← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 93

Sashe 61

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Haka Mimi ta faɗa, tana ƙamƙame dashi, kai tsaye ya ce" Duk abin da Mimi ta shiryama Aji kinsan bai taɓa juya mata baya ba."
BuÉ—e idanuwanta ta yi kafin ta ce" Ko mu soya kwai ne mu gasa buredi, mu sha Tea ko?
Sai ya gyaɗa mata kai kafin ya ce" Ni fa ba ruwana da wannan bangaren, ke dai kawai ki ciyar da ni, ni kuma ina yin aikina na ci da ciyarwa." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, Sai kawai Mimi ta daki kirjinsa cikin sigar wasa tana masa mirmishi,  sannan ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Rana ta yi, bari mu karya karfina ya dawo jikina tukunna."
Da kallo ya bita za ta shiga kitchen sai ya kwala mata kira ta juyo kai tsaye ya ce"Ba na hana ki shiga kitchen ba takalmi ba dankwali ba?
Sai Mimi ta dafe kanta kafin ta shagwaɓe tana faɗin"Na manta ne Aji."

  Miƙewa ya yi bayan yac e mata bari ya zo cikin bedroom ɗin su ya shiga ya ɗauko mata hula da silafas ɗinta na cikin hida ya zo har gabanta ya duka ta saka takalmin sannan ya kama kanta ya saka mata hular sannan ya kalleta kafin ya ɗan rankwasheta yana faɗin"Ba ki san saka Dankwali ko?
Sai na yi miki aski"
Baki ta tura kafin ta ce"Aski? To sai ka kalli gashin wa?
Ya na juyawa zuwa kan kujeran da ya tashi ya ce" Aure zan ƙara, ba zan zauna da mai kai kamar na maza ba."
Tsaye ta yi ta na buga kafa za ta fara masa kukan shagwaɓa, ya na jinta sai ma ya ɗauki romot ya ƙara ƙaran talabijin ɗin lokaci ɗaya ya na faɗin" Fatima ina jin yunwa fa. Ɗaya saura na rana ban karya ba fisabilillahi fa"

  Haka ya faɗa ya sa ta faɗa kitchen ɗin lokaci ɗaya tana faɗin"Da laifin ka me ya sa baka tashe ni ba?
Bai san ko ta ji ba ya ce"Mace tagari ba ta jira miji ya tada ta sai dai ta tada shi, amman ke sai barci kamar kasa, zan ga ranar da za ki haihu Fatima."
Ita ba ta ji sa ba. Ta kunna gas ta fara ɗora ruwan tea ɗin bayan ta saka kayan ƙamshi da ganyen shayi, sannan ta fara koƙarin Kwaso ƙwan da za ta soya buredi ya na can saman dinning wanda za ta gasa ga shi kuma sai da ta fara fasa kwan ta tuna sai kawai ta fito bakin kitchen ɗin tana kiran sunan Aji bai jita ba sai da ta ƙwalaa masa kira da Karfi sannan ya juyo lokaci ɗaya yana na rage ƙaran talabijin ɗin.

"Miye ne?

  Haka ya ce mata yana haɗe rai, shi fa baya son mace ta riƙa saka shi aiki kuma ya lura halin Mimi ne ta riƙa saka shi aiki kamar wani ɗanta.

"Buredi za ka É—auko a saman dinning.."
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, hararanta ya yi kafin ya ce"Ke fa? Kafar ki na ciwo ne?
Wani kallon ƙasa ƙasa ta yi masa kafin ta ɗaga masa hannuwanta lokaci ɗaya tana faɗin" Na saka hannuna a kwai ne, don Allah ka kawo min."
Kamar ba zai ta shi ba haka ya tashi yana tura baki kamar mace ita kuma tana danne dariya yana ganinta sai ya dakata yana faÉ—in" Dariya ma kike yi ko ? To Allah ba zan É—auko ba."
"Afuwan haba Nawan, Aji na ajin zuciyata."
Haka ta faÉ—a har ta na masa fari Mirmishi ya yi kafin ya ce"Eh mana tunda kin sakani aiki ba, dole ki yaudare da kalamai mana."
Haka ya je ya ɗauko mata shima ba ta karɓa ba, ta ce hannunta ba kyau ya kai mata kirchen, da sauri ya shiga ya sauke mata samman wani faranti har yana sauri ya fita ta bi shi tana Faɗin" Ka tayani mana,ko gasa buredin Aji"
Ko juyowa bai yi ba ya fice yana faÉ—in"Yunwa nake ji, don Allah ki yi sauri."
Daman ta san ba zai tsaya ba ba ta san me ya sa ba baya son ta yata aiki ba, aiki in dai ba shi ya yi niyya ba ita kuma tana so ta ga suna aiki tare cikin soyayya da ƙauna.

  Bayan ta gama fasa kwan sai ta tuna bata yanka albasa da kayan miya ba, wanke hannayenta ta yi ta yanka buredin ta saka masa butter ta saka shi cikin oven yunda Aji ba ya son gasaahen buredi da ƙwai ya fi son shi da Butter ya yi taushi.
Gani  ta yi aikin baya mata sauri tana yanka  su tattasai, ta ƙwalama gogan kira ya ƙi amsa mata sai ta da ƙara ɗaga murya sai ga shi a bakin kitchen ɗin lokaci ɗaya yana faɗin"Wai na ci miki bashi ne Mimi? Kada ki ce za ma ki ƙara aike na domin nima yunwa ta saka ba ni ma da kuzari."
Ya faɗa yana harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa, har ya na wani kauda kai ganin haka ya sa da sauri ta marairaice tana faɗin" Aji to ka kama min na gama da wuri mana."
Hararanta ya yi kafin ya yi mgana da tare shi da shagwaɓa tana faɗin" Don Allah haba mana."
ÆŠaure fuska ya yi kafin ya ce"Me kuma zan yi yanzu?
"Albasa za ka yanka min don Allah."

