← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 93

Sashe 67

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Inna Meri daga Tureta. Argungun ta wuce ta na can ba ta ma saka ranar dawowa ba, ba ta nan a ka yaye su Walida, a ka ba su certificate  Tana kuma wajen Mqgajiya har a lkacin kuma lafiya kalau ba nuna bambamci tsakaninta da Mariya. Sai dai ta leƙa gidan Bintu ita da Mariya, kwana biyu da yayesu suka fara zuwa gidan Bahijja ita da Mariya saboda darajan Inna yasa Bahijjan kyauta za ta koya musu, duk da tana karɓan 20k na mutum ɗaya a wata shidda shekara 40k kenan.
Sai da inna meri ta shafe sati shidda da kwanaki samman ta dawo gidanta, yaranta duk sun yi kewarta Mu'azzam ya zo mata sannu da zuwa tare da gaisuwa Hibba ba ta zo ba cikinta ya yi girma ba ta iya doguwar tafiya, Inna ta raba tsarabanta hida uku ne, ka shi ɗaya na ƴayanta ɗayan kuma ta aika ma Magajiya ta ce ta diɓar ma su gaje ɗayan kuma ta rabama makota da abokan arziki Har Hajiya ta zo ma Inna gaisuwa ta ɗiɓan mata tsaraban gujiya da gyaɗa da yawa da ta zo da shi.
Daman washegarin ranar da ta dawo Mimi Daga wajen aiki nan ta yini sai dare Aji ya zo ya É—auketa suka koma gida suma ta tarin tsaraban su, Walida tana murna Inna ta dawo gida daman ta yi kewar Inna. Abin mamaki kaf yaran Magajiya sun zo ma Inna gaisuwa. Sannan kwananta huÉ—u da dawowa a daran Magajiya ta zo ita da Gaje Maeesha tare da Matar Auwlu suka zo.

  Karon farko da Magajiya ta tako kafarta gidan inna, ta kuma ta karbesu hannu biyu, sun jima sai wajem goma na dare suka tafi, Magajiya dai ta kasa sakin jiki kunya da Nauyin sun isheta ta gama ganin ishara, Innar dai da take yi ma hassada da kyashi ta ga in da Ubangiji ya yi da rayuwarta ita kuma hassadarta da kyashinta ya cinyeta, Ƴaƴan inma Merin sune gatan su ita da na ta iyalan gaba da naya, ita Inna Meri ko a fuska ba ta nuna wai daman ba su shiri da Magajiya ba suna ta hira da Gaje tana kuma sako magajiya a cikin zencen na su.
Daman haka rayuwa ta gada, hassada mugun ciwo ne mai hassada sai ta ci sa, in ka zauna da kowa lafiya da zuciya É—aya sai Ubangiji ya turama masu hassada da kyashi a aniyarsu.

  Bangaren Rukky da Jaheed kuma soyayya ta mika har Jaheed ya zo garin saboda Rukayya. Maganar Nasir kuma ta sha ruwa tun da mahaifiyarsa ba ta amince ba.  Nasir ya yi ma Aji mgana shi dai ya ba shi shawaran ya fara daidaitawa da iyayensa tukunna, haka su Ahmad suka ce da ya fito group ya yi mganar, ita kuma Rukky Jaheed ya fara ɗauke mata hankali ya zo gida sun yi magana da alamu za su daidaita nan da lokaci kaɗan Mimi ta fi kowa murna. Tana so ta yi mganar da Aji sai kuma ta sha'afa yasa har lokacin bai san abin da ke faruwa ba.

******

_Monday_

Tun da ta tashi take jin jikinta ba daÉ—i amman ba ta nuna ba, Aji da wuri ya fita suna da morning traning tare suka fita ya sauke ta wajen aiki da cewa za ta kira shi in ta tashi domin ya je ya É—auko ta.
Kanta ke sara mata da safen kuma ta sha paracetamol, amman kamar ya sauka ashe bai sauka ba dakyar ta gama karanta L
Labaran safe ta koma Setting Room ta kwanta.

  Cikin lokaci kaɗan sai zazzabi ya rufeta ta fara rawan sanyin Aisha Farida ce ta je ta kira mata Rukky ta ga halin da take ciki. Sai ta yi amfani da wayar Mimi ta kira Aji amman har kira uku bai ɗauka ba, itama kuma tunanin abun na gaggawa ne ya sa ta kira Jaheed ta ce ya zo ma'aikata ya same su Mimi ba ta da lafiya  jin haka ya sa a ruɗe ya taho daman bai koma ba a ranar yake tunanin bin jirgi zuwa Lagos.
Ba jimawa sai ga shi ya zo, zafin zazzabi yasa Mimi ta kasa ma mgana Rukky ta riketa suka fita ana bin su da Allah ya sauwake ganin ko iya buÉ—e ido ba ta yi ya sa Jaheed yace su tafi asibitin da suke zuwa itama a can Mimi ke da katin ta.
Wani asibitin kuɗi ne suna zuwa a ka karɓi Mimi aka dibi jininta, sai a ka saka mata drip da allurai.
Jaheed da Rukky suna tare da ita, Ita Rukky ta manta da wayar Mimi a cikin jakarta kuma sun barota a motar Jaheed, Aji na ta kira ba'a É—auka ba daga Camp ma'aikatansu ya biya Na misau ke gaya masa Mimi ba ta da lafiya Rukayya da wani namiji sun zo sun É—auketa.

