← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 93

Sashe 89

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hibba ta nata kuka haka Mu'azzam ya dawo ya ssme ta da ya tambayi ba'asi sai ta gaya masa abin da ya faru tun farko sannan ta kunna masa Vioce É—in Mimi da wayar da su ka yi domin ta yi recording abun dai duk ba daÉ—i ya yi ma Hibba faÉ—a me ya sa ba ta ba ta hakuri ba? Ita kuma sai ta ce ita fatan alheri ta yi ba na tsiya ba, saboda dai a kashe mgana ya sa ya kira Mimi da kansa domin ya ba ta hakuri shima ta shafe su ba ta É—aga wayarsa ba sai ya kira Inna Meri ya gaya mata abin da ya faru, ta ce itama ba ta ma san Mommyn ta sake aure ba tun da daga Binta har Mansoor ba wanda ya faÉ—a mata sai ta ce ya bar mganar a hannunta Mansoor shi zai kashe wannan fitinar.
Ta fahimci Binta dai tana kishin Babanta ba ta so auran Mommy ba. Shi ya sa duk rayuwaka suka ɓaci itama kuma Hibba ta na ganin ba wani abu ta faɗa ba sai a ka kasa samun fahimtar juna gabaɗaya.

Inna Meri da kanta ta kira Mansoor ta faɗa masa abin da ke faruwa ta ƙara da cewa" Ba ina goyon bayan Hibbatu ba ne, amman zencen gaskiya ta fi matarka gaskiya saboda ita ba ta san abin da ke faruwa ta yi mata fatan alheri, daga karshe sun kasa fahintar juna har abubuwa suka lalace, na so na je na bata hakuri amman sai na yi tunanin ba hurumina ba ne tunda ba ta gaya min ba, ba na so a fara samun baraka daga matayenku saboda in hakan tana faruwa wata rana kuma ɓaraka za ta iya bayyana daga bangaren ku, kai ka yi ma Binta mgana ka fahimtar da ita shima Mu'azzamu na gaya masa ya fahimtar da matarsa in an samu daidaito sai su kira juna Hibba ta ba ma Binta hakuri magana ta wuce."

Sai Aji ya ce cikin satin nan zai zo gida zai yi mgana da Mimin shi ya É—auka Fatima na da tunani ashe dai da sauranta.
Mu'azzam suna waya amman bai gaya masa ba. Sannan ko Walida da ke gidan ta kwana ta tashi ba ta san wani abu ya faru, sai ya bari kawai sai ya dawo gidan ya samu lokacin da zai yi ma Mimin faɗa sosai ko ta dawo cikin hayyacinta ya je ma ya kara ganin Mommy tana hawaye ta na gaya masa duka yaran sun juya mata baya harda Mimi sannan ta hada shi da Alƙali har ga Allah bai ga illan shi ba, kamili mai mutumci sun samu uba amman suna haukan banza.

Ranar jumma'a ya dira gombe, ko a fuska bai nuna ma Mimi wani abu sai da ta gama bikin tarbansa bayan ya yi wanka ya ci abinci ya so ya yi mata mgana amman sai kewarta ta hana shi a ka kwana ba ma juna Soyayya da asuba ya tafi masallaci bayan ya dawo ya koma barci asabar ne ba ta fita aiki bai tashi ba sai goma na safe yana fita falo ya iske ta, tana goge goge ga Ummi saman kujera an jinginar da ita alamun an fara Koya mata zama. Ita kuma matar gidan tana ta gogen tibi wayarta na saman kujera ta saka speaker suna mgana da Madiha abun da kunnuwansa suka jiye masa shi ne Madihan na cewa" Ni fa na gayama Khadi in har Mommy na son mu sai dai ta zaɓa ko auran ta ko mu."
Mimi ta ce",Wlh nima fa ko kiranta ban sake yi ba, in har tana son mu sai ta zaɓa ko wannan mijin ko mu ƴayanta."
Yana tsaye ya ji Madiha na zuga Mimi da kada ta ƙara kiranta ta bar ta in suna da amfani za ta neme su.

