Sashe 81
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hajiya bakinta yaƙi rufuwa har da ita a asibiti har kuma suka dawo gida, ta ɗauki Jaririyan ta saka albarka sannan ta kalli Mimi dake zaune gefen gado a cikin bedroom ɗin ta, wani katon Jug ne a hannunta Inna Zainaba ta haɗa mata tea bayan sun yi wanka ita da jaririyar. Sai ta ji kwallah ta tarun mata a cikin ƙwayar ido, Allahu akbar yau ga shi Binta ta yi aure har ta kai ga ganin ƴarta a duniya. Sai dai Kabiru baya raye. Burin shi kenan ya ga Binta ta samu kyakyawan rayuwa irin na kowa ta mace. Hawayen nata sai da suka zubo ta share lokaci ɗaya tana faɗin"Allah ya jiƙan kabiru. Allah ya cika maka burin ka Binta ta samu kyakyawan rayuwa mai cike da farinciki da kake yi mata fata."
Mimi ba sai hawaye ta tuna da Abin ta amman a cikin ranta ta na yi masa addu'an rahama da dacewa.
Su Mama da Anty duk suna gidan har da Mamansu Rukky da Bibi da Nafisan Nasir, Sai su Bintu da Walida da Mariya su Yaya Amina sun tafi kafin mangariba, Inna kuma daman tun a asibiti bayan an haihu lafiya isowar su Mama ta koma gida. Sai can bayan isha'i gidan ya watse a ka bar Inna Zainaba kaɗai sai mai Jego ta kasa zama sai kai da kawo take yi domin kula da Mimin wacce ta samu ƙari sai da a ka yi mata ɗinki tana bukatar shiga ruwan ɗumi lokaci bayan lokaci, Aji bai shigo gidan ba sai wajen goma suna tare da Nasir da makama yau kam bakinsa ya ƙi rufuwa bai taɓa tunanin haka a ke jin farinciki in a ka zama uba ba sai yau wayar da ya amsa na barka bai san adadi ba, Mu'azzam daman shi ya fara kiran shi ya sanar da shi Fatima ta sauka an samu wata maryama Mu'azzam ɗin ne ya rika gayama sauran mutane, har su Baba Ɗanjuma da rana sun je asibiti sun Duba Mimi da abin da ta haifa.
Itama ta bangarenta har sai da ta gaji ta amsa wayoyin mutane, bayan ta dawo hayyacinta na natsu daga gumurzun Naguda ita ai sai dai ta yi ma Allah godiya domin ta samu ciki cikin sauki ba ta yi wahalan laulayi ba sannan wajen haihuwa ma Ubangiji ya saukaƙa mata, in a ka cire ƙarin da ta samu suka yi mata ɗinki sannan ba ta yi doguwar naguda ba, ko da yake Inna Zainaba tace irin Mommy ce itama haihuwan ta cikin sauƙi ne kafin ma a tafi asibiti wani lokacin ta haihu, har ita kanta Mimin a gida ta haifeta sai daga baya suka je asibiti a ka duba su. Rukky ce ta fara kiranta lokacin da ta fara amsa waya suka yi mgana bayan kuma sauran wayoyin da ta rasa ba ta amsa ba, ta yi mgana da duka ƴan'uwanta har Mommy suna yi mata barka da arziki har da Madiha da megidanta domin ita kai tsaye ta ce"Congratulation Fatima Kabir Dabo, Za mo wa uwa ba abu ba ne mai sauƙi. Allah ya raya abin da kika samu ke kuma ya baki lafiya da ƙwarin jiki wajen shayarwa tare da tarbiya."
Sai ta ji daÉ—i da abin da ya kai É—an'uwa daÉ—i a wannan duniya ko da kuwa kuna da tarin bambamcin hallaya ne a tsakanin ku.
Haka ma Dr ya ce ya yi ta mata addu'a sannan da faɗan ta kula da kanta, shi da Jawahir sau biyu suna kiranta haka ma Hibba da Mu'azzam ta samu wayarasu ita dai ba ma za ta iya kirga waɗanda suka kirata ba amman dai abu mafi soyuwa shine babban kyauta ne na Ubangiji ace yau ka na amsa sunan uwa wani farinciki na dabam ne. Farincikin da take ciki ya sa ta kasa daina kallon jaririyar da Aji ya yi mata huɗuba da Maryama ba. Mamaki take yi yau itace ta haihu? Haihuwan ma tare da Aji abin da ba ta taɓa tsammani ba, har ta cire tsammani kuma sai Ubangiji ya kaddara za su zamo abu ɗaya.
Sanda ya shigo gidan ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya sauya ya tsaya ya amsa wayar Coach na su in da ya ke yi masa barka, ya kira shi da safe suna asibiti sai ya tura masa saƙon ba zai shigo Camp ba saboda mai ɗakinsa ta sauka shi kuma Coach na jin haka ya gayama sauran ƴan Team da cewa matar Capatin ɗin su ce ta haihu so ranar shi ya jwgoranci morning traning ɗin, abinci da komai da zai bukata Mimi ta faɗa ma Inna Zainaba a ka tanadar mishi a saman Dining bai duba abincin ba sai da ya leƙa ɗakin Mimi ya gaida da Inna Zainaba sannan ta fice falo ta ba su waje, gefen gado ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Me jego."
