Sashe 74
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Baba ya kirata da mafi soyuwan sunan da ya ke kiranta da shi wani lokacin, ta ɗago ta kalle shi daga shi har ɗan na shi sun maraiiraice sai ta ji wani abu a ƙasan ranta, Da sauri ta kauda kai tana faɗin"Shi mai uba ko? Ya je ya ɗauko ka, kun yi min taron dangi saboda ni kunga nawa uban ya mutu ko? Da Sauri Baba ya ce"Ko ɗaya, ke yanzu kin fi wata mai uban, Allah ya ba ki ƴaya sanyin Idanuwanki waɗanda suka lulluɓeki da alheri sannan kina da ni, ina da tabbacin kin gama samun komai a nan duniya sai fatan cikawa da Imani kawai Maryama
Inna Meri kauda kanta ta yi tana share ƙwallah kafin ta ce"Shike nan amman ya sani wannan ne na farko kuma na ƙarshe wallah tallahi in ya sake aikata wani kuskuren sai ya rasa Binta."
Da sauri Mansoor ya ce"Ba zan ƙara ba Inna, ki yarda da ni."
Kallonsa ta yi kafin ta ce"In ka ji irin haka ya shige ka, ka kira sunan Allah domin ka samu natsuwa ina ƙara yi maka nasihan cewa ka koyi sarrafa wannan zuciyar taka saboda watan wata rana za ta kai ka ga aikata abin da ko kaso ka gyara ba zai taɓa gyarun maka ba."
Kansa na ƙasa ya ce"In sha Allahu."
 Baba Ɗanjuma na Mirmishi ya ce"Mun gode, Sai ki yi mata mgana ta fito su tafi, In sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba."
Inna Meri ta gyara zama kafin ta ce"A'a.."
A tare suka kalleta cikin mamaki kafin ta cigaba da faÉ—in" Itama macece mai Æ´anci ita kuma ya yi ma wannan laifin zan kirata a gabanka a gaban shi, in ta amince ta masa afuwa ba zan hana ta bin sa ba amman in har ta ce ba ta hakura ba, ba zan iya hana kaina goyon bayanta ba."
Baba ÆŠanjuma ya ce"Ba ma za'a yi haka ba, Kirata ta zo nima na ba ta hakuri."
Inna Ta mike lokaci ɗaya tana faɗin"Ba ma ta da lafiya, gwara ta zauna waje na har sai ta warware wannan mara tunanin magana kawai zai iya gasa mata da zai ɗaga mata hankali wani abu mara kyau ma ya faru.
"Me ke damun ta?
 Baba Ɗanjuma ya tambaya kafin Inna ta yi mgana da sauri Mansoor ya ce"Baba Inna ce ta ce Mimi na da ciki, tsakani ga Allah kula da mai ciki ai sai uban cikin ko?
Inna ta ji kunyar duniya ya kamata Baba ma kai ya kauda kafin ya ce"Wannan gaskiya ne. To to Allah ya raba lafiya."
Inna meri kuma daƙuwa ta maka ma Mansoor kafin ta ce" Ba ka da kunya ko?
Sai a lokacin ya tuna tabargazan da ya yi da sauri ya maida kai ƙasa yana sosa keyarsa ya na yar dariya.
Walida Inna ta kwalama kira bayan ta fito sai ta ce ta kira mata Binta.
Mimi daman tana zaune nem Jin Inna na kirata ya sa ta mike ta zura hijabin Walida zuwa Falo tun da kuma ta fito gogan ya kafe ta da ido kuma maganar gaskiya ta rame ta yi wano fayau to wai daman haka alamun cikin yake? Me yas a shi bai gane ba?
 Kusa da Inna ta zauna kanta na ƙasa ta gaida Baba ya amsa cikin sakewa lokaci ɗaya yana faɗin"Ya jikin Fatima? Kanta na ƙasa ta amsa da sauki ya ce Allah ya ƙara lafiya Mansoor a ka bari da amsawa Inna ta wurgeshi da maficin Hhnunta sai da ya same shi shi ya sa ya kama bakin shi.
Bayan tattaro duka bayanan Baba Ɗanjuma ya sake ba ta hakuri da cewa"Ki yi hakuri kin ji ko Fatima? Itama uwar taki mun ba ta hakuri kuma ta ce ta hakura amman mu tambayi izinin ki, ina so ki cire komai a ranki ko domin lafiyan abib da ke cikin ki, ki tashi ki bi mijin ki kin ji ko? Bai kyauta ba mun masa faɗa ya kuma ya ce ba zai ƙara ba, mu abin da kika yi mana na ɗauƙan mu iyayen ki ya fi komai yi mana aɗi Allah ya yi muku albarka Allah ya zaunar daku lafiya tare da zuru'a mai albarka."
Wannan karon gogan a cikin ransa ya amsa sai Inna ce ta amsa a fili. Mimin kanta na ƙasa ta kasa mgana.
"Kin yi shuru Fatima? Ki ce wani abu mana."
 Baba Ɗanjuma ya tambayeta. Sai ta ƙara sadda kanta ƙasa kafin ta ce" Na hakura Baba, ni daman saboda zargin yake yi min ne ya sa na kawo muku wannan mganar."
Da sauri Baba ya ce"Eh wlh, kuma kin kyauta mganar zargi ai babban mgana ce, an yi masa mgana ba zai ƙara ba."
Sai Mimi ta jinjina kai kafin tac ce"Shike nan zan bi sa mu koma."
