← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 93

Sashe 42

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faÉ—a ya na kureta da kallonsa, kasa jurewa ta yi sai ta kwace kafaÉ—anta ta matsa baya tana sauke numfashi.

"Allah da gaske nake yi, ba ki yarda ba ne?

  Numfashi ta ja ta sauke kafin ta ce" In hakane kana sona? Me ya sa da na ce zan tafi ba ka hana ni ba? Cewa fa ka yi wai is better na tafin"
Cikin dafe kansa ya ce"Mimi. Ke wai ba ki san gatse ba ne? Ni fa gatse na yi miki ban taɓa tunani  za ki yi fushi ki taho gida ba wallahi"
Wata harara ta yi masa kafin ta ce"Ai dole na zauna tunda ni ba ni da zuciya sannan ban san ciwon kaina ba."
Da sauri ya É—aga hannayensa sama lokaci É—aya yana faÉ—in"ba haka na ke nufi ba, ni dai ki yi hakuri ki saka ranar da za ki koma don Allah."
Shuru ta yi masa ganin haka ya sa ya matso kusa da ita, ba ta sani ba sai jin maganarsa kawai ta yi a kusa da ita.

"Kin ji My Mimi? Komai ya wuce ko?

  Da Sauri ta matsa can karshen kujera kafin ta ce"A a.
Cikin mamaki ya ce"To me ya rage? Na amsa duka laifukana na kuma ba da haƙuri."
"Akwai saura?
Haka ta faÉ—a ta na kallonsa shima kai Tsayen ya ce"Me ya yi saura kuma?
Kai tsaye ta gyara zama tana faÉ—in" Matsayin Mahaifina a wajen ka nake son sani yanzu, domin ba zan cigaba da zama da kai kana kiransa da azz.."

"Ya isa. Haba Mimi na ce fa na yi nadama ki yi hakuri mana."

  Ya katseta da sauri domin yana jin kunyar sunan da ya kira mahaifinta da shi , ita kuma sai kuka cikin yar shagwaɓa ta ce" Kai fa ka kira shi da hakan"
Da sauri ya ce"Ai ban yi gaddama ba, na tuba bazan kara ba kin ji ko?
Sai ta É—ago tana kallonshi Idanuwanta duk hawaye kafin ta ce"Ka na nufin ka yafe duk abin da ya faru.?
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Eh na yafe masa, na gane riƙo ba shi da amfani, na yi miki alkwarin ba zan ƙara duban ki da wannan abun ba. Sannan zan ɗauke shi a matsayin kaddara in sha Allahu."
Cikin jin daÉ—i ta ce"Da gaske kake yi?
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" In sha Allahu, Allah ya jiƙan Abi ya sa ya huta."
Mamaki ya kama Mimi ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ga hawaye lokaci É—aya cikin girgiza kai ya ce"Kin ji daÉ—i? Ina fatan komai ya wuce?
Ta na goge hawayenta ta ce" Eh, tunda ka yarda ka yi kuskuren  kuma ka amsa za ka gyara, shike nan nima na haƙura."
Cikin jin daɗi ya ce"Nago de, to goge hawayen shagwaɓɓiya mai kuka da dariya kawai."
Hararansa ta yi ba ta yi mgana dukkansu zukatansu ya cika da farinciki.

"Yaushe za ki koma? Yau ko gobe?

   Kallonsa ta yi a karkace kafin ta ce"Ko zan koma sai ka amince da wasu sharuɗɗai na nima, a baya kai ka saka naka nima a yanzu lokacina ne ma gindaya maka naka."

  Baki sake ya ce"Topha, ka ji wata sabuwa."
Tana murgaÉ—a masa baki ta ce"Ba dole, in ba ka amince ba sai n ace na fasa komawa."
Da sauri ya ce" WANE AJI? shi É—in banza zayyano su ki kaddara ma duka sun tabbata."
Tana dariya ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Komawa na tare da wannan sharuɗɗan guda ɗaya in ka tsallake ba zan koma ba."
Tagumi ya yi kafin ya ce"Ya na iya? Tun da ɓarawo ya shiga hannun mata ai ya shiga uku."
Yadda ya yi mganar ne ya sa ta ƙyalkyalce da dariya  Shi kuma ya na kallonta da Mirmishi ta juya kenan sai ya kira sunanta.

"Mimi.."

  Sai ta juyo tana kallonsa sai kawai yace"Amman dai mganar kin samu ba da gaske ba ne ko?
Tana É—age masa gira ta ce" Da gaske ne mana, in baka amince da sharuÉ—dana ba da shi za'a yi."
Nan da nan ya haÉ—e rai yana faÉ—in" Kin san dai kina da ma tarin laifi wajen Ubangiji, kin yi ta zuwa garuruwa ba tare da izinina ba, in kuma ban yafe ba Allah ba ki sha ba."
Kugu ta riƙe lokaci ɗaya da  bakin tana faɗin "Ba ka yafe ba ka ce! To ai da izinin ka na je ko'ina tun da kai ka ce na je duk in da nake so."
Zai yi mgana ta yi saurin cewa"Ka yafe ko ba ka yafe ba?
Yanayin yadda ta tsare shi da ido ya sa ya koma ya jingina da kujera kafin ya ce"Wannan shi ne a dake ka, sannan a hana ka kuka, ya na iya?  Na yafe."
Ya faÉ—a kamar ba ya so, Mimi ta saka masa dariya ta juya tana wani irin taku zuwa Koridin da zai sada ta da É—akunan su.
Shi kuma ta barshi da bin ta da kallo kamar wani sauna kira mana shashaaha.