Mimi na mirmishi ta ƙara kishingiɗa lokaci ɗaya tana faɗin"Na'am Angon ƙarni."
Mirmishi suka yi ma juna, sannan ya leƙa jaririyar dake kwance gefenta tana tasharan barcinta na wani lokaci sannan ya dawo ya daidaita zaman shi.
"Sannu da koƙari Matar Aji.."
Mimi na mirmishi ta ce"Yauwa Mijin Mimi.".
Hannunta ya kama ya riƙe yana kallonta kafin ya ce"kin ƙara kyau, yau kaɗai jego nan ya karɓe ki."
Dariya ta yi amman ba ta yi mgana ba sumbatar hannun nata ya yi kafin ya ce"Ina fatan komai lafiya ko? Ta fara shan nono?
Haka ta faÉ—a ya na rike da hannuwanta. Sai Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce" Ruwan zamzam kaÉ—ai a ka bata, ruwan Nono dai kaÉ—an ya fara zuwa kila sai da zuwa gobe haka."
"To ba matsala zuwa goben? Ba za ta ji yunwa ba?
Mimi na dariya ta ce"Yunwa kuma? Ba za ta ji ba kada ka damu, na sha tea,kuma Inna Zainaba ta damamin kuni na sha zuwa Gobe ruwan nonon zai zo in sha Allahu "
Sai ya jinjina kansa alamun gamsuwa, sai kallon Mimi yake yi itama ta na kallonsa ta na nasa mrmishi, ita ta ɗauko yarinyar ta ɗora ta saman jikinsu dukkansu biyun a tare suka rike ta, sannan ɗayan hannun Mimi ta saka ta sakalo bayan Aji da shi, sun haɗe yarsu waje ɗaya sun rike. Ya riƙe hannun jaririyar ya haɗa da na Mimi ya damke kawai ya na mirmishi ya kasa mgana.
"Ka ga Kyautar da ubangiji ya yi mana ko? Yau mun zamo iyaye ma'ana mun zamo uwa da uba daga yau, nauyi ya same mu mun zama iyaye akwai haƙƙin ƴarmu a kan mu na tarbiya da kula da ita."
Ƙura ma jaririyar ido ya yi ta na ta barcinta sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Allah ya raya ki Inna ta, "
Haka kawai ya faÉ—a ya na cigaba da kallonta In Mimi ta na mgana sai dai ya É—aga kai ya kalleta ya yi mirmishi kamar yau sauran kalaman bakinsa nasa sun É—auke.
Ya dai kalleta cikin wani yanayi ya ce" Na gode sosai, na gode da kika yi dalilin jin wannan farinciki a matsayina na Uba na gode kwarai da kika kasance a cikin rayuwata Fatima kika kuma bani dukkan farincikin da gata a zamantakewar mu na aure. Na gode miki bisa yardan ki, haƙurin ki, Koƙarin ki a kaina Allah ya shirya mana Maryama ya ba mu ikon yi mata tarbiya ita da sauran ƴan'uwanta da suke tafe nan gaba."
Kanta ta É—ora saman kafaÉ—ansa lokaci É—aya tana faÉ—in"Amin Amin Mera. Nima na gode da ka yi sillar zamowa ta Uwa. Allah ya bar mu tare Amin."
Shima kansa ya jinginar saman kanta yana amsa mata da Amin Amin, sun É—auki lokaci a haka sannan Mimi ta É—ago da kanta tana faÉ—in" Na manta ka ci abinci kuwa?.
Sai ya girgiza mata kai da sauri ta karɓi Jaririyar daga hannunsa lokaci ɗaya tana faɗin"Yana can saman dinning."
"Me kuk dafa ne?
"Jallop rice ne Bintu ta dafa É—azun nan kafin su tafi, sai na ce su saka maka Food Flaks kada ya yi sanyi kafin ka dawo"
Kai ya jinjina kafin ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin"Kuma sai da kika yi mgana na tuna ina jin yunwa tun tea da na sha da safe ban kara cin wani abu ba."
Mimi na mirmishi ta ce"Na sani, na ga duk ka fara rama ne."
"Zo ki rakani mana, ni kaÉ—ai za ki bari naci abincin?
Ta na yar dariya ta ce"Jego fa na ke yi Mera, ba'a son na zauna wajen sanyi Inna ma ba za ta barni na fita falo na bar yarinyar nan ita kaÉ—ai ba.
Da sauri ya ce"Tare da ita za ki taho, ina cin abinci ina kallon ku ina jin É—adi."
Mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Haihuwa fa na yi jego nake yi, in na fita Inna za ta min faÉ—a sai ka yi hakuri fa."