Sashe 93
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Tun suna saka ran ganin shi da wuri har su ka cire tunda har dare bai iso gida ba. Hatta Mommy da Baba Alƙali suna gidan suna jiran dawowarsa Amman sai bayan sallar isha'i a ka rakosa gida da jama'a da Security, ya na shigowa get sai Abu ya fara tashi da farko duhu ne ya mamaye ganinsa Yana shigowa suka kunna wutar gidan gabaɗaya a ka fara waƙan AJI IS A GOAL NAGERIA IS A GOAL NAGERIA IS THE GREAT AGAIN."
Gabaɗaya bakinsa ya ki rufuwa kayan ƙwallon nagerian ne ko a jikinsa, bai sauya ba abun da ya ba shi mamakin ganin duka yan'uwansa a waje ɗaya suna masa tafi, sai ga su Ummi sun jere a gabansa su Fati kuma suna jan wata igiya Bloons suka cika haraban gidan gabaɗaya.
Aji ya na dariya da mirmishi lokaci É—aya bai sani ba ya tsaya kawai ya kasa motsi.
Yana ta saka ido ko zai ga Mimi maman Maryama da Ibrahim, amman bai ganta ba sai da suka gama wakarsu sannan suka haÉ—a bakin wajen faÉ—in" Congratulatoon Aji In sha Allahu nan gaba kai za ka É—aukan ma Nageria kambun nasara."
Ya na ta mirmishi ya kasa mgana Mu'azzam ya je gare shi suka rumgume juna shi sannan ya dago ya na dukan kafaÉ—ansa Lokaci É—aya yana fadin" Thanks Bro."
Haka ma su Nasir ke rumgumansa ɗaya bayan daya suna gaisawa, har da Baba Alƙali ya na neman ya ramkwafa ya gaishe shi ya hana shi ta hanyar kai masa rumguma yana faɗin"Congratulation Son in low" ya amsa ya na mirmishi Dr ma ya kariso shi da Muhammad duka rumgume juma matan kuma ya karisa ya na kiran sunayensu su kuma suna gaishe shi, Mommy kuma ya duka ya gaisheta ta amsa tana faɗin"Sannu Allah ya sa albarka muna alfahari da kai."
Shi dai har lokacin bai ga Mimi ba kuma ya kasa mgana sai ya koma yana ɗaukan yara bayan ɗaya ya na dire su, Ummi ta maƙale sa tana faɗin"Abba.."
Shima ya É—aga ta sama yana faÉ—in"Uwata ta fi ta kowa."
Ammin É—in Mu'azzam ta tura baki kafin ta ce"Abba har da ni m maman taka ta fi ni?
Ta faÉ—a cikin shagwaba gabaÉ—aya a ka saka dariya ya juya ya na kallonta sauke Ummi ya yi ya É—aga ta sama yana faÉ—in"Haba Mamana ai ba wata sai ke? Sai ta washe baki kafin ta ce"Yauwa ka daina ce ma Ummi ta fi kowa."
Yana dariya yac e an gama Inna, Babangida kuma sai ya fara jan kafarsa yana faÉ—in"Abba ni ba ka É—auke ni ba?
Ya faɗa ya na wani haɗe fuska, domin kamar yadda ya ke kama da Aji a hallita haka ya diɓo hallayansa na zuciya da baƙin rai tun yana karaminsa.
Dole ya sauke Ammi ya É—auke shi yana fadin"My photocopy, My Baaba.."
Haka ya faɗa ya na jan kumatun Babangidan domin ya saki fuska, amman kuma ya ƙi sakin fuskar, sai ma wani ƙara dakuna fuska da ya yi, Nasir na dariya yace"Kamar uban kamar ɗan."
sai abun ya koma gasa ga gajiya a tare da shi sai da Mu'azzam da su Nasir suka zo suka raba shi da yaran sannan suka dumguma cikin gida Zuciyarsa na son sanin inda matarsa ta shiga .ya dai san ta tura masa wani gigitacen sakon da ya ke jiranta da safen nan, ta san haknee ta ɓoya ma ganinsa Ahalin da kishin ruwanta ya dawo?
Suna zuwa falo nan ma wani Decoratoin É—in ne Aji na dariya ya ce"Lalle yau rana ta ce."
