Sashe 15
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Mansoor Aji kuwa yunwa ta saka sai da ya biya ya siya nama da lemu sannan ya koma gidansa, rabonsa da abinci tun eea ɗin da ya sha da safe. Sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci ya ɗora da lemu.
Tunaninsa yadda zai tunkari Mimi ne, Dama tuni ya ke so kiran ta amman ba shi da dalili amma tunda yanzu Baba ya yi mgana ya samu abun fakewa.
 Yana kwance daga shi sai hajeren wando ba riga ya ɗauki wayarsa ya laluɓo Lambar Mimi da ya yi mata saving da LIFE PARTNER , Sunan ba iya rubuce ba ne har a gaske ma itace cikon rayuwarsa, ba wanda yasan ma sunan da ya saka mata wayarsa kenan hatta ko da ita kanta.
Yana kiranta sau ɗaya ya dauka da rawan jiki za ta ɗauka sai ga shi sai da ya yi mata Missed call biyar ba ta ɗauka ba, kuma shi ya san ba ta da ɗabi'an barcin wuri yana da tabbacin Idanuwanta biyu.
Nan da nan wata zuciyar ta harzuƙa shi, kamar shi Mimi za ta yi ma wannan wulaƙancin?
Sai kawai ya shareta bai ƙara kira ba amman kuma ya kasa sukuni har ya kwanta amman ya kasa barci yana ta juye Juye.
Sai kawai ya sake ɗaukan wayan ya ƙara kiranta har sau uku ba ta ɗauka ba.
Saboda ɓacin rai har wani duhu duhu ya fara gani kawai sai ya shiga wajen saƙo ya rubuta mata haka.
 "Ni ne za ki wulaƙanta Mimi? ni ko? To ya yi miki kyau."
 Ya gwada ne domin ya samu tabbacin tana ganin nashi ko ba ta gani ba?
 Hasaahen shi ya zama gaskiya domin ba daɗewa, sai ga martanin saƙon ta.
 "Maganar saki ne? Kada ka damu za ka iya turomin ta text nassages, ko kuma ka aiko min da takardata gidan Hajiya ko wajen Daddy."
 Idanuwansa har rawa suke yi da ya karanta ßakon Mimi, bai san lokacin da ya yi mirmishin takaici ba, lalle ma wannan yarinyar da shi za ta yi wasaa ko?
"Ina jiran sammaci ne."
 Abin da ya aika mata da shi kenan, amman ha wajen bayan awa ɗaya waya na hannunsa ya na gadi amman ba ta dawo masa da amsa ba.
"Kin yi shuru? Ko kin fara karaya ne?
 Haka ya sake turamata nan ma shuru. Sai ya koma ya sake kiranta kawai sai ya ji ta danna masa lamba busy.
Wayar ya bi da kallo a fili ya furta" Kan uba can!"
Haka ya faɗa, har ya na wani hararan wayarsa, wai shi ne Mimi ta kashe ma waya? Wasa wasa kasa sukuni ya yi yana kwance yana ta juye Juye ya kasa barci har cikin dare sai da ya tashi ya kara kiram Mimi ba ta ɗauka ba har asuba ma sai da ya kara kiranta ta kuma ƙara danna masa busy
Ransa ya kai kololuwar ɓaci.
Yana kiranta yana Hargagi shi kaÉ—ai.
"Mimi ki ɗaga kiran kafin ranki ya ɓaci."
 Amman ba ta ɗaga ba Daga karshe ma wayarta a kashe ya ji. Haka nan ya shirya ya tafi camp suna da morning traning, amman kowa ya gansa yasan ran maza a ɓace ne daga can gida ya wuce ya gaida Inna Meri amman tunda ta ce lafiya lau ba ta ƙara masa mgana ba haka ya gama zamansa Shuru kuma ga shi ya na jin yunwa amman Inna Meri ba ta bashi Koko da Kosan da ta yi ba, har ya gaji ya yi mgana kaii tsaye Inna Meri ta ce ya kare kuma yana ganin shi ga shi a fulas tunda a gabansa ta juye.
Daga nan yasan saamun Kwanciyar hankalinsa da kuma ganin farin cikin Inna shi ne ya je ya samu Mimi su yi mgana.
 Yana durkushe a gaban ta ya ce"Inna yau zan je na samu Mimi mu yi mgana za ta dawo in sha Allahu."
 In dutse na mgana to Inna Meri ta yi mgana haka ya kwashi sanyin jikinsa ya fice. A tsakar gida ya ga Maeesha kazama ce ta fito daga ɗaki ta na tsintar da yawu nan kofar ɗaki, kusan amai ya tashi yi kallo ɗaya ya yi mata ya fice ganinta ma ya sa ya tuna da Maganar da ya ce zai yi ma Auwalu.
Yana hanyar komawa gida ya kira shi ya gayamsa cewa ya ja ma ƙaninsa kunni ya tsawatar ma matarsa domin Inna Meri ba sa'arta ba ne, in kuma bai iya ja mata ba to shi zai yi abin da rayuwaka za su ɓaci, Auwalu ya ba shi hakuri ya ce zai yi mgana da Saddiqun.
Shi daman yasan wannan zaman ai ba za'a wanye lafiya ba.
