← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 93

Sashe 73

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Sai Baba ya kaɗa kai kafin ya ce"To bari na shiga ciki na sanar da Magajiya sai mu je tare na yi mata mgana."
Tare suka shiga cikin gida, Mansoor ya ce bari ya gaida magajiya, suna shiga suna ma tsakar gida ne ita da Mariya suka shigo ya rankwafa ya gaida Magajiya da irin salon gaisuwarsa ta amsa cikin sakewa kamar yadda ta saba yanzu ta daina É—aure musu fuska, ko da ma da sauran wani abu a cikin ranta ta boye ma zuciyarta
Mariya na gefe ta gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya ya na faɗin"Ke kina nan?  yaushe rabon da na ganki?
Kanta na ƙasa ta ce"Kwanaki mun je gidanka ba ka nan Anty Mimi kawai muka samu a gida."
Sai ya jinjina kai Magajiya ta ce" Ranar lahadi tunda tana gida sai ku je ke da Walida ku gaishe su."
Sai ta amsa dai dai lokacin da Saddiqu ya shigo gidan fakan fakan kamar mahaukaci, daman ya samu labarin yanzu sai yawon gari can lagos ɗin dama yar buga buga ce kuma jari ya suɓuce. Har da Auwalu sun yi mganar ya ce ya zo ya fara harkan gini ya ce ba zai iya ba ya koma sai zaman shagon wani abokinsa. Dole Maeeshan ta nemi aikin koyarwa tana zuwa domin ta rufa ma kanta asiri.

  Ko Magajiya bai gaisar ba. Sai ita ce ta ga zai wuce zuwa bangaren matarsa ya sa ta ce" Kai Saddiqu ba ka ga Yayan ka ba ne?
Sai ya juyo ya na kallonta ya na kuma kallon Mansoor tunda akwai wuta haske ya gauraye tsakar gidan. Sai ya kasa mgana Yana mamakin yadda Magajiya ta koma ruwan sanyi shi fa jin su kawai yake yi, ba bu wani abin da mutum zai yi maka wanda Allah bai maka ba. ƙaramin tsaki kawai ya ja ya yi wucewarsa mirmishin gefen baki Mansoor ya yi domin wanda bai daraja uwarsa ba har yaushe kake tunanin kai zai iya daraja ta ka mahaifiyar? Magajiya kunyar duniya ya kamata saboda abin da Saddiqu ya yi mata.

  Dai dai lokacin da Baba ya fito cikin shirinsa yau kwanan Magajiya ne sai gobe ne  yake gidan Inna shi ya sa yana fitowa ya kalli Magajiya lokaci ɗaya yana faɗin" Magajiya Mansor zai ɗauke ni zuwa gidan Meri zan dawo zuwa anjuma in sha Allahu.".
Sai Magajiya ta kallesa a sanyaye kafin ta ce"Ina fatan dai ba wata matsala?
Da Sauri yace"Lafiya lau, wata yar matsala ce amman kada ki damu."
Ganin bai faÉ—a mata ba ya sa ta kaÉ—a kai kafin tace to Allah ya sa a dawo lafiya.
Mansoor ya yi mata sallama suka fita tare da Baban ta bi su da kallo tana girgiza kanta, Ko ta ƙi ko ta so Ƴayan Meri da agolan da ta raina su ne su, yaran nata kuma da ta nuna sun fi kowa ga shi nan su ne rayuwarsu ke wulaƙanta gwara gwara ma Auwalu da shi yanzu ya zama Enginer ba ya gini sai dai karɓan kwangilan gini kuma ba laifi yana samu sannan ya na yi mata tunda ba halinsu ɗaya da Saddiqu ba, Jummai sai dai ta zo ta ƙarbe na ta, har gwara ma Zuwaira to yanzu haka shi kan shi Saddiqun kusan ci da shi na wajen su ne tunda ba shi da komai yanzu sai bakin rai.
Mariya kuma ba domin su ba da tuni itama rayuwarta ba ta inganta ba, tana da tabbacin da bikin ta in ya zo su ne za su yi komai da abunda uwa za ta yi da abin da ubq zai yi ta na da tabbacin suna yi domin Allah ne ba domin komai ba  in da ace suna yi domin ganin ido ne da tuni sun daina tun baya da take nuna hassadatan a fili, yanzu kan ta saduda tunda ta ga jama'a ma suna gudunta har su Gaje yanzu sai su yi wata ba su leƙo ta ba, ko wani abu ya faru a anguwa sai dai in ta biya musu su ce sun shiga jaje ko Allah ya kyauta, amman ba sa nemanta Ta dai fahimci duniyar ce gabaɗaya ta sauya gwara ka aikata alheri yanzu in da mutuwa ta yi fa? Haka mutanen da ta zauna da su za su yi mata?  ta kuma fahimci lalle ka zauna da mutane lafiya shima wani abu ne, Sannan ka aikata alheri tun kana duniya za ka ga amfanin haka, ga shi Meri ta bar mata gidan amman  kamar ta tafi da duk wani albarkan gidan  gabaɗaya.