Saboda haushi ko Mimi ba ta san ya shigo falon sai da ta ji muryansa yana faɗin" Ko shekara ɗari ta yi ba ta neme ku ba, ba abin da zai sameta amman ku sami ko wata uku kuka yi ba ku neme ba ta tsinuwan Allah da ta mala'iku sai ta tabbata a kan ku, sannan ku sani ita ce ta haifeku ba ku ne kuka haifeta ba, aure ta yi ba zaman zina take yi ba, ko da saka albarkan ku ko babu za ta zauna lafiya.Ku ne in ba ta yafe muku ba ku ke cikin bala'i da masifa, sannan zan miki gargaɗi na karshe in har ba alheri za ki kira matata ki gaya mata ba, to don Allah kada ki sake kiranta ina son ta samu rabauta a duniya sennan ta samu lahira ke da kika juya ma Albarka baya je ki ki yi ta fushin ki ki jira ranar da mahaifiyarki za ta zabi sunnar ma'aiki a kan ki, ga ki kamar mai hankali maimakon ki zama jagoran ƙannen ki wajen faɗa musu gaskiya sai ke ce ke ƙara zugasu kuna kauce hanya, girman banza gareki sannan takmar ilimin ki bai yi miki wani amfani ba, ki je can ki yi ta sakarcin ki amman na gaya miki wlh tallahi ka da ki kara kiran matata kina zugata."

Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, Mimi ta dankare a tsaye tana kallon Aji cikin mamakin manya manyan kalaman da mijinta ya sauke ma yayarta, ta buɗe baki za ta yi mgana itama ya ɗaga mata hannu ya fara zazaga mata nata faɗan tas ya yi mata sai ta fara kuka tana faɗin" To koma menene sai ka gaya ma yayata mganganu haka? Kai tsaye yavce" An gaya mata in kuma za ki rama mata ne, bismillah ina ruwana da girmanta tunda girmanta bai mata amfani ba,.Mahaifiyarku ce fa amman saboda rashin tunani kuna neman saɓa mata saboda haukan banza in ba'a aure za'a haifeta? Ita ba tana gidan Mijinta ba ne? Sai ta hana ta auren ita? Ba ku da adalci ba ku ba yara ƙanana ba amman kuma kuna yin abin da ko yara suka yi sai an yi mamaki, har saboda haka Hibba ta yi miki murna ki ka bi ta da zagi saboda ke kin isa ina laifin wanda abun alheri ya same ka yace maka Allah ya sanya alheri? Sai ki zage ta?

Mimi na kuka wiwi ta ce" Ni fa ban zageta ba, ita ce ta min dariya to abun dariya ne?
Shima ya taso mata da cewa to abin kuka ne, ko so take yi ta ta ya ta haukan da take yi na faÉ—a da mahaifiyanta saboda ta yi aure. Mimi duk yadda ta so kare kanta Aji bai ba ta dama ba, ya yi mata faÉ—a sosai ya kuma bar ta, tana kuka ya É—auki Ummi suka shige É—aki ranar gidan yini ya yi ba daÉ—i ko abun kari ba ta yi ba ta shige É—aki tana kuka shi kuma ya É—auki Æ´arsa suka fita zuwa gidan Inna ya karya ita kuma Inna ta yi ma Ummi wanka tunda Aji cewa ya yi Mimin ba ta jin daÉ—i.

Saboda nono ne ya sa ya maida Ummi gidan a mamakinsa sai ya ga Mimin ta tashi har ta yi abinci ta gyara gidan,ganin haka ya sa bai sake fita ba ya zauna ya na ƙara mata da nasiha, ita kuma ta baahi hakuri ta ce za ta,kira Mommy ta ba ta hakuri ita da Hibba.
A gabansa ta kira Mommy ta ba ta hakuri, Mommy kamar ta yi kuka farinciki ya cika ta, ta yi ta sakama Mimin albarka tana faÉ—in" Wlh Allah saboda ku na yi wanman auran saboda na kare muku mutumcin ku da na Æ´ayan ku." Mimi na hawaye tace"Hakane mommy ki yi hakuri, In sha Allahu ba zan kara ba suma su khadi duk za su daina." Mommy tace bakomai ita ba ta rike su ba ta yafe musu tun kafin ma su roke ta
Chapter 89 · 0% Book details