Sai ya juya yana kallon su Nasir kafin ya ce"Ni na ga kowa amman ban ga matata ba, ina ta ke ne?
A hankali ya yi mganar, shi kuma Nasir da karfi ya ce" kana da rawan jiki ai za ta fito kuma za ka ganta"
Kunya yaji ganin har da su Mommy a wajen,sun zazzauna kenan Junior ya ƙi zama ya koma gefe ya harɗe alamun kamar ya yi fushi Bintu ta kira shi amman ya ki jin ta, sai Aji ya kalle sa kafin ya ce"Junior ta ho ka zauna mana"
Ya wani ƙara bata rai kafin ya ce"Abba ni ka ga kowa amman kamar ma ka manta da ni Alhallin kuma ni nre zan ga je ka na zama ɗankwallo."
Ya faÉ—a ya na nuna rigan jiknsa, ta Jc na Æ´an kwallo gabadaya falon a ka É—au dariya shi kuma sai ya kara fusata dole dai Aji ya mike ya je lallashi har ya hakura,.Shi ya yi masa raÉ—a a kunne ina Anty Mimi sai ya ja hannunsa ya ce bari ya kaisa wajenta afalon ba wanda ya bi ta kansu suna ta hiransu har suka shige ciki kowa ya bi su da kwallo suna kunshe dariya.
Junoir na shigar da shi Bedroom É—in ya kulle kofar kamar yadda a ka basa umarni ya dawo falo yana dariya .Bedroom É—in duhu ne amman sai tashin kamshin turare, ba ya iya ganin ko tafin hannun shi amman ya na jin Nlnumfashin Mimi a É—akin..
"My jan kina ina ne? Kinsan idanuwana ke kaÉ—ai suke mararin gani don Allah ki fito na ganki kafin na suma saboda zullumi."
Wal hasken ɗakin ya kawo. Yanaa juyawa baya ya ga kyakyawan matarsa da ba ta tsufa a idanuwansa ta ci riga da wando na White an Green bai taɓa mantawa shi ya kawo mata kayan ta tsuke har da p. Cap ta yi wani irin tsayuwan gayu har da farin takalmi covrer mai igiyoyi, galala ya tsaya yana kallonta ta ɗauro ga shinta ta baya har tsayuwan da ta yi abun kallo ne da sha'awa. Mirmishi ta sakar masa sannan ta ɗaga Hannunta sama ta zana love da hannunta duka biyu, sannan ta hura masa iskar Love ɗin zuwa gare shi lokaci ɗaya tana faɗin" WELCOME BACK AJIN MIMI."
Jikinsa har wani rawa yake yi wajen nufarta, kafin ya matso ita ta yi gudu ta faɗa jikimsa suka wani irin rumgume juna kamar za su maida junansu ciki, yana faɗin na yi kewarki Mimi ta na faɗin na yi kewarka Aji na, shinshinta ya ke yi saboda kamshin Turarenta ita kuma sai raɗa masa wasu zantuka take yi da suka susatar da shi ya nemi ya birkice mata dakyar ta kwace jikinta ta tura shi Tiolet ta tuɓe sa ta yi masa wanka karshenta itama cikin shower ya jawo ta, dole kafin a yi wannan wankan sai da a ka yi ta shagali da love sannan suka sake wanka suka fito suka kuma shirya a tare shi ya yi shigar shadda mai ruwan kasa har da Babban riga ita kuma ta saka lafaya a saman atamfar da ta saka, shi a koƙarinsa ya na son kaɗaicewa da ita, ita kuma tana gaya masa suna da baki a falo haka nan ya hakura suka fito falo sai tafi ya tashi khadi da Bntu suka rangaɗa guda, Hibba ta ce"Barka da fitowa Mr and Mrs Ibrahim Aji."
Suna ta fama mirmishi nan fa aka ba za manyan dardumai a tsakiyar falo a ka zauna nan fa su Bintu suka fara kai da kawo da abincin da snaks da nama, kaza tsire da sauran a baben sha ci, Walima ce ta Family domin taya sa murna Mimi ta haɗa a ka ci a ka sha ana ta hira da raha,bayan an gama an yi hotuna duk da dai dare ne da vedio bayan an gyara in da aka ɓata suka yi shirin tafiya gidan Mommy gabaɗayan su matan mazan kuma a Hotels za su kwana sai ga shi Aji na ba da umarnin har yaran gabaɗaya a tafi da su wajen Mommy yana bukatar hutu ne.