******

Tunda Inna Meri ta ga Baba Ɗanjuma da Mansoor ta san ƙaranta ya kai. Shi ya sa tunda suka shigo ta haɗe rai, ta ga fa zuwan su suna zaune a falo suna jiranta Baba Ɗanjuma ke saman kujera Mansoor kuma yana zaune a ƙasa. Walida ce ta kawo musu ruwa Aji sai faman waige waige yake yi ko zai ga Mimi amman ba ta fito ba.
Inna Meri ko kamar da gayya ta shiga aikace aikacenta wai wanke wanke da daddare saboda dai kada ta sauraresu.
Mansoor yunwa ya ke ji bai ci wani abun kirki ba, sai ya tambayi Walida abin da suka dafa kai tsaye ta ce"Tuwo Inna ta yi da rana na zubo maka ne?
Sai ta amsa mata da eh, ai kam tana zuwa Kitchen É—in Inna ta ga za ta zuba abinci ta tambayeta wa zai ci? Ta ce yayanmu ne.
Kai tsaye Inna Meri ta ce"ba zai ci tuwon ba, rufemin kular nan"
Cikin mamaki Walida ta ce"Saboda mene Inna? Inna ta mata wani kallo kafin ta ce"Sai na ji shaƙa sannan."
Walida na jin haka ta yi sum sum ta fita daga Kitchen ta koma ta gaya ma Mansoor abin da Inna ta ce sai ya yi mirmishi kawai ba tare da ya yi mgana ba Baba ÆŠanjuma ya ce" Me ya sa Meri take hakane? Ban san ta da wannan fushin ba."
Kawai sai ya miƙe yana faɗin bari ya je ya sameta a cikin madafin.

  Yana ta shi, Mansoor ya kalli Walida yana faɗin" Ina Antyn ki?
Sai da ta kalli É—akin sannan ta ce"Tana ciki, kila ta kwanta ne"
Kai ya jinjina mata sai kawai ta wuce ta shiga ɗakin nata, ta iske Mimi kwance amman ba barci take yi ba, ta na shiga ta yi saurin miƙewa zaune lokaci ɗaya tana faɗin" Aji ne ya zo?
Sai Walida ta ce"Eh shi da Baba, wai me ya yi ma Inna ne? Abinci ma fa hana shi ta yi.".
Mimi ta zaro ido kafin ta ce"Kai.!
Walida ta zauna gefenta tana faÉ—in" Wlh Allah, kuma fa ta ga har da Baba amman ta na kitchen tana wanke wanke."
Sai Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba, to ita me za ta ce?  duk da ya yi mata ba dai dai ba amman bai kamata Inna ta hora sa da rashin abinci ba, gabaɗaya tausayin shi ta ke ji, Kamar ta ta shi ta je ta roki Inna kuma tana da tabbacin bai ci wani abinci ba tun jiya nan, amman ba za ta iya ba sai Inna ta ga kamar ta yi rashin kunya kuma duk abin da take yi ta na yi ne saboda ta ƙwatan mata ƴancinta. Suna ciki suna jin tashin maganar Baba da Innar a talon,  kenan Baba ya samu nasaran Fito da Inna Meri daga cikin kitchen.

  Inna Meri na saman kujera Baba Ɗanjuma na gefenta Mansoor na gefen Baban kansa a ƙasa. Shi kuma Baba Ɗanjuma sai faman kallashi inna yaoe yi da kalaman ban hakuri faɗi yake yi" Haba maryamu ban san ki da dogon fushi ba, ina miki shedar ke macece mai afuwa, tunda har ya san ya yi laifin kuma ya ce ya yi nadama ya ba da hakuri to me zai hana ba za ki yi hakuri ki ba shi matarsa su koma gida su daidaita ba?.
Inna Meri ta yi shuru kafin ta muskuta lokaci É—aya tana faÉ—in" Ya gaya maka zargin matarsa yake yi? Ya sanar da kai shi da kansa ya ce ta fitar masa a gida, shi isheshe mai gida ba."

  Ta faɗa tana hararanshi lokaci ɗaya tana cigaba da faɗin" Ya yi sum sum da kai kamar mutumin ƙwarai. Ahalin ya iya aikata tsiya kala kala, ace a shekaran Baban Inna talatin da ɗoriya bai san ciwon kansa ba? Ƙanin sa Mu'azzamu wlh ban taɓa jin kansu shi da matarsa ba. Amman shi kamar wani ƙaramin yaro daga wannan sai wannan., ni kuma na gaji da wata rana ya yi abin da za mu kasa shiga mutane gwara ya sauwaƙe mata cikin girma da arziƙi na maida ma Hajiyar jikarta na ba ta hakuri."
Inna Meri ta gama faɗa tana ƙara haɗe rai shi dai Mansoor sai faman ba da hakuri ya ke yi,  Baba Ɗanjuma ma haka.

"Duk ya faÉ—a min wlh, na kuma yi masa faÉ—a tunda dai ya yi nadama ki duba girman Allah ki yi hakuri Maryama.."
Chapter 73 · 0% Book details