanin irin aikin Jawad É—in agareshi ne yasa ya shiga kaÉ—a kansa haÉ—i da cewa " weldone" yana bashi hannu suka kashe..
Nan Jawad ya fice a office ɗin na maleek bayan ya damƙa masa wasu muhimman abubuwa.
Nan shima maleek ya miƙe tare da yin wajeee cikin gaggawa.
Kai tsaye motarsa ya shiga tare da mata key yana janta da wani irin mugun gudu na fitar hankali, gida ya nufa nan danan kuwa ya isa gidan cikin ƙanƙanin loƙaci.
Kota kannnn su jadderh baibi ya shige ɗakinsa cikin wani irin azabar sauri, domin dama yasan tarkon daya haɗa musu shi yasa cikin hamzari, yake komai tun kan burinsa yacimma haƙa.

Idan hankalinsa yayi dubu toya tashi yana son yau É—in nan ba sai gobe ba kama su kashim baba a hannunsa, cikin sassarfa ya faÉ—a É—akinsa tare da shigewa cikin clothes nashi rigar bullet nashi ya É—auko ya zira ajikinsa tare da wasu shirye shiryen sa, kamar kibtar ido yazo ya gimla su jadderh dake zaune a parlourn fuuuuuuuu ya fice a gidan baki É—aya, saida ya tabbatar ya gama Bama gidansa da kuma gidansu tsaro na musamman.
Motarsa ya kuma faɗawa tare da janta a 360 yabar gidan. Duk inda na'urar bibiyar dake nuna masa yake bi tare da shima da setawa su Jawad hanya, nan ya fara kurdawa cikin lunguna da saƙuna tun yana cikin garin na Abuja, harya fara barin cikin garin.

Daga cennn kuwa ɓangaren su kashim baba gaba ɗaya suna tare Dukansu, gaba ɗaya suma sun gama zama cikin target, domin ko yaushe wannan shegen yaron ka iya kai musu farmaki, shi yasa akoda yaushe suke kewaye da yaransu, gaba ɗaya suka shiga tattaunawa akan yadda za suyi da rayuwar maleek bayan sun gama kashe yaronsa a gaban idonsa, zasuzo suga yadda maleek zai yi bayan sun kashe jaririn yaronsa mafi soyuwa a gaban idansa!.
Hakan yasa suka shirYa sosai wajen farmakar maleek É—in.

Shi kuwa maleek cikin ƙwarewa yaci gaba dabin diddigin na'urar, haka ya dinga barin cikin garin yana kutsawa jeji, saida yayi tafiya ta fitar hankali kana na'urar ta tsaya cakkk daidai wani ƙaton kango, hakan yasa shi yin wani uban reverse daidai ƙofar mashigar.
Fitowa yayi cikin shirin Kota kwana yake kutsa kansa cikin gidan, nan ya dinga haɗuwa da nasu gaɗin su kashim baba da miyagun bindugu, aikuwa ya shiga sheƙesu tare da ɗebe makayan yana tattare su wuri guda, babu zato babu tsammani kawai su kashim baba sukaji qarar harbin bindaga hakan yasa a gigice suka miƙe, tare da yin settings kowa na abinda yake hannunsa.
Suna Nan tsaye sukaji ƙarar fasa ƙofar da maleek yayi tare da kutso kansa cikin wargajejen forlourn! Me zasu gani maleek ne tsaye hannayensa duka biyun riƙe da manyan bindugu hakan yasa su kashim baba sheƙewa da wata sheiɗaniyar dariya tare da tafa hannayensa, sai kuma yaYi wani irin fito fifitttt, Nan kuwa kan kace me gaba ɗaya yaran su kashim baba suka zagaye forlourn baki ɗaya.sai kuma sukawa maleek ƙawanya suka sashi a tsakiyar su, Nan suka Alhaji Atiku suka shiga ƙaƙatawa maleek dariya, tare da faɗin "Sannu jarumi, wai kai nan JARUMI ko? Hhhhhhhhhh yau qarshen ka yazo kazo a daidai dan yanxun hakan na tabbata yaronka yana kan hanya, da munso saimun kashe shi kana mu tura maka da gawarsa, bayan munyi raping nashi, amma babu komai ko ba komai zakaga yadda za muyi raping na jaririn ɗan ka akan idonka! Kaga kuwa dole ne yayi MUTUWAR AZABA da RAƊAƊIN FAƊEEE"
Hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh sai suka shiga ƙaƙata dariya Dukansu kafin kashim baba ya ratso ta tsakiyar taron tare da nuna maleek da bindiga kana ya shiga faɗin.
"IDANNNNNN🙊🙊🤣🤣🫰🏻🥰

Mai zai faru?
Idan yayi mene kenan?