  Da farko ya ɗauka Nasir ne sai da ya kira shi sai yace masa yana wajen aiki. Sai ya fara tunanin to waye? Shi kuma ba shi da L lambar Rukayyan ballantana ya kira sai ya yi tunanin ya je gida ya gani, nan ma ba ta nan  kuma ya na cigaba da kiran wayarta amman ba'a ɗauka ba har bayan la'asar.
Ba tunanin da sheɗan bai sakaa masa ba Har hassowa ya yi wai Mimi ta bi wani namijim Ransa in ya yi dubu ya ɓaci, kirjinsa na sama da kasa idanuwansa sun yi jajirce, Zagaye kawai ya ke yi a falo ko zama ya kasa yi ya kira wayar Mimi bai san iyaka ba amman ba ta iya ɗauka ba.

  Su kuma suna asibitin har la'asar sai da a ka cire ma Mimi ƙarin ruwa sannan eesult ya fito, Mimi ciki gare ta na tsawon sati shidda da kwanaki, ita kanta ba ta san da shi ba amman dai ta san watan da ya gabata ta yi ɓatan wata, Ita likitar ma ya ba ma tarkadan sakamakon Rukayya da Jaheed suna waje kuma ko da ta fito ba ta faɗa musu ba sai kawai ta ce maleria ce,  da tare da Rukky za'a kaita gida amman sai mamansu ta kira waya hankali ta she ta ce Rukayya ta zo mijin Bibi ya kirata ya ce tana asibiti za ta haihu., Don ma ta yi ɓarin cikin ta na farko da ta jima da haihuwa. Dalilin da ya sa suka rabu a nan kenan ta hau abin hawa zuwa asibitin da a kace Bibi na can ta na naguda shi kuma Jaheed ya ɗauko Mimi zuwa gidanta.

  Aji na jin ƙaran bude get ya yi zaraf ya fito haraban gidan a kan idanuwanshi Jaheed ya shigo da motarsa ya yi parkimg sannan ya fito ya zagaya ya buɗe ma Mimi ta fito. Jikinta ba karfi yasa ta yi kamar za ta faɗi sai ya riketa sannan ya karbi jakar hannunta, takardan Result ɗin cikin kuma na cikin aljihun rigan jikinta ta saka.
Aji na ƙofar falon gidan yana kare musu kallo a ƙankance, Ba abin da sheɗan ke gaya masa sai Mimi ta bi tsohon saurayinta sun je sun gama yawon iskancin su shi ne ya kawota gida saboda dukkansu ba su da kunya.
Saboda kishi da ɓacin rai har wani huci mai zafi yake fitarwa ta baki Mimi ta na tafe a hankali jaheed na riƙe da hannunta tana dagowa suka haɗa ido da Aji sai da ta ji ta warke gabaɗaya da sauri ta kwace hannunta a na Jaheed ta na jin gabanta na faɗuwa. Aji a fusace ya juya ya koma cikin falon yana tsaye ya na zagayen falon yana huci hannayensa goye a bayansa.
Suna shigowa Mimi ce a kan gaba sai Jaheed ya na tafe da jakar Mimi da ledan mganganinta na karin jini da na saka cin abinci, tunda an rubuta magani suka tsaya phamarcy suka siya.

   Mimi ce ta yi sallama amman ko ƙarisa sallaman ba ta yi ba Aji ya daka mata wata razananiyar tsawar da sai da ta yi baya kaman za ta faɗi, Jaheed dake bayanta ya tare ta yana faɗin" Subhanallah ki yi a hankali kin san jikin ki ba karfi."
Aji ya kallesu tuni sheÉ—an ya haska masa zargi a cikin zuciyarsa idanuwansa ya rufe bai yi tunanin da ya ciza ya hura ba.
Cikin nuna su da yatsa ya ce"Me kuma ya kawo ku gidana? Wato saboda ba ku da kunya kun gama watsewar ta ku a waje shi ne sai kun zo har gabana kun nuna min ku Æ´an ta zubar ne?
Mamaki ya hana daga Mimi har Jaheed magana, kawai sai Aji ya cigaba da faÉ—in"Ashe kina can tare da tsohon saurayin ki shi ya sa nake ta kiran wayarki ba ki É—auka ba ko? To me ya dawo da ke gidana,? Me ya sa ba ki bi shi can gidan na su ku cigaba da barbaÉ—an naku ba."

"MANSOOR...!"
Chapter 67 · 0% Book details