  Ido ya zaro kafin ya ce"Albasa? Mugunta ko? Kin san fa ranar haka ki ka sakani ina ta kukan dole."

  Dariya takke so ta yi amman sai ta kanne ta lamgwabar da kai kamar za ta yi kuka kafin ta ce"Shike nan bar shi ma,"
Yadda ta yi mganar ne ya sa dole ya shiga Kitchen É—in ya na faÉ—in" Ina albasan?
Tana mirmishi ta nuna masa ya ɗauka sannan ya dauki wuƙa, ta nuna masa wani ƙaramin vol ya ɗauka ya fara yankawa a ciki yana ƙunƙuni ta na jin sa sai ta kanne ba ta yi magana ba sai da ta ga ya na ta yankawa manya manya sai ta kalle sa kafin Ta ce.

"Haba Aji, sun yi girma yankan"

  Hararanta ya yi har ya fara ƙanƙance ido kamar yajin ya fara tasowa.
Haka nan ya gama yanka mata sannan ya tace ruwan tea ɗin ya juye cikin flaks ɗin ruwan zafi, ita kuma ta fara soya kwan shi kuma ta ce ya duba buredin a oven, ya cire ya nuna mata ta ce sun gasu ta karɓa ta ƙara sakaa wasu buredin da butter ta maida, ita kuma tana cigaba da soyan ƙwan suna hira sama sama.

   A tare suka gama sannan Mimi ta gyara kitchen ɗin dakyar Aji ya taya ta ɗaukan Kayan karyawan nasu zuwa Dinning suka zauna saman karyawa, a lokacin ne yake ce mata mganar zuwan su kwami ba ta sai dai zuwa gaba.
Cikin mamaki ta kalle shi lokacin tana tura Buredi da ƙwai bakinta sai da ta kurɓi Tea sannan ta ce"Me ya sa?
Kai tsaye ya ce" Nima tafiya ce ta dole ta kamani zuwa Abuja."
Sai Mimi ta washe baki kafin ta ce"Gaske? Me za ka je yi?. Nan ya ke gaya kata yadda suka yi da Coach ita kuma ta ce"Gaskiya bai kyautu kace ba za ka je ba. To ya kenan?
Ya na kallonta kai tsaye ya ce" Tare za mu tafi Abujan sai ki je gida ki yi adadin kwanakin da zan yi, domin ba zan barki can ba tare za mu dawo."
Cikin gamsuwa ta ce" To can Bauchin fa?
Sai da ya kurbi Tea shima kafin ya ce"Sai dai zuwa bayan sallah tunda kinga yau sallah bai fi saura kwanaki goma ba."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Allah ya kaimu da rai da lafiya."
Ya amsa mata da Amin Amin, suka cigaba dahiiran su,  ba kasafai ya cika faɗa mata wasu abubuwan da suka danganci aikinsa ko iyayensa ba, sai in yan hiran na shi suna kusa. Kamar daga sama ta ji ya ce"Fatima kinsan burika na guda uku ne anan duniya?
Sai ta girgiza kanta amman ta maida hankalinta a kansa  tunda dukkansu sun gama ƙaryawan.

"Burina na farko shine Inna ta kasance cikin farincikin da kowacce uwa ke fata, Sannan burina shi ne na kai ta kasa mai tsarki ta sauke farali, na biyun kuma na mallakeki shi na cika wannan burin tunda na same ki, sannan na cika burin inganta rayuwar Inna abu É—aya ya ragemin na kaita kasa mai tsarki ta sauke farali, É—ayan kuma zan faÉ—a miki daga baya."

  Mimi ta yi shuru tana kallonsa kafin ta ce"In sha Allahu za ka cika burin ka, inna za ta je ta sauke fqrali ƙila ma ba sau ɗaya ba."
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ba ni da kuÉ—i yanzu duk na yi amfani da su Wajen hidindimu, ga kuma sallah na matsowa akwai sauran hidima amman ina so a wannan shekaran Inna ta je ta sauke farali In sha Allahu."
Mimi cikin jin daÉ—i ta ce"Allah ya amince,in kana bukatar kuÉ—i, akwai kuÉ—i a hannuna sai ka yi amfani dashi in ka samu sai ka maida min."
Bai ce mata komai ba, sai ta cigaba da faÉ—in" Kuma ga shi ma za ka je wannan taron na ji ana ta zuzuta ka iya taka leda nasan za ka iya kaiwa matakin kaiwa A kungiyar kwallon kafa ta Nageria."
Sai a lokacin ya ce"Ni fa ba ruwana da wannan, in da na ke ma ya isheni Fatima a baya ban taɓa tunanin zan kai haka ba, Shi ya sa ban cika son tusa kaina ba,  matsayin da na kai a yanzu ma Ubangiji ne ya kai ni, ina kuma gode masa ban sani ba ko nan gaba Ubangiji ya ƙara dagani amman yanzu ni dai ba zan tusa kaina ba. A hakan ma Alhamdulillah."
Mimi ta na so ta kara mgana amman sai ya dakatar da ita miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana na faɗin" Zan yi wanka Fatima."
Sai ta miƙe suka jera zuwa cikin Bedroom ɗin su kowanne na sake sake a cikin ransa.
Chapter 61 · 0% Book details