Nasir ya kallesa kafin ya ce"To Allah ya sa hutawar da gaske za ka yi?
Hararansa ya yi har yana ta ka masa kafa, Su Bintu suna dariya suka tarkata yaran har da Mu'azzan ƙarami, Akwai motoci ga direban yara har da shi a ka kira ya zo duk ya kwashe su sai gidan ya yi shuru.
Suna tafiya tun a falo Aji ya rike Mimi yana faɗin"Ki cika alkwari Mimi, ke fa kika ce min kin cika makil da ruwan ni'ima ni kawai kike jira." Gira ta ɗaga masa lokaci ɗaya tana kai hannunta wani wajen ai sai ya ƙara gigicewa dakyar ya bari suka isa bedroom suka faɗa kan gado, sai ka ce daran amarci sannan suka yi watsi da kayan juna. Kowa na nuna yadda ya yi kewar ɗan'uwansa.
Sai da suka samu natsuwa sannan suka yi wanka, suka koma suka kwanta akwai gajiya a tare da shi ya sa ta zauna tana masa tausa yana jin daÉ—i idanuwansa a rufe ya ce"Allah ya yi miki albarka Fatima Fatima mai zogale."
Ya faɗa cikin sigar waƙa ita kuma tana dariya, bakin ta har kunne farincikinta anan duniya ya gama samuwa. Auranta na shekara goma ta fuskanci ƙalubale ma su yawa da za ta ba da labari, ta kuma samu cigaban da za ta iya faɗa, tunda ga shi ma anan Abuja ma tana shirye shiryen buɗe wani shagon kaya take yi,sannan a bangaren sanin menene aure duka za ta iya mgana a haka sannan a bangaren sanin hallaya maza ma za ta ce wani abu, Ita za ta iya dukan kirji ta ce aure na da daɗi sannan in ka yi dace aure rahama ne sannan farinciki ne abin da ya fi daɗi irin ka ga mijinka tare da yayan da Allah ya baku tare, bayan duka gwagwarmayan da a ka sha a baya an fahimci juna ana zaune cikin farinciki in akasasin sa ya samu sai a yi hakuri da juna, ta fahimce shi ya fahimce ta sai kuma suka gina zaman su cikin yarda da Amana, duk da zamantakewa daman zo mu zauna ne zo mu saɓa, balle ita irin mijinta amman Alhamdulillah, Aji ya canza a cikin kaso mai yawa na hallayarsa ya sauya wasu saboda samun daidato da Miminsa.
"Tunanin me kike yi?
Aji ne ya katse mata tunani, kuma kafin ma ta ce wani abu ya saka hannu ya jawota jikinsa lokaci É—aya yana faÉ—in" In har ina kusa da ke, har abada baki ba tunani in dai ni ne kin samu har gangan jiki ba ma kan ba." Mimi sai mirmishi take yi cikin kunya shi kuma yana sake mata raÉ—a a kunne ta na zillewa, blanket ya ja ya rufe su gabaÉ—aya lokaci É—aya yana faÉ—in"Mu shiga cikin nan Fatima ta ba ni zogalen ta mai É—an karan daÉ—i."
Suna ta kyatatan dariya, Mimi ta ƙamkame Aji a cikin zuciyarta tana faɗin"Bismillahi da Alhamdulillahi duka a lokaci ɗaya."
*Tammat bihamadulillah*
*Nima na fara da Bismillahi zan ƙarƙare da Alhamdulillah. Nan na sauke alƙalamina daga rubuta labarin IDAN AN CIZA. Abin da na rubuta dai dai Allah ya haɗamu a ladan gabaɗaya, kuskuren dake ciki Allah ya yafe min, wataƙila akwai abin da bai yi muku ba, to ku yi hakuri akwai ajizanci na ɗan adam duk yadda naso na yi komai ɗari bisa ɗari ba zan iya ba, dole za a samu kuskure ta wani bangaren. Na gode kwarai bisa soyayyar ku gare ni, na gode bisa yadda kuka yi tururuwa wajen siyan wannan labarin Na gode kwarai Ubangiji ya yi albarka Amin.