 A daran ya so zuwa gidan Hajiya da fakewar ba zuwan kanshi ba ne saboda Inna ne da Baba Ahalin zuwan kanshi ne, domin har a daran ya kirata a kashe, Bai samu zuwa ba saboda ya samu wayar Coach Team ɗin kwallon kafa na Anguwan Jeka da Fari suna bukatar a shirya musu wasan sada zumunci da Team ɗin Tudun wada, kuma a matsayin sa na Captain na Gombe united gabaɗaya yana kula da sauran kananun Team din dake Jiharsa, abin da ya ɗauke masa hankali kenan da zuwa Gidan Hajiya in ya fita tun safe sao dare ba ya samun zama.
 Sai da aka shirya wasan da za a buga a Stadium ɗin su na cikin gari, sannnan ya samu kansa, kwana huɗu tsakanina ya shirya da Daddare saboda har a lokacin Inna ba ta masa magana daga gaisuwa shike nan ko a waya ya kira suna gaisawa ta ke ce masa sai an juma, Mu'azzam ma yanzu ya fahimci ya daina goyon bayansa su Nasir daman an yi rabuwan ba daɗi shi zai neme su kuma bai neme su suma suka ce sai dai a dauwama a haka har gwarama Ahmad sun yi mgana sau biyu.
 Shigar farar shidda ya yi har da hula, wani farinciki ya ke ji zai je ya ga Mimi amman sai ta raina kanta shi za ta yi ma wulakanci Saboda ta ga yana nin ta ko? To zai gaya mata ba saboda ta isa ba ne, Saboda Inna ne da Baba, Ya tuna har Babansa Kabiru na Bauchi ya kira shi kan maganar abin da ya ba shi mamaki ce masa ya yi ya zo gidansa ya zaɓi mata. Sai ya ce masa ai bai saki matar ta shi ba sai kawai ya ce"To ka sake ta mana, ba an ce ba ka son ta ba?
Cikin mamaki ya ce"In ji waye ya ce ba na son matata?. Kai tsaye ya ce" In ji Gwaggon ka Yalwa ta ce ka ce ba ka son ta ko ƙarya ta yi maka?
Baki ya riƙe ya na mamaki, kafin ya ce"A'a ba ta yi ƙarya ba. Sai dai in ba ta ji da kyau ba, Baba Na gode da yayin ka amman ba na jin bayan Mimi zan iya auran wata macen, matata na sona nina kuma ina sonta, kawai dai akwai dalilin da ya sa abubuwa suka yi faruwa ne, kuma ba laifi ba ne in ka ɓata ma mace rai ta yi yaji, in ta je gida ta huta nima na huta zamu daidaita daga baya.".
Da haka ya samu ya kashe bakin Baban na shi, wai ya ba shi mata? Bai jin ma in ya yi wani auran zai iya yin adalci. Mace ɗaya ce a cikin zuciyarsa tun farko ita ya zaɓa a yanzu ma ita ya kara zaɓa.
 Yana tafe ne a mota yana wannan tunanin, Sai ga shi a kofar gidan Hajiya ya yi jon megadi ya leko da ya ga shi ne suka gaisa ya buɗe masa get ya shiga da motarsa ciki,bai yi niyar shiga can ciki ba ba sai ya ɗauki waya ya Kira Mimi amman ba ta ɗauka ba sai ya cije baki ya tura mata saƙo.
 "Ina haraban gidan Hajiya ki fito da kayan ki ina jiran ki.".
 Shuru shuru sama da mintina ashirin ba Mimi, tun yana mota sai ga shi ya fito, ya jingina da motar ta shi.
Haushin kanshi ya fara ji yadda ya tsaya Mimi na yi masa wulakanci ta manta hala har yanzu shi mijinta ne? Ya kamata ya nuna mata har yanzu tana ƙarkashinsa ne.
Yana wannan tunanin sai ga sakonta ya shigo jiki na rawa ya buÉ—e.
"Ka shigi cikin gida. Domin ba zan iya fitowa ba."
 Ya yi jim yana tunanin wai ita a dole za ta rama ne? Sai kawai ya yi yar dariya ya kulle motar ya nufi hanyar falon Hajiya kofar na kulle sai da ya kwankwasa Baba Uwani ta zo ta buɗe masa tana ganin shi ne ta gaishe shi cikin girmamawa a bakin kofar ya tsaya yana faɗin" Mimi, ki yi mata mgana ki sanar mata ina jiranta."
Ya faɗa yana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunsa na hagu.
Baaba uwani ta yi shuru kafin ta ce"Binta ba ta nan ta yi tafiya. Sai dai Hajiya shigo ciki ka zauna bari na gaya mata zuwan ka."
"Ba ta nan? Ta yi tafiya?
 Haka ya riƙa nanatawa a cikin tansa Bai san ma Baba Uwani ta koma ciki ba yana tsaye ne yama jin zufa na keto masa Mimi ta maida shi wani cartoon ne ko kuwa wani sakarai ko sauna? Ba ta nan? To gidan iban wa ta je da auran sa a kanta?
Yana wannan tunanin yaji muryan Hajiya na faÉ—in" Na yi fushi tunda sai yau nake ganin Megidan nawa."
Dalilin da ya sa ya É—an saki fuska kenan ya tako kafarsa zuwa cikin falon ya ysaya ya cire takalminsa sannan ya karisa kusa da Hajiya ya zauna a kasan cafet.
Dai dai lokacin da Baaba Uwani ta kawo masa ruwa da lemu da ƙaramin kofi.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC