Sashe 30
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mu'azzam ya ji tausayin Yayan nashi cikin kwantar da murya ya ce"A'a ni fa ina ganin akwai abin da kake yi mata ne ba ta so, in za ku zauna ku samu daidaitu za ta dawo in sha Allahu."
Aji ya dafe kansa lokaci ɗaya yana faɗin" To ta ƙi ba ni damar haka? Allah ba zan mata faɗa ba zan saurareta wannan karon, sannan ina ji a zuciyata zan iya mata abin da ta ke so, mganar gida kuma sai in da take so za ta zauna na janye duka sharuɗda na a kan ta."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tagumi kafin ya cigaba da faɗin "Mu'azzam na taɓa ga ya maka ina son Mimi? Na taɓa ga ya maka itace rayuwata?
Ya faÉ—a yana mai kallon É—an uwan na shi Mu'azzam ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce" Na san kana sonta mana amman abin da ban gane ba me ya sa bayan ka same ta ka kasa nuna mata wanman son? Me ya sa kuma ka ga ya mata ba ka sonta?
"Ba ni da wani dalili Sai na jin hauahin abin da ya faru a baya. Sannan Allah ni fa ba gaskiya na faɗa ba, kawai dai na faɗa saboda ta ji haushi, kuma ita ta ja na faɗi haka saboda ita ta riƙa ja na da maganganu."
Haka ya faɗa yana rike fuskarsa yana sakin huci Saboda tsoro ne ya shigesa tsoron rasa Mimi a wannan karon. Har ga Allah tabon dake zuciyarsa ya fara raguwa ga shi har ya zo Office ɗin kaninsa ya zauna suna mgana kai, ka ba ma zuciyarka aminci ma wani salama ne zama cikin kunci ba shi da amfani. Yau ɗin ranar sakin duk abin da ke damunsa ne haka ya riƙa yi ma Mu'azzan zan tuka na fita hayyaci da nadama.
Sai Kawai Mu'azzam ya ce"Ina da shawara me zai hana in ka koma ka nemi Babanta Alhaji Hamza? Tsohon Sanata tunda shine Waliyinta?
Aji ya yi shuru kafin ya ce"Da na ce ba zan je ba, amman yanzu ai ba ni da zaɓi. Zan je in sha Allahu da zaran na koma."
Sun É—an tattauna Mu'azzam na kara gaya masa in ya je ya kwantar da kai tunda sulhu ya ke so, Bayan nan suka gangaro kan mganar gida Mu'azzam na faÉ—in Bintu ta gaya mai Inna wulakanci take kwasa tun bayan dawowar Matar Saddiqu bangarenta.
Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ka san Allah na kusa ɗauke Inna daga gidan, kawai dai ba na so Baba ya ga na nuna masa shi ya gaza ne."
Mu'azzam ya yi saurin cewa" Ni ma na yi wannan tunanin. Tunda Dai Magajiya ta fi ƙarfin Baba ba ya iya tsawarta mata, Inna kuma kasan halinta ko dukanta za su yi ba za ta taɓa mgana ba."
Mansoor ya koma ya jingina da Kujeren da ya ke zaune kafin ya ce" Kar dai a yi wani abin da zai ɓata min rai, zan ɗauke Inna gaskiya a wannan gidan."
Mu'azzam ya ce"Ko Yaya Amina abin da ta ce kenan gidan duk ba daÉ—i."
Sun cigaba da tattaunawa har kan batun su Walida Mu'azzam ya ce hakan ya yi dai dai, Aji yac e da zaran ya koma zai nemi Auwalu kan mganar ita Mariya.
Nan su ka shantake sai bayan oa'asar sannan suka ɗumguma zuwa gidan Mu'azzam d ke BUK old site. Sai dai Hibba ta ga Yaya Mansoor kamar daga sama itama bakinta kamar zai yage, faɗi take yi" Lalle muna da babba baƙo, sannu da zuwa Yaya Mansoor"
Ya amsa mata cikin sakewa abincin da ta yi sun fi kala huÉ— nan suka baje suka ci suka sha suna ta hira kamar kada su rabu, Mu'azzam ya kira Inna ya sanar da ita ga shi ga Baban Inna itama kanta ta yi mamaki ta ce ya kyauta.
Sun É—auka ma ko kwana zai yi ya ce ba zai kwana ba. Sanin halin shi ya sa Mu'azzam bai matsa masa ba wajen shidda da rabi ya kai shi tasha ya hau mota sai da suka tashi ya dawo gida tafiyar dare suka yi sai wajen sha biyu ya iso Gombe, bai je gidansa ba a Camp ya kwana kuma evening Traning suke dashi shi ya sa tun bayan sallar asuba ya kwanta barci ya kwashe shi. Bai ta shi ba sai da ya ji ana ta kiran wayar sa yana tashi ya Duba sai ga inna ta kira shi Bintu ma haka.