Baba ya ce Alhandulillah Allah ya yi miki albarka Mansoor kuma har da sauke Ajiyar zuciya.
"Amman kuma ina da sharaÉ—i. SharaÉ—in nawa kuma ina so ku zama shaida Baba da Inna.."
 Haka ta faɗa kai tsaye tana kallon Aji da ke kallonta, Inna ta yi mirmishi kafin ta ce" Faɗi sharadin ki, muna goyon bayan duka hukuncin ki Binta."
Sai ta kauda kanta kafin ta ce"Na yi hakurin zargin da ya jefeni da shi, amman ku zama shaidata wlh tallahi in har ya ƙara maimaita wani abu makamcin haka zan tafi, kuma in na tafi bazan dawo ba, domin ba zan iya zama da wanda bai yarda da ni ba sannan ba zai iya shaida na ko da a bayan idanuwana ba ne."
Baba ya jinjina kai kafin ya ce"Gaskiya ne, In sha Allahu ma haka ba zai ƙara faruwa ba." Inna Meri kuma ta ce"Kin yi min dai dai, ni da kaina wlh in ka ƙara sai na tursasa maka ka saketa, in dai kai ba ka san baiwar da Allah ya yi maka ba to ka in ka yi sakaci Binta ta bar ka sai dai ka mutu ba ka yi aure domin ban ga macen da za ta yi hakuri ta zauna da kai da mummunan hallayarka na rashin lissafi ba. kishi ai ba hauka ba ne sai ka hana yarinya walwala kawai saboda kishin ka na banza? To wlh ka shiga hankalin ka tun kafin wata rana ka yi ta kuka ba mai share maka hawaye."
 Baba Ɗanjuma ya ce"Gaskiya ne, amman duk hakan ba zai kai ga faruwa ba in sha Allahu"
inna Meri ta harari bangaren Mansoor kafin ta ce"Shi dai ya sani,damar ta karshe gare shi, ki je ciki ki shirya sai ku tafi."
Mimi ta miƙe a sanyaye ta wuce Mansoor ya bi ta da kallo, shi yanzu ai yana cikin TSAKA MAI WUYA. Ya san yana da kishi amman kuma dole ya koyi sarrafa kishin sa matukar yana son zaman lafiya.
Bayan tashin Mimi nasiha faÉ—a haka Inna da Baba suka tasa shi suna yi har sai da Mimi ta fito Walida ta rakota da jakarta da kayanta da Walidan ta wanke mata.
Inna ta kalli Mimi lokaci É—aya tana fadin"In kina bukatar wani abu ki gaya min sai na saka Walida ta kawo miki kin ji ko?.
Sau ta gyaɗa kanta, so take yi ta ce a zuba mata tuwo amman ta kasa mgana sai Walida ta yi ma raɗa ita kuma ta gaya ma Inna. Mirmishin su na manya ta yi domin ta na da tabbacin domin Mansoor za ta ɗauki tuwon nan sai ta ce Walida ta zuba musu a kula su ta fi da shi.
 Mansoor ya ce Baba ya zo su fara sauke shi a gida yace a'a zai samu mai mashin su dai su tafi. Har bakin mota Walida ta rakata ta saka musu tuwon a bayan mota da jakar Mimi da kayanta tare da magungunta. Har su ka bar anguwan nan kallo Aji bai ishi Mimi ba shi kuma sai ya rasa abun cewa, ya kalleta sai ya ga ta na kallon gefe ne ba ta ma son kallon shi, sai ya rasa abun cewa sai da ya ji ta na tari sannan ya ce"Sannu, ko a rage A.c ne? Ta yi masa banza da kansa ya rage iskar motar sannan ya koma yana faɗin" Har da mura ke damun ki ko?
Kamar ba ta motar haka ta yi masa, Ya yi ta taƙalan mgana amman Mimi ko uffan ba ta ce masa ba, har suka isa gida yana hon megadi ya buɗe musu get suka shiga gidan yana gyara parking ta yi saurin buɗe motar ta fito, baya ta buɗe baya ta ɗauko jakarta da ledan mganinta da sauri ya zagayo ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin"Ke da ba ki da lafiya ina ke ina ɗaukan kaya Mimi?
A sanyaye ya yi mganar, sai kawai ya ga ta ƙara kauda kai ta sakar masa kayan hannunta ta juya a hankali ta nufi cikin gida shi a ka bari da kwaso kayan har da kwandon da Walida ta zuba musu tuwon ko da ya shiga falon har ta shige ciki ya duba ba ta a bedroom ɗinsu a she ɗakinta ta shige a bin ta yana shiga kuma ya ganta ta tuɓe za ta shiga wanka, bai yi mgana ba ganin kallonsa ma ba ta san yi, dole ya koma falo ya zauna yana shafa kansa.
 Mu'azzam ne ya kira shi suka yi mgana ya ce masa Inna ta hakura, shima sai da ya ƙara yi masa faɗa sannan suka yi sallama Hibba na gefensa da katon cikinta ta ce"Kai ni dai na kasa gane halin yaya Mansoor."
Mu'azzam ya ce"Ya dai kusa zama uba watarana sai labari."
Hibba ta zaro ido kafin ta ce"Mimi na da ciki?
Sai ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta saka shewa har suna tafawa da Mu'azzam a fili ta ce wa ya ga Yaya Mansoor da ɗa akwai shan kallo, Aji baya jin kunyar faɗan Mimi da na ciki shi a ganinsa abun alheri ne miye kuma na ɓoye ɓoye.