Allah masani amsar
kunsan tana ina?😉

Tana Nan

*KAREN BANA*
👆👆👆🏻👆👆

🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
Na Maryam Naseer mirrah
*Ammey laylerh*

Page 4️⃣0️⃣

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
====================

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/B5h5bUBTy1SDjMGoQs7Yb1

*IDAN nagama dakai zanbi ahalinka,ɗaya bayan ɗaya na sheƙesu! sannan na aure matarka uwar yaronka ayman, waɗanda na tabbata sune rayuwarka MALEEK!"*

Wata iriyar razanan niyar uwar tsawa maleek ya bugawa Kashim baba, daya nuna kanshi da bindiga,
Wani irin kallo maleek yabi Kashim baba dashi irin dube kan nan, sannan ya naɗe hannayensa a ƙirji ya fara magana cikin dakewa da rashin tsoro
*"KAREN BANA* maganin *ZOMON BANA* sa shiru hana ƙara Hayaƙi NOOOOOh, Inkaji ana ƙi gudu to sa gudu ne bai zoba"
Gaba ɗayansu sun razana da irin tsawar da maleek Ya musu, amma dake suma shegun kansu ne, hakan bai hana Isa tanbuwal ƙarasowa gaban maleek ɗin ba.
Cikin tacewa a rashin M Isa tanbuwal ɗin Ya fara magana " Kai yaro iya bakinka! Kasan su waye kaka bugama tsawa haka?, To kada ka manta Kashim baba shine mijin matarka bayan ka sheƙa duniyar da ba'a dawowa! Sannan gwamnatin da kake taƙama dasu, mune Nan gwamnatin ba kowa baaaaa!"

Maleek ne ya buga masa tsawar data sa ya riqe kansa, sannan ya damƙi gefin rigar saya fara jijjaga shi cikin ihu yace, "Su wa ye ku wanda ya wuce dabbobi! Azzalumai!! Maciya amanar ƙasa!!!, Duk wanda ya qara magana ba tare da izininaba! Na rantse saidai uwarsa ta haifi wani badai shiba."

Ya faÉ—i hakan yana cilla Isa tanbuwal da qasa,wanda kansa yaje ya bugu da jikin ginin É—akin.

Ai kuwa duk loƙaci guda suka ja baya,ganin ran ƴan maza ya ɓaci a tsorace suka soma ja baya. Suna zare idanu jin irin uban worning ɗin daya gargaɗesu.

Cikin aro jarumta azama ranshi Kashim baba ya shiga tafa hannuwansa, "da kyau JARUMI Lallai jarumtarka ta daɗe tana burgeni. duk kuwa cewa kana sansani na kewaye da yarana, amma hakan baisa ka girgiza ba. Na gaishe ka UBAN AYMAN! To kasani a yau base GOBE ba Lahira zatayi babban baƙo, MAZA afara aiki"

Ya faÉ—i hakan yana sakin wani irin munafikin murmushi.

Aikuwa kankace me yaran nan suka yo kan maleek, hakan yasa maleek ja baya ya zama qafarsa, tare da jan wata uwar tunga. Nan sukayo kanshi haiqan da bindugu suka shiga fara harbawa maleek bindugu, aikuwa kankace me gurin ya turniƙe da qaran harsasai. Daidai Nan kuma ƙungiyar rundunar sojojin maleek suka kutso kansu cikin gidan. Aikuwa suma tu daga bakin qofa suka fara nasu aikin suma, kafin su kutso kansu cikin ɗakin Nan aka shiga fafatawa tsakanin yaransu Kashim baba, da rundunar sojojin.

Ganin yadda gaba ɗaya wurin ya turniƙe, kuma gashi sai zubar da yaransu akene. Yasa hankali Ibrahim nera tashi, hakan yasa ƙoƙarin fecewa daga cikin ɗakin.
Saidai bai sani ba yayi shuka a idon makwa domin kuwa maleek yana ankare dashi, kafin yayi woni yunƙuri kuma, maleek yaja rawanin daya naɗa ma kansa.
Tuni jikin Ibrahim nera ya fara mazari gudun abinda kake yazo, amma cikin dakewa yace " kanason wasa da rayuwar ka kenan?, Yaro ka tafi kabar Nan idan harba mutuwar wulaƙancin da yaronka zai yi kakeson gani ba. Kana Kasan Ni Ko waye! Kuma Kasan matsayi na na shugaban ƙasar ku".

Zuciyar maleek ce ta fara tafarfasa jin irin kalaman Ibrahim nera, wai ahakan ko kunyar kansa baiji ba yake ƙiran kansa shugaban ƙasa.

Ba tare daya iya control kansa ba, ya sanya hannu ya finciko shi ya haÉ—e sifes É—in dake tsakanin su ta hanyar haÉ—e jikinsa dana Ibrahim nera, baiyi tsammani ba kawai sai ganinsa yayi a gaban maleek. Yana huci tamkar zaki.

"Me kace?, Kace kai shugaban ƙasa ne? Kai yanxun ko kunyar kanka bakaji ba dan Allah? ku sani ba kowanne hadarine yake ZUWA da ruwa ba.
Kuna buɗe asibiti a mazaunin kyauta wa al'umma! Bayan kuma abin ba haka yake ba. Kuna da woni naku tsarin na daban akan bayin Allahn da basu jiba, basu gani ba. Alhalin kun buɗe asibitocin ne kawai dan kuna auna jinin mutum! Idan yayi daidai da jinin da kuke nema sai ku zuƙema mutum jininsan. Daga qarshe sunan mutum min mattace! Ku kuma kunsa mi abinda kuke soooo Koooooo"

Ya faɗi maganar ƙarshen cikin hargowa da amsa kuwwa.

Shiru Ibrahim nera yayi cikin bugawar zuciya sai rarraba idanu yake, ganin duk yadda hankalin jama'ar wurin ya dawo kansu, Nan ya fara muzurai yana ƙafƙafta idanu, ya TSOHON maye.
Cikin tsananin azabar sukar da zuciyarsa take cikine, naƙin bashi dama akan ya harbe su kashim baba a hannunsa, da aka ƙi bashi damane yasa ya fara magana cikin wani irin ɗacin rai yace.
Chapter 36 · 0% Book details