← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 93

Sashe 53

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Bayan kuma barowansu gidan ba daɗewa kayan Mimi suka iso, Khadi daman ta zo garin a ranar ita da Baaba Uwani da Anty Mama cewa ta yi ba ta jin daɗi, Mimi ta kira Aji ta gaya masa sai ya ce su haɗu a ƙofar gidan da kwatance da komai suka isa. Shi ya ba su key ɗin gidan suka kuma gaisa da shi  cikin mutunci. Masu kayan daman tare da masu haɗa su suke tafe a daran aka gama haɗa komai sauran ɗakunan kuma sai gobe, Ita kanta Khadi sai da ta yi santin gidan nan haka ta koma tana ce ma Mimi" ke ashe dai mijin nan na ki kuɗi ne da shi, Hajiya kin ga gida? Ma sha Allah wlh gida ya yi kyau Allah ya sa a shiga a sa'a"
Hajiya ta amsa a fili Mimi kuma ta amsa mata a ciki,.Washegari Jawahir ta iso itama duk ba wani taro ba ne Yayan Yaddiko sun zo da su aka haÉ—u a ka koma gidan da sauran kayan Mimi na gidan Daddy aka gama gyaran gidan gabaÉ—aya.

  Hatta bangaren Aji an saka masa kujeru a falo bedroom kuma gado da wardrope, ɗayan ɗakin daman ya ce kada a taɓa shi akawai abib da zai yi da shi,  babban falon Mimi kujerun ta kalan browna mai haske haka ma kalan fentin yake sannan cafet da komai kalan shi kenan da labule, kowani falo Bedroom guda biyu ne. To duka gadajen guda biyu masu ruwan browan ne mai haske sai ƙaramin falon aka maida mata Kujerunta na farko, da gadon ta ɗayan  bedroom ɗin kuma aka siya masa wani gado shima amnan ƙarami ne.
Kitchen ɗin ta kuma ga fali da fili. Nan aka cika mata da kaya, firizanta guda biyu, bayan akwai wani a ɗayan bedroom ɗinta amman shi ƙarami ne ga kuma again fridge a wajen dinning, gaskiya gida ya yi kyau ma sha Allah suka turare shi da turaren kamshi sannan suka yi ta Video Khadi jiki na rawa ta turama Mommy da Madiha, ita kanta Madiha tasan gidan da take ciki a lagos bai fi wanda Mimi za ta shiga ba yanzu duk kushenta sai da ta ce"Woww gidan ya yi kyau Khadi. Ko dai haya ne ba na shi ba ne?
Khadi na dariya ta ce" Na shi ne to ko wata biyu ba'a yi  da fara gina shi, Kuɗi ne da bakin mijin nan na Mimi wallahi"

  Madiha ta jinjina kai kafin ta ce"Na ga alama wato abun na shi ma mugunta ce."
Ita dai Khadi na ta yi mata dariya, Mommy kuma da ta gani ta yi ta saka albarka da tarin addu'o'i, Rukky ta zo itama daga baya ta ga gida ya yi kyau ɗas da shi itama ta saka albarka washegari ya kama jumma'a a kuma ranar Mimi za ta tare. Daga nan bayan sun gama gyaran sun rufe gidan tunda akwai megadi suka koma gida suna ta ƙara Koɗa kyan gidan, Rukky kuma tana ciki tana na taya Mimi haɗa kayanta na gida a daran suka fito da akwatin da suka haɗa reras guda takwas cike da kaya, bayan waɗanda a ka dinka, kowa nata mamaki Hajiya ce kaɗai tasan da maganar kayan kefe. Sai Mommy amman ita ba ta gani ba Mimin dai ta sanar da ita.

  Khadi na ɗaga kaya tana santi ta gaji dai ta ce"Ke wai a ina aka haɗa kayan nan ba mu da labari ne? Rukky ce ta ba ta amsa da Cewa" Anan garin mana cikin azumi muka yi ta shiga kasuwa har da shi, ina gaya miki Anty Khadi Atm ɗinsa ya bamu muka siya komai da komar bai karɓa sai kwanan bayan mun gama duka shirin mu."
Khadi ta zaro ido kafin ta ce"Kai kaji rabo, kuma kuɗin ba su ƙare ba?
Rukky ta ce"Ko girgiza kuma mun kashe kudi ya yi miliyan huÉ—u wlh,"
Sai kowa ya fara hinjina kai, Æ´ayan Yaddiko na ma juna gulman daman mai kuÉ—i ne, Rukky ke ta kora jawabi da cewa" Daman fa da kuÉ—insa, kwai dai yana da dalilinsa ne tun fark. To É—an kwallo ne fa kuma Babba wallahi an ce suna samun mahaukatan kudaÉ—e."

  Khadi ta ce"Na ga alama. Muhammad ma ai ya faɗa min na ga kuma zahiri, ga gida ga lefe ina ga sama da miliyan talatin sai da ta yi kuka kai jama'a, amman ya shammace mu."
A na ta mata dariya ba ta gaji ta kara gyarawa tana ɗaukan Video ɗin kayan nan da nan ta tura ma Dr da Madiha da Mommy ta ce lefen Mimi ne,.Daman Mommy ta san da maganar ta na gani ta saka albarka amman ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da darajarsu, Madiha kan sai ta kasa magana ta ce au har da lefe an yi ne? Khadi ta ce ga zahiri nan ta na gani lefe ne na gani  na faɗa. Dag anan bakin Madiha ya mutu ta ji daman ta zo domin ta ba ma idanuwanta abinci amman dai za ta yi koƙari ta zo ko da baya ne domin ta ga komai da Idanuwanta.