Sai ya bi bayan kiran yana duba Lokaci goma saura na safe,
Wayar Inna ta na ƙara ba'a ɗauka ba, yana cikin neman Bintu sai ga kiranta sai ya ɗauƙa da sauti gabansa na faɗuwa yana tunanin ba lafiya.
Kuka ya ji ta na yi masa, da sauri ya miƙe ya na laluban rigarsa.
Cikin fargaba ya ce"Bintu me ya faru ne?
"FaÉ—a ake yi a gida saboda Matar Saddiqu ta dagi junior har sai da ta ture shi ya fasa goshi, shi ne shi ne Walida ta yi magana Meesha ta ja ta da faÉ—a suka kama Kokuwa sai ta faÉ—i, Saddiqu na zuwa kawai ya rufe Walida da duka Inna ta zo ta hana ya tureta har sai da hannunta ya goce."
Bintu ta faɗa ta na shesshekan kuka, Aji ya ji wani abu ya taso masa a ƙasan zuciyarsa. cikin maimaitawa ya ce"Ta goce? Ita Inna ce ya gotar don uban shi? Lalle ne ma."
Haka kawai ya ce ya kashe wayar daman ya saka riga kawai sai ya zura takalmi ya É—auki key É—in mota tabbas yau Saddiqu zai fahimci yana cin darajan mai daraja ne amman tunda har tura ta kai bango yau za'a buga final É—in.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3007*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Allah kaɗai ya kawo sa anguwan Arawa lafiya. Domin a yanayin yadda ya tuko motar nan a fusace ne yana kuma ganfala gudu kamar zai ta shi sama. Motar ma kusan a karkace ya iya faka ta a kofar gidan ko key ɗin bai zare a jikin motar ba ya fito da sauri ya shiga cikin Glgidan abin mamaki har su Baba Sani da matan su suna gidan wai ace har Saddiqu ne zai ture Inna har sai da ta goce saboda rayuwa ta lalace gabaɗaya.
 Bangaren Inna Meri ya cika da mitane, su Gaje ma duk suna wajen abinn mamaki Baba Ɗanjuma ma yana wajen ko da yake ba abun mamaki ba ne tunda kaf ƴaƴan Magajiya da ita kanta sun fi ƙarfinsu lokacin da ya shigo ya iske magajiya ta riƙo Maaesha wacce ke wani lamgwaɓe wa tana kuka kamar wacce haihuwan ce ta zo, Binta na Kofar ɗakin Inna tana harare harare, Inna Meri na zaune a kasa a kofar ɗakin ta kanta a kasa Walida na gefenta tana kuka kamar ranta zai fita junior kuma na raɓe jikin Bintu ga goshinsa sannan ya sunduma sauran kuma duk suna tsaye suna kallon Magajiya na ta bala'i tana faɗin Saboda mugunta mata da ciki za ki ja ta da dambe?
Lokacin da ya shigo Saddiqu ba ya gidan ya je É—auko mai adadaita domin kai matar sa asibiti.
 Yana tsaye daga bayan su ba wanda ma ya san ya shigo gidan ya goya duka hannuwansa a bayansa yana ƙokarin sarrafa ɓacin ransa domin ji ya ke yi kamar ya je ya hambare Magajiya a wajen nan, kuma abun haushi har Baba na wajen amman ya kasa tsawarta mata sai Harira ce ta kalleta lokaci ɗaya tana faɗin" Gaskiya Magajiya kina faɗan rashin gaskiya ne, shi abin da Saddiqun ya aika ma Meri da Walida ya yi dai dai kenan? Sannan ita matar ta shi da ki ke faɗin ba ta da lafiya ita ce ta samu karfin ture wannan yaron har sai da goshin sa ya samu rauni? Ya kamata mu rika gayama junan mu gaskiya Magajiya bakya kallon abin da ƴaƴan suka yi a matsayin laifi sai dai ƴaƴan wasu."
 Kafin ma ta dire maganarta Magajiya ta taso mata da cewa" Ba wani, yaro ya yi mata rashin kunya ba za ta dake shi ba? Ta ce ma mgana kawai ta yi masa ya daina zubar mata da ruwa a kofar ɗaki saboda sauro kawai sai ya shiga ɗaki yana kuka ita kuma wannan mara kunyan ta zo rama masa, in tana da mutumci ai Saddiqu Yayanta ne amman ta yi ma matarsa rashin Kunya Aisha ta ce tana mgana ne ta ji ta cacumeta da dambe ko tausayin halin da ta ke ciki ba ta yi ba. Ban ga laifin Saddiqu domin ya kama ta da duka ba ai ta yi abun dukan ne sannan ita kuma Meri son kai ne da gulma miye na kokarin hana Saddiqu ɗaukan hukunci? Kuma ba da gangan ya tureta ba ita ta ja ma kanta, ai shi ne abin tausayi shi da yana zama zamansa an jawo masa wata laluran kashe kuɗi, in ma Allah ya takaita abun ya tsaya a iya kashe kuɗin kenan."