Sashe 51
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasir ya fara rantsuwan ba haka ba ne, Makama na rantsuwan ya gano shi, Aji na gefe ya ce"To miye! In kana sonta ka shiga cikin Manema kawai kai namiji ne mijin mace huÉ—u"
Me za su yi in ba dariya ba domin Nasir ne ya ce"Kwarai mutumina." Da alamu ya na so yana kaiwa kasuwa, da Rukky ta fito za ta tafi kawai sai Makama ya ce ga Nasir zai kaita gida, Aji ya dafa kafaÉ—ansa yana faÉ—in" Sa'a dai Nasiruddeen Angon Nafisa da Rukayya."
Dariya har su Mu'azzam na dafe ciki ganin Nasir ya miƙe ya jinjina ma Aji hannu lokaci daya yana faɗin"Na gode namijin duniya, Angon Mimi."
Suna ta masa shakiyanci har ya fice. Shi kuma ya kaita gida amman hiran na su sama same ne ya dai karɓi lambar wayarta sai da ya dawo sannan suka watse Nasir da Ahmad tafiyar su ɗaya Mu'azzam da Aji ma haka.
Sanda suka koma gida su Hibba na ta fama da suyan nama ga Walida da Mariya na ta fama da suyan dumblan ba su ci abinci ba domin cikinsu ya cika sai suka zauna a falo suna ta hira da Inna Meri, Inna na faɗin Yalwa ta kira ta tana godiya ta ce Mansoor ya tura mata 50k Aji ya ce ba shi da kuɗi ne ya so ya fi haka shina Mu'azzam Inna na ta saka albarka, sannan ta ɗauko musu wata farar keda da kaya ciki Mimi ta aiko da shi ta yi ma Inna Atamfa da hijabi da takalmi, sai kuma Walida Abaya da mayafi, Aji bai ma san da saƙon ba kwata kwata nan ma Inna ta yi ta saka albarka sai da suka koma ɗaki shi da Mu'azzam ya kira Mimi, yana ce mata ta ga kuɗi a hannunta baja baja tana ta hidima da shi a ciki ta yi ma su Inna kaya
Ita kuma ta ce"Eh da yake kai kaÉ—ai ke da KuÉ—i ka manta nima aiki nake yi"
Ya ce"To ma su aiki, ni ai kin san zaman banza nake yi."
Dariya ta yi masa kafin ta ce"Kayan sallah ta fa? Ba ka aiko min da shi ba?
Kai tsaye ya ce"Amman ba ki da tausayi, duk kuÉ—ina ya kare ki É—auka cikin na lefe ki É—inka mana."
Mimi ta shagwabe tana faɗin"Haƙƙin ka ne fa ka min sutura, da ci da ciyarwa."
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ai zan ci kuma zan yi ciyarwan in sha Allahu.
Sai daga baya ta gane maganarsa ai sai ta saka Ihu ta kashe wayarta ta bar shi ya na Mirmishi, Mu'azzam ya fito daga wanka ya tsaya kawai yana kallon Yayan na shi sai daga baya ya ganshi, ya ga yana kallonsa sai ya basarwa ya miƙe yana faɗin" Ka fito? Mu'azzam na yar dariya ya ɗaga masa kai har ya shiga tiolet ɗin yana bin sa da kallo ya na yar dariya.
A daran aka faɗi an ga watan salla washegari a ka ta shi da shirin zuwa sallar Idi. gaɓadaya gidan har da su Inna, Mu'azzam zai je ya ɗauko su Baba Danjuma su uku tunda matan su ba sa zuwa. Hatta Magajiya kuwa Amman Inna sallar Idi ba ta taɓa wuce ta ba, Aji kuma zai ɗauki Inna da su Hibba. Masallacin takwas da rabi suke tada salla nan cikin gari ne Aji da Mu'azzam shigar fararen shadda suka yi harda babban riga da baƙaƙen takalma da huluna da agogo baƙaƙe, Ahmad ya ɗinka musu daga kaduna zuwa da shi kawai ya yi Mu'azzam ya biya komai da komai, in ka gansu kamar yan biyu, Inna na kallonsu tana mirmishi sai kwalla addu'a take yi a cikin ranta Allah ya kara haɗa kawunan su Hadda Junoir shima an ɗinkka masa shaddan matan kuma kowacce ta ci gayunta lalle ne kaɗai ba su yi ba sai sun dawo daga idi tun da ba lokaci.
Rufe gidan a ka yi gabaÉ—aya, a masallacin Idi su ka haÉ—u da su Mu'azzam da kuma su Nasir tunda duk can suke zuwa. Bayan an idar da sallar idi kenan zaratan abokan suna ta hotuna daman Nasir da matarsa ya zo haka Ahmad da Makama, kawai sai kuma su ka haÉ—e da Mimi, ita ta kawo su sallar idi ita da Hajiya da Baaba Uwani. Kamar haÉ—in baki matan abokan suka haÉ—e gabaÉ—aya Mimi ta ji kunyar Inna ta duka ta na gaisheta Inna ta ta da ita tsaye ta na saka mata albarka, Hajiya kuma na ta yi ma Inna tsiyar Idonta kenan shike nan sai yara su raba zumunci inna na dariya ta ce tana nan zuwa.