  A daran suka gama haɗa komai, bangaren kayan gara ma Daddy ya aiko da shi komai buhu, itama Mimi ta kara siya ma kanta abin da take so, kamar irin su kayan kamshin girki da zannuwan gado na kamfanin FHB CLOTHING domin zamnuwan gadon su masu inganci ne, shi ya sa Mimi ke yaba kayan su, in kina so kema ki samu zannuwan gado masu kyau kamar irin na Mimin Aji nemi FHB CLOTHING Phone no 08034109622
Wtsapp no.08080266674

   Sun yi mgana da Aji da asuba a kan mganar Walima ita Mimi ta so a bari sai ranar asabar amman Gogan yace a ranar Za'ayi komai a gama shi.Saboda haka ta yi duk abin da ya kamata kafin biyu tana gidanta sai a yi waliman daga lokacin zuwa dare, Da ta gayama Hajiya da su Khadi su ka ce hakan ya yi zaman me za'a yi dama tunda ba wani gagarumin taro ba ne, Rukky ta faɗa ma su Aisha Farida da su Glorin na wajen aikinsu amman direct can gidan za su sauka tun da a matsayin walimar gidan a ka gayyace su.
Tun safe Mimi ta yi wamka mai kwalliya ta zo ta yi mata sannan sun kira mai hot. Wani leshi Mimi ta saka ɗinkin riga da sikat kayan sun karɓe ta matuka ta sha hotuna ma su kyau da yarari. Gidan ba kowa daga su Khadi sai Anty da ta zo da safe da Yaddiko da ƴayanta,  Rukky ma tun safe ta zo ita da Bibi, suma sun sha kwalliyar su gwanin burgewa, Mama ma ta zo ita da ƙannen Jahedd wanda dole dai ya hakura da Mimi tun da Har Daddy sai da ya kira shi ya yi masa fata fqta, sannan tun bayan abin da ya faru tsakaninshi da Mimi ya fara kokarin cire ta a ranshi tun kuma bayan sallah da ya tafi bai dawo ba amman ya yi ma iyayensa alƙwarin cire soyayyar Mimi a ranshi domin ya gina sabuwar rayuwa.

  Rukky har video ta saka Mimi ta yi na waƙar kewa na mawaƙi, Auta waziri ta kuma tura ma Nasir. Shi kuma bayan ya gani sai ya tura cikin group ɗin su ya yi tagging ɗin Aji da cewa"To kai fa Aji ka ji, maganar gaskiya yau kada ka ɗaga kafa Amarya ta ce ta yi kewar ka."
Su Ahmad suka fito suna ta dariya shima yana gari bai koma ba shi da matarsa,Aji kuma bai ma ga sakon ba sai daga baya yana gani ya yi delete for everyone, Nasir na ganin haka ya ƙara turawa Aji ya sake gogewa tun da dukkansu kowa admin ne, Har wajen sau uku, Aji na ganin haka ya danna ma Nasir kira yana ɗagawa ya ce. "Nasir miye haka?  Hoton matata ne zai sama abun wasan ka?
Nasir na dariya yana kwaikwayon waƙan" Kewa. Kewa. Nayi kewar masoyiya."
Aji ya ce"Mallam ka goge shi a wayarka tunda ko a shari'a ya haramta ka riƙa ganin hoton matata, to wai ma a ina ka samu wannan Vedio? Ni fa ban da shi"
Nasir na dariya ya ce" Baby Rukky ta tura min." Aji ya girgiza kai kafin ya ce"Lalle ne ma,." Daga haka ya katse wayar ya kira Mimi, an ci ko sa'a Rukky ta É—auki wayar Mimi na É—akin Hajiya kai tsaye ko ya ce mata me ya sa ta tura ma Nasir video É—in Mimi? Sai tacl ce saboda ba ta da lambarsa ne. A dakune ya ce" Ki goge shi haka kurum ni ban ga adon matata ba wani gardi na can na gane min hakan adalci ne?

  Rukky na danne dariyanta ta ce ya yi hakuri za ta goge, sannan ya ce yauwa ya kashe wayar ya bar Rukky na dariya. Kamar haɗin baki sai ga Nasir ya kirata nan fa ta sabar da shi abij da Aji ya ce ya na dariyan mugunta ya ce"Kyale shi, nima ai ya kirani ya na min surutu."
Rukky ke gaya ma Mimi abin da ya faru, Mimi ta harareta kafin ta ce" Ke ma da gulman tsiya, Mijina bai ga kwalliya ta ba sai saurayin ki.?
Rukky ta ce"Na bani, ni da masu miji miji ko?
Mimi ta yi mata fari kafin ta ce"Kwarai, masu miji ehe."
Nan Jawahir ta zo ta same su Mimi ta gaya mata abin da ya faru tana dariya ta ce"Maganar gaskiya ba'a kyauta ma Ango ba dole ranshi ya ɓaci, ke kuma Rukky baki kyauta ba."
Mimi ta fahimci suna mata shakiyanci ne sai ta bar musu wajen kawai.
Chapter 53 · 0% Book details