  Ta na shiga ɗakinta ta buɗe wata ƙaramar jakarta dake rataye ta ɗauko biro da takarda a cikin wani Memo ta yanka na bikin Biban su Dukky ne. Da farko ba wannan zencen sharuɗɗan amman yanzu ta ji ta na so shima ta jarabasa, kai tsaye ta fara rubutu bayan ta zauna a saman gado, wasa dai da ta kusa cika takardan nan da rubutu sannan ta ninke ta, ta koma falon ta miƙama Aji lokaçi ɗaya tana faɗin"Sai ka koma gida sannan ka buɗe ka karanta a tsanake, in ka amince sai ka yi ticking ɗin duka sannan ka saka hannu a ƙasa, nima sai ka dawo min da takardan na saka hannu, sannan saɓa alkwarin mu dai dai yake da sunan ba zan koma ba."
Karɓan tarkadan ya yi lokaci ɗaya yana faɗin" Kamar Interviuw ɗin ɗaukan aiki?
Hararansa ta yi da sauri ya ce"Sorry Matas"
Ita kuma sai ta koma tana wani hura hanci bai daÉ—e ba ya ce zai tafi saboda bayan mangariba zai gana da Coach É—in su ya ce yana son ganin shi, ko Hajiya bai tsaya ma sallama ba ya ce Mimi ta gaya mata da zai tafi ko rakiya ba ta yi masa ba sai da ya ce"Matas ba rakiya?.
Kai tsaye ta ce"Sai ka cike sharudÉ—anmu tukkunna"
Sai ya jinjima kai kawai ba tare da ya yi magana ba.

  Shi dai yana mamakin me ta rubuta? Me kuma take so? Ya san dai ba za ta ce kuɗi ba, Saboda zaman da za su yi da Caach ya sa bai samu damar duba takardan lokacin da ya koma ba.Sai wajen ɗaya suka gama Meeting ɗin ga shi ya gaji ga shi ya na jin yunwa amman hakanan ya kwanta bai duba takardan ba, da Safe kuma yana cikin barci wayar Inna ya ta da shi ta ce ya fita bakin Camp ɗinsu Walida ma jiran shi.
Ya yi ta mamakin lafiya riga ya saka ya fita ko da ya je ma ba kowa ya na shirin kiran Inna sai ga Walida ta sauka daga mashin, Da kwandon abinci riƙe rike sai da ya yi hawaye Allah sarki uwa.
Cikin ɗan faɗa ya kalli Walida yana faɗin"Inna ta ba ki wahala?  ba shago za ki tafi ba? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce"Eh, ita ta ce na biya na kawo maka.".
Sai ya karɓa yana yi ma Inna fatan Aljjana acikin ransa mai mashin ɗin bai tafi ba shi ya tsaya ta hau zai kai ta in da ta ke koyon Computer bai fito da ko wallet ɗinsa ba sannan ba kuɗi a hannunsa amman ya ce zai shiga gidan anjuma.

  Yana komawa ɗakinsa na cikin Camp ɗin ana Sake kiran shi yana dubawa sai ya ga Baba, sai bai ɗauka ba sai da ta katse sannan ya bi bayan kiran bayan sun gaisa, daya ke sun kwana biyu ba su haɗu ba shi fa tun barowar Inna wannan gidan anguwam bai ƙara komawa ba, ko kan maganar Mariya a camp Auwalu ya zo ya same shi suka yi mganar, kiran Baban ma saboda haka ne yana gaya masa waliyyan yaron sun zo suna bukatar a saka musu Shekara mansoor ya ce a saka a hakan ai kamar gobe ne, kuma tunda an yi bincike yaron da sana'arsa ɗinkin maza da mata yake yi kuma ba shi da wata matsala.
Sun tattauna kan maganar sannan suka yi sallama ya zauna ya ci wainar da Inna ta aiko masa sannan ya sha tea ya haɗa da soyayyen buredi da ƙwai.

  Yana gama ci ya natsa kawai sai ya koma ya kwanta ya yi ta barci tun yau ba su da Traning sai gobe yana ta jin hayaniyarsu sun fita can haraba amman bai iya ta shi ba, wayarsa ma kashe ta ya yi sai gabda azahar ya ta shi ya yi wanka lokacin har sun yi sallah tunda suna da masallaci a cikin Camp ɗin sai ya yi na shi a cikin ɗaki sannan ya kunna wayarsa.
Ya duba sakonni masu muhimmaci, har da sakon Mu'azzam daman ya faɗa masa zai je wajen Mimi a jiyan, sai a lokacin ya tuna da takardanta da sauri ya miƙe ya isa ga ma sagalan kayansa ya zura hannu a aljihun wandon da ya sa jiya ya ɗauko takardan ya zo ya zauna a saman ƙaramin gadon dake ɗakin ya warware ya fara karantawa..

*SHARUÆŠÆŠAN KOMAWA TA GIDAN AJI.*

1. BA ZAN KOMA BA SAI NA SAKE YIN WANI TARON BIKIN.

2. SAI KA HAÆŠAMIN LEFE, DOMIN BAN ÆŠAUKE MAKA BA.

3.SANNAN ZA KA RIƘA ZUWA TAƊI, DUK BAYAN BAYAN KWANA UKU, DA KUMA YAWAN TURAMIN SAƘONNIN SOYAYYA..

4. NA ƘARSHE SHI NE SAI KA GYARA MU'AMALANKA DA KOWA CIKI HAR DA SASANTAWA DA ABOKAN KA, DA MAI DA DANGINKA DANGINA DA MAIDA DANGINA DANGINKA."

"Amincewar ka ga sharuÉ—dana sune tikitin komawata gidan ka."

  A ƙasa sai ta rubuta sunanta Fatima Kabir Dabo, shima daga gefe sai ta rubuta sunan shi Manaoor Ibrahim aji, sannan daga kasa ga wajen saka hannu da kawanan wata.
Chapter 42 · 0% Book details