Mimi ta sha kyau cikin abaya mai ruwan kasa, ta naÉ—a mayafinta a kanta.
Saboda su Inna da su baba ba su daÉ—e ba, Hibba da Mimi sun yi mganar sai sun yi waya sannan suka rabu kowa ya shiga motar da ya zo, Aji dai sai da ya jira Mimi saboda go slow, sai da ya samu suka fita sarari tare sannan suka tafi tare zuwa juction É—in da suka rabu.
Bayan duk an koma gida aka fara ciye ciye da cin nama, ranar Idi ce ranar zama cikin Iyaye da Æ´an'uwa Aji da Mu'azzam a gida suka yini cikin yan'uwansu amman sun kira Æ´an'uwansu sun yi musu barka da salla har Baba Yakubu ya kira bayan ya kira can Kwami ya yi musu barka da sallah Sannan sai ga shi ya kira Dr. sulaiman, ya yi masa barka da Sallah sannan ya kira Mommy itama ya yi mata barka da sallah har da Daddy kuma sun ji daÉ—i, Ita Mimi ma mommy ke gaya mata da farko sannan Dr ma ya faÉ—a mata Daddy sai da ya zo gidan ne ya ke ce mata mijinta ya kira shi sai ta ji daÉ—i kenan dai da gasken Ajinta ya sauya.
Ranar ba su yi waya sosai ba saboda kowa na can cikin ahalinsa. Ranar yawon sallah na farko ma duk suna gida ranar na uku ne gidan Inna ya cika da su yaya Amina da jikoki ranar kuma aka yi abincin sallah su kuma su Mu'azzam da su Nasir gari suka shiga suna ta ziyarce ziyarce sune har gidan surukan Nasir da Makama. Rukky na gida itama tunda Bibi itama gidan ta je Nasir dai bai furta yana son Rukkaya ba amman ta fahimci haka. Daga nan suka je gidan surukan Ahmad bayan nan suka zagaya duka gidan iyayensu har gidan Wanzamai da wajen inna suka mata barka da sallah gidan Hajiya ne ƙarshe Mimi ba ta san ma da zuwan su ba gidan Hajiya cike da yaddiko da ƴaƴanta da jikokinta ta ji kiranta yana faɗa mata ga su sun yi ma Hajiya barka da sallah.
Sai a ranar wasu cikin ƴaƴan Yadikko suka ga mijin Mimi lalle ya ci sunan shi Aji haka suke faɗa Hajiya ta ji dadi tana ta zolayansu Kowanne su sai dai ya bata goron sallah, Ba su wani tsaya ba suka ce za su karisa gidan Daddy naman da cake din sai package din shi Mimi ta yi musu, ta yi kyau cikin leshinta doguwar riga kamar ka sace ta ka gudu. Daga anan sai gidan Daddy shima ya na gida sun kuma samu harda Jaheed tunda shima yaran na shi duk sun zo gaisuwan sallah hakika ya ji daɗin wannan ziyaran duk da shima gidan cike da mutanensu yan Siyasa sai a ranar Aji suka taɓa musabaha da Jaheed kowa na kallon kowa. Sai bayan sun baro gidan ne Makama ya kalli Aji yana faɗin"Yau dai ka ga rival ɗin ka Aji."
Tun da shinl ne daman ya kawo ma Aji labarin Jaheed É—in da ya ji a wajen Bibi.
A wajen ginin Aji suka yada zango aiki akwai ake yi ba dare ba rana domin nan da kwana goma Aji ke bukatwr matarsa daga can suka ka rabu kowa ya yi gidan shi.
Washegari kuma Hibba ta tafi gidansu itama ta yi gaisiuwan sallah. Mimi kuma a ranar suka yi mgana da Aji ya jadadda mata kada abin da za ta yi ya wuce nan da kwana goma. Dole ta kira Rukky domin su fara shiri mganar gida daman ya yi mata vedio ta gani ta tura ma Mommy ta ce ba matsala tuni ta ba da oder komai da komai, mganar gyaran jiki suka fara yi, kayan gyara kuma Khadi ta haÉ—a ta da wata Surayya Dee mai saida kayan mata da gazar sababi tana kano ne aiko mata da shi kawai za'a yi, kayan surayya dee mai suna Bojuwa kaya ne masu inganci da daÉ—ewa a jikin mace kafin su sake, ku yi amfani dashi domin zamowa tauraruwa kamar Mimi a gidan Ajin ta.+234 803 277 3332
Sannan ma yaddiko ta aiko mata ds su gumba, Mommy kuma ta siya wasu kayan daga wajen Surayya mai kazar sababi na Amare da uwayen gida +234 803 277 3332 ta siya mata babban Package har da kaza da matsalan ta yanzu wajen aiiki ne amman sun yi shawara da Rukky za ta samu manaja ko hutun sati É—aya ya taimaka ya ba ta, duk shirin nan da ake yi Madiha ba ta saka kanta a ciki ba Khadi ta kira ta ta faÉ—a mata za ta je Gombe Mimi za ta koma sabon gida sai ta ce ba za ta samu zuwa ba, ita dai ta ce za ta je Dr kuma ya ce Jawahir za ta zo daman kuma ta yi arba'in za'a kawo ma Daddy Baby shi da Hajiya.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3012*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*